18
Sep
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ofishin Jakadancin Nijeriya da ke Johannesburg, Babban Birnin ƙasar Afirka ta Kudu, ya fitar da gargadin tsaro ga ’yan Nijeriya da ke zaune a yankunan Kempton Park, Rhodesfield da sauran wuraren da ke kusa da Ekurhuleni, sakamakon mutuwar mata takwas da rundunar ’yan sandan Afirka ta Kudu (SAPS) ke gudanar da bincike a kan al’amuran. A cikin sanarwar tsaron da ofishin ya fitar ranar 16 ga Satumba, 2026, ya ce mutuwar matan ta faru ne cikin kimanin watanni biyu, lamarin da ya sa aka tura wata tawagar bincike mai ƙunshe da jami’an hukumomin tsaro…
