13
Sep
Komai na mutum yana da iyaka, kuma neman abin da ya wuce ƙaddarar halitta kan iya kai mutum inda bai yi zato ba, kamar wata karin magana da ke cewa, “garin neman ƙiba, akan nemo rama”. Wannan ce ke bayyana akan abin da ya faru da Mista Igho Tiny Ubiribo, wani attajirin ɗan kasuwar Birtaniya kuma ɗan asalin Nijeriya, wanda wata tafiyar jin daɗi da ya kai Thailand tare da matarsa ta sauya salo zuwa labarin mutuwa mai ɗaukar hankali. Attajirin ɗan kasuwar kuma mai tasiri a kafafen sada zumunta, wanda aka fi sani da Denisi ko Ego, ya rasu…
