ukarofi

12469 Posts
Mutuwar marubuciya Gloria Steinem: Ba marubuta kawai aka yi wa rashi ba

Mutuwar marubuciya Gloria Steinem: Ba marubuta kawai aka yi wa rashi ba

Daga AISHA ASAS Shahararriyar marubuciya kuma jagorar fafutukar kare haƙƙin mata a Amurka, Gloria Steinem, ta rasu tana da shekara 92, bayan shafe sama da shekaru 50 tana cikin manyan muryoyin gwagwarmayar neman daidaito tsakanin mata da maza. Steinem ta shahara tun shekarun 1960 da 1970, musamman ta hanyar aikin jarida da rubuce-rubucenta kan yadda ake tauye haƙƙin mata. Daga cikin ayyukan da suka sa ta yi fice akwai wani bincikenta na 1963 da ta yi a ɓoye a matsayin ma’aikaciyar Playboy Club, inda ta rubuta kan yadda ake mu’amala da mata masu aikin wurin. A shekarar 1971 ta taimaka…
Read More
Duniya na ci gaba da alhinin mutuwar marubuci Wendell Berry

Duniya na ci gaba da alhinin mutuwar marubuci Wendell Berry

Daga AISHA ASAS Marubuci, mawaƙi kuma manomi ɗan Amurka Wendell Berry ya rasu yana da shekara 92, bayan shafe tsawon rayuwarsa yana rubuce-rubuce kan noma, muhalli da rayuwar karkara, musamman a Jihar Kentucky da ya fito. Berry, wanda ya shahara da littattafai, waƙoƙi da makaloli, ya mayar da rayuwar manoma da al'ummomin karkara wani babban jigo a cikin ayyukansa. Rubuce-rubucensa sun kuma yi kakkausar suka ga yadda bunƙasar masana'antu ke sauya alaƙar mutane da ƙasa da muhalli. A cikin ayyukansa akwai 'The Unsettling of America' da 'The Gift of Good Land', yayin da littattafan almara kamar 'Jayber Crow' suka mayar…
Read More
Marubuta sun nemi kotu ta hukunta OpenAI kan amfani da littattafansu wajen horar da AI

Marubuta sun nemi kotu ta hukunta OpenAI kan amfani da littattafansu wajen horar da AI

Daga AISHA ASAS Wasu marubutan littattafan karatu a Amurka sun kai ƙarar OpenAI da Microsoft, suna zargin kamfanonin da amfani da littattafan da suka rubuta wajen horar da tsarin basirar wucin gadi ba tare da izininsu ba. Karar, wadda aka shigar a watan Agustan 2026, ta ƙara faɗaɗa takaddamar da ake yi a Amurka tsakanin marubuta da kamfanonin fasaha kan yadda ake amfani da littattafan da ke da haƙƙin mallaka wajen gina tsarin AI. Marubutan sun ce littattafan karatunsu na daga cikin abubuwan da kamfanonin ke amfani da su wajen horar da AI, lamarin da suke ganin ya tauye haƙƙinsu…
Read More
Duwan ya jinjina wa gwamnan Katsina bisa aikin sake gina hanyar Bindawa zuwa Duwan

Duwan ya jinjina wa gwamnan Katsina bisa aikin sake gina hanyar Bindawa zuwa Duwan

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Mai bai wa Gwamnan Katsina shawara kan harkokin jam’iyyu, Alhaji Shafiu Abdu Duwan, ya yaba wa Gwamna Raɗɗa, bisa amincewa da sake gina hanyar Bindawa zuwa Dallaje, Doro, Giremawa da Duwan Junction. Alhaji Duwan ya bayyana aikin a matsayin wani muhimmin mataki da zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki da sauƙaƙa rayuwar al’ummar yankin. Gwamna Raɗɗa ya amince da bayar da aikin sake gina hanyar a yayin taron Majalisar Zartarwar karo na 16 da ya gudana a gidan gwamnatin Katsina. Bayan kammala aikin hanyar zai taka muhimmiyar rawa wajen haɗa al’ummomi da kuma sauƙaƙa zirga-zirgar…
Read More
Marubucin Najeriya ya shiga jerin ƙarshe na masu fafatawa a gasar Caine Prize

Marubucin Najeriya ya shiga jerin ƙarshe na masu fafatawa a gasar Caine Prize

Daga AISHA ASAS Marubuci ɗan Najeriya Akinwande Remilekun Jordan na cikin marubuta biyar da aka tantance zuwa jerin ƙarshe na Caine Prize for African Writing ta shekarar 2026. Jordan ya shiga gasar ne da gajeren labarinsa mai suna 'So Long Now It’s Starting To Look Like Eternity', wanda aka wallafa a cikin kundin labarai A House That’s Not A Home. Shi ne kaɗai ɗan Najeriya da ya shiga jerin ƙarshe na bana, yayin da sauran marubutan huɗun suka fito daga Kenya, Kamaru, Masar da Zimbabwe. Su ne Gladwell Pamba, Melara Mvogdobo, Yasmine Zohdi da Simbarashe Steyn Kundizeza. Caine Prize, wadda…
Read More
‘Yan sanda sun kama ‘yan bindiga biyu a Katsina

‘Yan sanda sun kama ‘yan bindiga biyu a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Rundunar 'yan sanda sun kama wasu da ake zargi 'yan bindiga su da mai taimaka masu tare da cewo mutane biyu a Dutsinma da Kankia. Sanarwa daga jami'in hulɗa da jama'a na 'yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu,ya bayyana cewa yan sandan da suke gudanar da sintiri a hanyar ƙauyen Shema Fulani a ƙaramar hukumar Dutsinma suka suka kama mutane uku da ake zargi 'yan bindiga ne bayan samun bayanan sirri. Waɗanda ake zargi sun haɗa da Sani Dikko, Kabir Sani da Salisu Bello. DSP Abubakar Sadiq ya bayyana cewa a yayin da…
Read More
Mutane shida sun mutu a hatsarin motar yaƙin neman zaɓen tsohon Sufeton ‘yan sanda a Nasarawa

Mutane shida sun mutu a hatsarin motar yaƙin neman zaɓen tsohon Sufeton ‘yan sanda a Nasarawa

Daga JOHN D. WADA a Lafia Wani mummunan iftila'i ya afku a jihar Nasarawa inda wasu magoya bayan ɗan takarar gwamnan jihar Nasarawa na jam'iyyar SDP wato Adamu Muhammad Abubakar su shida suka rasa rayukansu sakamakon wani mummunan hatsarin mota a kan gadar sama ta Lafia babbar birnin jihar a jiya Talata. Wakilin mu a jihar ta Nasarawa wanda ya ziyarci inda haɗarin ya auku ya ruwaito cewa waɗanda hatsarin ya rutsa da su, magoya bayan ɗan takarar gwamna na SDP ne kuma tsohon Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya Mohammed Abubakar Adamu. Suna kan hanyarsu ce ta zuwa garin…
Read More
Rundunar ‘yan sandan Katsina ta tallafa da Naira miliyan 28 ga iyalan ‘yan sandan da suka rasu a bakin aiki

Rundunar ‘yan sandan Katsina ta tallafa da Naira miliyan 28 ga iyalan ‘yan sandan da suka rasu a bakin aiki

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Rundunar "yan sanda a Katsina ta tallafa da Naira miliyan 28 ga 'yan sanda 25 da suka rasa rayukansu a lokacin da suke bakin aiki. Da yake miƙa chakin kuɗin ga Iyalan mamattan CP Ali Umar Fage ya ce wannan tsare ne na shugaban 'yan sanda na ƙasa na kula da jin daɗin iyalan 'yan sanda da suka rasa rayukansu a lokacin da suke bakin aiki. CP Fage ya yi ta'aziyar 'yan sandan da suka rasu tare da bayyana su matsayin jarumai da suka sadaukar da kai wajan bautawa ƙasa inda yayi fatan Allah masu…
Read More
Yadda garin Kano ya samo sunansa

Yadda garin Kano ya samo sunansa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Daga cikin tsoffin biranen Hausa, Kano ta shahara a matsayin ɗaya daga cikin biranen da suka fi ɗauke da tarihi mai zurfi a Arewacin Nijeriya. Amma kafin a kira ta da sunan “Kano”, akwai wasu tsoffin matsugunai da al’ummomi a yankin, musamman a wajen Dutsen Dala. To, ina sunan Kano ya samo asali? Tarihin garin Kano yana daga cikin tarihin da suka fi jan hankalin masu bincike a kan tarihin Hausawa. Birnin ya yi suna wajen kasuwanci, sana’o’i, ilimi, siyasa da kuma tsarin mulkin gargajiya, amma tambayar yadda aka samo sunansa har yanzu tana da ruwayoyi…
Read More
Maguɗin zaɓe da illolinsa ga ‘yan ƙasa

Maguɗin zaɓe da illolinsa ga ‘yan ƙasa

Daga Dr. BILKISU YUSUF ALI Zaɓe shine ginshiƙin dimukraɗiyya, domin ta hanyarsa ne jama'a ke bayyana ra'ayinsu wajen zaɓar shugabanninsu. Ingantaccen zaɓe yana tabbatar da gaskiya da adalci da zaman lafiya da ci gaban ƙasa. Sai dai idan aka samu maguɗin zaɓe, hakan na iya raunana amincewar jama'a da tsarin dimokuraɗiyya sannan ya haifar da rikice-rikice da koma bayan tattalin arziki. Wannan takarda ta yi nazari kan ma'anar maguɗin zaɓe, nau'o'insa, abubuwan da ke haddasa shi, illolinsa ga 'yan ɗasa, da hanyoyin da za a bi wajen rage wannan matsala domin ƙarfafa dimokuraɗiyya. Gabatarwa Dimukraɗiyya ce tsarin mulki da ke…
Read More