ukarofi

12469 Posts
2027: Kungiyar mata Musulmi daga Arewacin Nijeriya ta goyi bayan Tinubu

2027: Kungiyar mata Musulmi daga Arewacin Nijeriya ta goyi bayan Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A ƙalla malaman addinin Musulunci mata 500 da suka fito daga jihohin Arewa 19 da Babban Birnin Tarayya Abuja sun bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ya sake tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027. Matan, ƙarƙashin ƙungiyar Muslim Intellectuals Forum, sun bayyana matsayinsu ne a wani taron tattaunawa da aka gudanar a Kaduna ranar Lahadi. Sun ce sun yanke wannan matsaya ne bisa la’akari da abubuwan da suka ce gwamnatin Tinubu ta cimma a fannonin ilimi, tsaro, samar da ababen more rayuwa da bunƙasa tattalin arziki. A cikin wata…
Read More
Zaɓe: ADC ta buƙaci INEC ta daina amfani da malaman jami’a masu ra’ayin siyasa

Zaɓe: ADC ta buƙaci INEC ta daina amfani da malaman jami’a masu ra’ayin siyasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam’iyyar ADC ta buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta sake duba amfani da malaman jami’a masu ra’ayin siyasa a matsayin jami’an tattarawa da haɗa sakamakon zaɓe a 2027. Kiran ya biyo bayan rahoton cewa sama da manyan malaman jami’o’in gwamnati 600 daga Arewacin Nijeriya sun nuna goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027. A cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya fitar, jam’iyyar ta ce duk da ’yancin malaman jami’a na goyon bayan dan takarar…
Read More
Wutar lantarki ta kashe ɓarawon kayan tiransfoma a Ribas

Wutar lantarki ta kashe ɓarawon kayan tiransfoma a Ribas

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wani mutum da har yanzu ba a gano ko wanene ba ya mutu bayan wutar lantarki ta kama shi yayin da ake zargin yana ƙoƙarin lalata wata na’urar transfoma domin satar kayayyakin cikinta a yankin Abam-Ama da ke ƙaramar Hukumar Okrika ta Jihar Ribas. Kwamandan Rundunar Tsaron Fararen Hula (CJTF) ta Okrika, Igwe Godswill, ne ya bayyana hakan ranar Talata, inda ya ce mambobin rundunar ne suka gano lamarin yayin da suke sintiri a yankin. A cewarsa, an sanar da rundunar da safiyar Talata cewa an gano gawar mutumin a wurin da transfomar take.…
Read More
Ba za mu dawo da tallafin man fetur ba — Fadar Shugaban ƙasa

Ba za mu dawo da tallafin man fetur ba — Fadar Shugaban ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Fadar Shugaban ƙasa ta yi watsi da shirin tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, na dawo da tallafin man fetur idan ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027. Mai bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya ce dawo da tallafin zai kawo koma-baya ga sauye-sauyen da aka samu a ɓangaren man fetur. Ya kuma ce hakan na iya rage sha’awar masu zuba jari a matatun mai na cikin gida, ciki har da matatar Dangote da sauran ƙananan matatun mai. Onanuga ya bayyana shirin Atiku na…
Read More
Remi Tinubu ta bai wa gwarzuwar musabaƙar Alƙur’ani kyautar miliyan N20

Remi Tinubu ta bai wa gwarzuwar musabaƙar Alƙur’ani kyautar miliyan N20

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Uwargidan Shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bai wa Maryam Ibrahim Dan’Azumi, wadda ta lashe musabaƙar Alƙur’ani ta duniya a Saudiyya, kyautar Naira miliyan 20. A makonnin baya-bayan nan ne Maryam, wadda ’yar asalin Jihar Gombe ce, ta lashe Musabaƙar Alƙur’ani ta ƙasa da ƙasa ta Sarki Abdulaziz karo na 46 da aka gudanar a Makka, Saudiyya. A yayin da take karrama ta a Abuja ranar Talata, Uwargidan Shugaban ƙasar ta bayyana nasarar Maryam a matsayin abin alfahari ga Nijeriya da kuma ’yan mata a duniya. Ta ce Maryam ta zama abin koyi ga…
Read More
Gwamnatin Sokoto ta rufe masallacin Lukuwa, ta kafa kwamitin bincike kan rikicin addini

Gwamnatin Sokoto ta rufe masallacin Lukuwa, ta kafa kwamitin bincike kan rikicin addini

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Jihar Sokoto ta bayar da umarnin rufe Masallacin Juma’a na Musa Lukuwa da ke Mabera, cikin birnin Sokoto, biyo bayan harin da aka kai wa malamin addinin Musulunci, Sheikh Musa Lukuwa, a ranar Juma’ar da ta gabata. Jaridar Tribune ta ruwaito cewa gwamnatin ta kuma ayyana masallacin a matsayin wurin da ake gudanar da binciken laifi, tare da bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin rikicin. Jaridar ta tuna cewa wani matashi daga cikin masu ibada ya kai wa Sheikh Lukuwa hari da wuka jim kaɗan bayan ya jagoranci sallar…
Read More
An kashe ’yan ta’adda sama da 1,200, an kama masu taimaka musu 758 a arewa maso gabas

An kashe ’yan ta’adda sama da 1,200, an kama masu taimaka musu 758 a arewa maso gabas

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kwamandan Rundunar Hadin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation Hadin Kai, mai barin gado, Manjo Janar Abubakar Abdulsalam, ya bayyana cewa an kwato sama da N350m daga hannun masu ɗaukar nauyin ayyukan ’yan ta’adda tun bayan da ya karɓi ragamar jagorancin rundunar. News Point Nigeria ta ruwaito cewa kwamandan ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar Rundunar Hadin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation Hadin Kai, da ke Maiduguri, Jihar Borno, a wani ɓangare na shirye-shiryen bikin kammala aikinsa a rundunar. Abdulsalam ya ce lokacin…
Read More
Kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da ƙarar Hamza Al-Mustapha kan wani fili a Asokoro

Kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da ƙarar Hamza Al-Mustapha kan wani fili a Asokoro

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta yi watsi da buƙatar tsohon Manjo Hamza Al-Mustapha, inda ya nemi a ƙara masa wa’adin da zai ba shi damar ɗaukaka ƙarar hukuncin da Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT) ta yanke kan wata kadarar da ke Asokoro, Abuja. Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa kwamitin alƙalai uku na kotun ya yi watsi da buƙatar Al-Mustapha baki ɗaya, a hukuncin da ya yanke ranar Litinin, inda ya ce bai gabatar da isassun dalilan da za su sa kotun ta amince da ƙarin lokacin ɗaukaka ƙarar ba. A hukuncin…
Read More
INEC za ta binciki zargin almundahanar malaman jami’a da za su gudanar da zaɓen 2027

INEC za ta binciki zargin almundahanar malaman jami’a da za su gudanar da zaɓen 2027

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta ce za ta binciki zarge-zargen nuna son kai ga ’yan siyasa da ake yi wa wasu malaman jami’o’i da ka iya zama jami’an gudanar da zaɓe a babban zaɓen 2027, sannan ta ɗauki matakin da ya dace bisa sakamakon binciken. Daraktar Ilimantar da Masu Zaɓe da Yaɗa Labarai ta hukumar, ɓictoria Ita-Messi, ce ta bayyana hakan a wata tattaunawa da ’yan jarida a ranar Laraba, yayin da take martani kan damuwar da aka nuna game da yiwuwar ɗaukar malaman jami’o’in da suka fito fili suka bayyana goyon…
Read More
Gwamnatin Kano ta ƙudiri aniyar ƙarfafa Hukumar Kashe Gobara ta jihar

Gwamnatin Kano ta ƙudiri aniyar ƙarfafa Hukumar Kashe Gobara ta jihar

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamnatin Jihar Kano ta jaddada aniyarta ta ƙarfafa Hukumar Kashe Gobara ta jihar tare da inganta ƙarfinta na tunkarar al’amuran gaggawa yadda ya kamata, domin kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu. Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Kano, Hajiya Bilkisu Shehu Maimota, ce ta bayyana hakan a lokacin da ta gana da shugabannin Hukumar Kashe Gobara ta jihar, inda suka tattauna dabarun inganta ayyukan hukumar, jin daɗin ma’aikata da ci gaban hukumance. Taron ya mayar da hankali ne kan muhimman batutuwan da ke kawo cikas ga gudanar da ayyukan hukumar yadda ya kamata, inda aka tattauna hanyoyin magance…
Read More