19
Sep
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ƙasar Amurka ta miƙa wasu kayan aikin soji ga Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya, a wani mataki na ƙara ƙarfafa ƙarfin Nijeriya wajen yaƙi da ta’addanci a yankin. Rundunar Sojin Amurka da ke kula da ayyukanta a Afirka (AFRICOM) ce ta bayyana hakan a wani saƙon da ta wallafa a shafinta na ɗ ranar Alhamis. AFRICOM ta ce wani jirgin saman sojin Amurka kirar C-17 ne ya kawo kayan aikin zuwa Nijeriya a ƙarshen mako, ƙarƙashin yarjejeniyar sayar da kayan aikin soji tsakanin ƙasashen biyu. Rundunar ta ce manufar wannan jigilar kayan aikin ita…
