ukarofi

12469 Posts
Yadda cutar damuwa ke shafar yara

Yadda cutar damuwa ke shafar yara

Daga AISHA ASAS  Mai karatu sannu da jimirin karatun jaridar al'umma, Blueprint Manhaja, sannunmu da sake kasancewa a shafin Iyali na wannan mako. A wannan mako, za mu tattauna ɓangaren da ba kasafai ake kallonsa a matsayin matsala ba, ko ma in ce ba kasafai ake iya amincewa da wanzuwarsa ba, musamman ma a Arewacin Najeriya, wato cututtuka irinsu damuwa ko baƙin ciki. A gidaje da dama, akwai cututtukan da ba su bayyana a ido, amma suna barazana ga zaman lafiyar iyali. Cutar damuwa (anɗiety) da bakin ciki (depression) suna daga cikin irin waɗannan cututtuka.  Yayin da mutane da yawa…
Read More
Hydroquinone: Ko yadda muka ɗauke shi haka yake?

Hydroquinone: Ko yadda muka ɗauke shi haka yake?

Daga AISHA ASAS Mai karatu, barkanmu da sake kasancewa a shafin Kwalliya na jaridar Blueprint Manhaja. Sannunku da jimirin bibiyar wannan shafi, inda a 'yan kwanakin nan muke ƙoƙarin duba wasu daga cikin abubuwan da suka shafi kula da fata da kyau, musamman waɗanda ake yawan amfani da su ba tare da cikakken bayani kan illarsu ko amfaninsu ba. A makon da ya gabata, mun yi magana ne kan wani sinadari da aka daɗe ana amfani da shi a wasu kayayyakin kula da fata, amma wanda ke iya zama mai matuƙar haɗari idan aka yi amfani da shi ba daidai…
Read More
Gwamna: Tsohon bidiyo ne ke nuna ina goyon bayan Atiku

Gwamna: Tsohon bidiyo ne ke nuna ina goyon bayan Atiku

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe na jam’iyyar APC, Alhaji Dakta Jamilu Isyaku Gwamna, ya yi watsi da wani faifan bidiyo da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta, wanda ake amfani da shi wajen nuna cewa har yanzu yana goyon bayan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar. Gwamna ya bayyana cewa bidiyon tsoho ne, kuma an ɗauke shi ne a lokacin da yake ɗaya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar PDP, kafin daga bisani ya sauya sheƙa zuwa APC tare da mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2023. A cewarsa, kalaman…
Read More
Sarkin Katsina ya karɓi tawagar al’ummar Dutsi da Sabuwa

Sarkin Katsina ya karɓi tawagar al’ummar Dutsi da Sabuwa

Mai Martaba Sarkin Katsina, Dakta Abdulmumini Kabir Usman, ya karɓi tawaga daga ƙananan hukumomin Dutsi da Sabuwa, wadda ta kai ziyara a masarautar domin yin gaisuwa da Jinjina. Tawagar ta yi godiya da jinjina ga mai martaba bisa naɗa sabbin hakimai da za su wakilci al’ummar ƙananan hukumomin biyu, Alh.Ibrahim Bello, wanda aka naɗa a matsayin Kogon Katsina, Hakimin Sabuwa, da Alhaji Abba Lawal Sani, wanda aka naɗa Gabasawan Katsina, Hakimin Dutsi. Da yake jawabi a madadin al’ummar ƙaramar hukumar Sabuwa, Hon. Sagir Tanimu ya yaba wa Mai Martaba bisa ƙoƙarinsa na tabbatar da adalci da daidaito a cikin al’amuran…
Read More
‘Yan wasan ƙwallon ƙafa uku daga Katsina sun sanya hannu a wani kulob na ƙasar Belarus

‘Yan wasan ƙwallon ƙafa uku daga Katsina sun sanya hannu a wani kulob na ƙasar Belarus

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina 'Yan wasan ƙwallon ƙafar na Football Academy su uku daga Katsina sun sanya hannu na buga tamola a ƙungiyar Prolex da ke ƙasar Belarus. Yan wasan sun haɗa da Isma'il Nuhu,Alhassan Muhammad Sherif da Aliyu Abdullahi. Ana sa ran za su fara buga ƙwallon a matsayin abin ƙwararru bayan da suka kammala samun horo a ƙungiyar ta FC Torpedo na ƙasar. Wannan cigaba da aka samu ya nuna mahimmancin kulla da ƙwallon matasa na Football Academy,ya kuma ƙara ganowaɗanda suna Iya samun damar buga wasa a Ƙasashen waje. Kamar yadda sanarwa ta fito daga Football…
Read More
Kwamitin kare kasafin kuɗi na majalisar dokokin Katsina ya shirya taron jin ra’ayoyin al’umma

Kwamitin kare kasafin kuɗi na majalisar dokokin Katsina ya shirya taron jin ra’ayoyin al’umma

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Masu ruwa da tsaki a Jihar Katsina sun samu damar bayyana ra’ayoyinsu da kuma gabatar da shawarwari kan yadda ya kamata a tsara kasafin kuɗin jihar na shekarar 2027. An gudanar da zaman a ɗakin taro na yan jarida da ke majalisar dokokin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura, inda wakilan ƙungiyoyin fararen hula da sauran mahalarta suka nemi ƙarin haske kan abubuwan da aka tanada a cikin kasafin, tare da jaddada buƙatar fifita ayyukan da suka shafi rayuwar al’umma. Shugaban kwamitin kasafi na Majalisar, Hon. Lawal H. Yaro, ya…
Read More
Zuwa ga matasa: Kada mu bar siyasa ta raba mu, mu mayar da ita hanyar gina ƙasarmu

Zuwa ga matasa: Kada mu bar siyasa ta raba mu, mu mayar da ita hanyar gina ƙasarmu

Ya ku matasan Nijeriya, Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu. Ina rubuta wannan wasiƙa ne a gare ku a daidai lokacin da siyasar Nijeriya ke sake ɗaukar wani sabon salo, yayin da ake ƙara tunkarar babban zaɓen shekarar 2027. A hankali, gangamin siyasa na fara ƙamari, ’yan siyasa na fara neman goyon bayan jama’a, ƙungiyoyi na fara bayyana matsayinsu, yayin da kafafen sada zumunta ke ƙara zama filin muhawara da yaƙin neman zaɓe. A irin wannan lokaci ne ya kamata mu, matasa, mu tsaya mu yi tunani sosai. Domin gaskiyar magana ita ce: siyasa ba ta da matsala; abin da…
Read More
Sani Shawai: Kwararren ɗan jarida da dabarun hulɗa da jama’a mai tasiri

Sani Shawai: Kwararren ɗan jarida da dabarun hulɗa da jama’a mai tasiri

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano  Sani Kamaluddeen Shawai an haife shine a ranar 13 ga Maris, 1978, a Dawakin Tofa, Jihar Kano, Najeriya. Tun yana ƙarami a Sabon Gari, Dawaki, ya nuna sha’awar sa kan yaɗa labarai, sadarwa da hidimtawa al’umma, waɗanda daga baya suka zama ginshiƙan aikinsa a fannonin aikin jarida da hulɗa da jama’a. Tafiyar karatunsa ta haɗa tushen ilimin gida da kuma gogewar ƙasa da ƙasa, duk da cewa ya fito ne daga fannin kimiyya. Ya fara karatunsa a Makarantar Firamare ta Musamman ta Dawakin Tofa a shekarar 1989, daga bisani ya halarci Unity College, Karaye, ta…
Read More
Garkuwa: Yadda makarantu, wuraren ibada da masu sufuri suka tsaurara matakan tsaro

Garkuwa: Yadda makarantu, wuraren ibada da masu sufuri suka tsaurara matakan tsaro

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Makarantu, coci-coci da masu gudanar da harkokin sufuri a wasu sassan Nijeriya sun ƙara tsaurara matakan tsaro, sakamakon ƙara fargabar hare-haren ’yan ta’adda, ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane. Wasu makarantu sun ƙara ɗaukar matakan kariya, ciki har da saka kyamarorin sa ido, ƙarfafa katangar makarantu, ƙara yawan jami’an tsaro da kuma samar da hanyoyin tserewa idan aka samu aukuwar wani hari. ɗaukar wazannan matakai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan hare-haren da ake kai wa makarantu da sauran wuraren da ake ganin suna da rauni a faɗin ƙasar.…
Read More
Mu kori kamfen ɗin siyasar ƙabilanci a Arewa

Mu kori kamfen ɗin siyasar ƙabilanci a Arewa

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA ‘Yan siyasar da zallawa su ka so su zama iyayen gidansu, sun ƙi sauraronsu don haka su ka zama ‘yan barandar maciya bulus. Kowa ya san ba mahaluƙin da ya isa ya yi siyasar ƙabilanci a Arewar Musulmi ko ma a ce kokuwar Arewa kuma duk mai ƙoƙarin haka za ka taras ɗan barandar AIFOB ne. Zallawa ‘yan “GEN Z” ba ma abun da su ka sani sai makirci da a ke lakkana mu su. Kawai dama ba Hausawa ba ne balle su san cewa ba wanda ya isa ya raba Hausawa da musulunci da karyar…
Read More