13
Sep
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Gwamnan Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi Alla-wadai da harin da aka kai wa tawagar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, yayin da yake kan hanyarsa zuwa Jihar Benue. Sanata Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Talata. Kwankwaso ya ce daƙilewa da kai wa ayarin Obi hari domin hana shi shiga Makurdi wani mummunan lamari ne ga dimokuradiyyar Nijeriya. Ya buƙaci Gwamnatin Jihar Benue ta gaggauta gano tare da gurfanar da waɗanda ke da hannu a lamarin,…
