ukarofi

12469 Posts
Annobar Kwalara Da Mashaƙo: Mu ɗauki matakan kariya ga lafiyar iyalanmu

Annobar Kwalara Da Mashaƙo: Mu ɗauki matakan kariya ga lafiyar iyalanmu

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Ba sabon labari ba ne yadda cututtuka masu haɗari irin su cutar amai da gudawa (Kwalara) da Mashaƙo wacce a turance ake kira da difteriya, ke cigaba da barazana ga rayukan iyalai da dama a Nijeriya. Bincike ya nuna cewa a wannan shekara ta 2026 kaɗai, an riga an samu fiye da mutane 65,000 da ke fama da zazzaɓin cizon sauro, da kuma fiye da 10,000 da ke fama da difteriya. Wannan lamari ya sa dole a ƙara ɗaga murya da kira ga iyaye da masu kula da yara su ƙara himma da sa ido wajen…
Read More
NASEMA ta raba kayan agaji ga waɗanda hare-haren ta’addanci ya shafa a Nasarawa

NASEMA ta raba kayan agaji ga waɗanda hare-haren ta’addanci ya shafa a Nasarawa

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Hukuma dake kula da aukuwar gaggawa wato Nasarawa State Emergency Management Agency (NASEMA) a turance ta raba kayayyakin agaji na miliyoyin kuɗi ga waɗanda bala'oin rayuwa daban daban suka shafa da suka haɗa da hare-haren ta'addanci da rigingimun ƙabilanci da rigingimun filaye da ambaliyar ruwa da gobara da sauran su a wasu ƙauyuka da ke ƙananan hukumomi uku wato Akwanga da Wamba da kuma Nasarawa Eggon duka a jihar ta Nasarawa. Wakilin mu da ya kasance a wajen rabon ya rawaito cewa kayayyakin agajin da aka raba sun haɗa da buhunan shinkafa da na…
Read More
Zan mayar da mafi ƙarancin albashi N500,000 idan na zama shugaban ƙasa – Sowore

Zan mayar da mafi ƙarancin albashi N500,000 idan na zama shugaban ƙasa – Sowore

Daga USMAN KAROFI Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Action Congress (AAC), Omoyele Sowore, ya yi alƙawarin kafa mafi ƙarancin albashi na N500,000 duk wata ga ma’aikatan Najeriya idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a babban zaɓen 2027. Sowore ya ce manufar jam’iyyar ta mayar da hankali ne kan tabbatar da adalci, daidaito da inganta rayuwar ‘yan Najeriya. Ya kuma yi alƙawarin samar da wutar lantarki na sa’o’i 24, da tabbatar da ilimi kyauta kuma mai sauƙin samu a dukkan matakai. Haka kuma, ya ce gwamnatin AAC za ta gina gidaje miliyan ɗaya masu sauƙin kuɗi tare da yin…
Read More
Yana da muhimmanci mai karantar da Musulunci ya zama mai ilimin duniya – Aisha Lemu

Yana da muhimmanci mai karantar da Musulunci ya zama mai ilimin duniya – Aisha Lemu

“Wace ce matar da ta taimaka wajen kafa IET, ta haɗa mata a ƙarƙashin FOMWAN” Daga AISHA ASAS  Ci gaba daga makon jiya. Me ya sa ta kafa FOMWAN? Bari mu koma wani muhimmin sashe. Shin Aisha Lemu ta gamsu da aikinta a makarantu da IET, ko ta ga akwai wani babban giɓi da ya shafi matan Musulmin Najeriya? A shekarar 1985, Aisha Lemu tare da wasu mata musulmai suka kafa Federation of Muslim Women’s Associations in Nigeria, wato FOMWAN. An zaɓe ta a matsayin Amirah ta farko ta ƙasa, kuma ta yi wannan wa’adi na tsawon shekaru huɗu. Manufar…
Read More
Rikicin makamai ya jefa gwamnatin Iraƙi tsaka mai wuya tsakanin Amurka da Iran

Rikicin makamai ya jefa gwamnatin Iraƙi tsaka mai wuya tsakanin Amurka da Iran

Firaministan Iraƙi, Ali al-Zaidi, na fuskantar babban ƙalubale wajen ƙoƙarin kwance damarar wasu ƙungiyoyin Shi’a masu ƙarfin gaske da ke da alaƙa da Iran, duk da alkawarin da ya yi wa Shugaban Amurka Donald Trump cewa gwamnatinsa za ta mayar da makaman ƙasar ƙarƙashin ikon gwamnati. Zaidi ya yi wannan alƙawarin ne bayan ganawarsa da Trump a Fadar White House a watan Yuli, inda ya ce za a kammala aikin kwance damarar waɗannan ƙungiyoyi zuwa ranar 30 ga Satumba. Wannan rana ita ce kuma lokacin da aka shirya sojojin ƙawancen ƙasashen duniya da Amurka ke jagoranta za su kammala ficewarsu…
Read More
Tsohon shugaban Saliyo ya koma gida bayan janye tuhumar cin amanar ƙasa

Tsohon shugaban Saliyo ya koma gida bayan janye tuhumar cin amanar ƙasa

Tsohon shugaban ƙasar Saliyo, Ernest Bai Koroma, ya koma gida a ranar Lahadi bayan shafe sama da shekaru biyu yana zaune a Najeriya, sakamakon matakin da hukumomin ƙasarsa suka ɗauka na dakatar da shari’ar da ake yi masa kan zargin cin amanar ƙasa. Koroma, wanda ya shugabanci Saliyo daga 2007 zuwa 2018, ya bar Najeriya zuwa Freetown bayan da aka kawo ƙarshen shari’ar da ta shafe tsawon lokaci tana rataye a kansa. Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, wanda Koroma ya yi zaman gudun hijira a ƙasarsa, ne ya sanar da tafiyar tasa ta wani saƙo da ya wallafa a shafinsa…
Read More
Nijar ta zargi Faransa da hannu a yunƙurin kifar da gwamnatin soji

Nijar ta zargi Faransa da hannu a yunƙurin kifar da gwamnatin soji

Gwamnatin mulkin sojan Nijar ta zargi Faransa da hannu a yunƙurin kifar da ita da wasu sojoji suka yi a ƙarshen watan Agusta, tana mai cewa ta tattara hujjojin da za su ba ta damar kai batun gaban kotunan ƙasa da ƙasa, yayin da Faransa ta yi watsi da zargin tana mai cewa “ƙirƙira ce tsantsa”. Hukumomin Nijar sun ce yunƙurin ya samo asali ne daga wani gungun sojoji da suka bar wuraren da suke aiki a fagen yaƙi, suka kuma mamaye wasu muhimman wurare a Niamey tsakanin 28 da 29 ga Agusta. Daga cikin wuraren da suka shiga hannunsu…
Read More
Mijin Shugabar Tanzaniya, Samia Suluhu ya rasu

Mijin Shugabar Tanzaniya, Samia Suluhu ya rasu

A ranar Litinin mijin Shugaba Samia Suluhu Hassan ta ƙasar Tanzaniya, Hafidh Ameir ya rasu yayin da yake karɓar magani a wani asibiti da ke Birnin Zanzibar. BBC ta ruwaito cewa, Mataimakin Shugaban ƙasar, Deogratius Ndejembi ne ya sanar da rasuwa Ameir, inda ya ce ya kasance yana fama da wata cuta da ta shafi zuciya. Ndejembi ya ce, Ameir ya rasu ne da misalin ƙarfe 8:00 na safiyar Litinin a Asibitin Emilio Mzena Memorial da ke Zanzibar. Ya ƙara da cewa, ana shirin gudanar da jana’izarsa a ƙauyen Kizimkazi da ke wani yankin na tsibiri a Zanzibar. Ameir dai…
Read More
Attajirin ɗan Nijeriya ya mutu bayan tiyatar ƙara girman mazaƙuta a Thailand

Attajirin ɗan Nijeriya ya mutu bayan tiyatar ƙara girman mazaƙuta a Thailand

Komai na mutum yana da iyaka, kuma neman abin da ya wuce ƙaddarar halitta kan iya kai mutum inda bai yi zato ba, kamar wata karin magana da ke cewa, “garin neman ƙiba, akan nemo rama”. Wannan ce ke bayyana akan abin da ya faru da Mista Igho Tiny Ubiribo, wani attajirin ɗan kasuwar Birtaniya kuma ɗan asalin Nijeriya, wanda wata tafiyar jin daɗi da ya kai Thailand tare da matarsa ta sauya salo zuwa labarin mutuwa mai ɗaukar hankali. Attajirin ɗan kasuwar kuma mai tasiri a kafafen sada zumunta, wanda aka fi sani da Denisi ko Ego, ya rasu…
Read More
Ya kashe ƙaninsa kan irin albasa a Sakkwato

Ya kashe ƙaninsa kan irin albasa a Sakkwato

Wani mutum ya kashe ƙaninsa sakamakon wani rikici da ya ɓarke a tsakaninsu kan irin albasa a garin Barkeji, da ke ƙaramar Hukumar Tambuwal a Jihar Sakkwato. Lamarin ya faru ne ranar Talatar makon da ya gabata, inda Hadi Barkeji ya kashe ƙaninsa, Malam Shehu Barkeji, bayan wata taƙaddama da ta shafi irin albasa. Majiyoyi sun ce rikicin ya samo asali ne bayan Shehu ya ɗauki irin albasa da ɗan uwansa Hadi ya ajiye domin amfani da shi. Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufa’i, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce, an kama wanda ake zargi da…
Read More