18
Sep
Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano Sabon Sarkin Fawa na Babbar Mayankar Kasuwar ’Yan Awaki da ke ƙaramar hukumar Tarauni a jihar Kano, Alhaji Ahmad Musa, ya bayyana cewa tun bayan hawansa kujerar ya gudanar da wasu ayyukan ci gaba tare da samar da hanyoyin ƙarfafa zaman lafiya da tsaro a mayankar. Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a ofishinsa da ke cikin kasuwar ranar Asabar. Alhaji Ahmad ya ce an samu nasarorin ne sakamakon haɗin kai da goyon bayan da al’ummar kasuwar suke bai wa masarautarsa, yana mai cewa tun kafin hawansa…
