ukarofi

12468 Posts
’Ya’yana sun isa su gaji kasuwancina duk da mata ne – Dangote

’Ya’yana sun isa su gaji kasuwancina duk da mata ne – Dangote

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa samun ɗa namiji da zai gaji daular kasuwancinsa ba shi ne babban abin da ya fi ba shi muhimmanci ba, yana mai cewa ’ya’yansa mata uku suna da cikakkiyar damar jagorantar Rukunin Kamfanonin Dangote nan gaba. Dangote ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na ARISE a ranar Talata, inda ya ce yana ganin ɗaya daga cikin ’ya’yansa mata na iya zama jagorar babbar daular kasuwancin iyalin. Da aka tambaye shi ko yana ganin ɗaya daga cikin ’ya’yansa mata za ta iya karɓar…
Read More
2027: Kada ku bari ’yan siyasa su ruɗe ku da alƙawura – Sarkin Musulmi

2027: Kada ku bari ’yan siyasa su ruɗe ku da alƙawura – Sarkin Musulmi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Mai Alfarma Sarkin Musulmin Nijeriya, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya shawarci ’yan Nijeriya da su yi taka-tsantsan tare da tantance alƙawuran ’yan siyasa kafin su yanke shawarar wanda za su mara wa baya a babban zaɓen ƙasar na 2027. Sarkin ya kuma gargaɗi ’yan siyasa da su guji mayar da matsalar tsaro da sauran ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta tamkar kayan kamfen a lokacin yaƙin neman zaɓe, yana mai cewa ya kamata su fi mayar da hankali kan batutuwan da za su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa. Sarkin Musulmin…
Read More
Jirage 7,961 suka yi jigila a Agusta amma 4,765 sun samu jinkirin tashi – NCAA

Jirage 7,961 suka yi jigila a Agusta amma 4,765 sun samu jinkirin tashi – NCAA

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kamfanonin jiragen sama na Air Peace da United Nigeria Airlines ne suka fi samun yawan jiragen da suka makara a tsakanin kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama na cikin gida a Nijeriya a watan Agustan 2026. Hakan na munshe ne cikin rahoton Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Nijeriya (NCAA), kan yadda zirga-zirgar jiragen saman cikin gida suka gudana a watan Agusta. Bisa ga bayanan hukumar, Air Peace ta yi zirga-zirgar jirage 1,864 a cikin watan, inda 1,330 daga cikinsu suka samu jinkiri. United Nigeria Airlines ce ta biyo bayanta, inda daga cikin jirage 1,231 da ta…
Read More
Dage takunkumin Amurka zai rage kuɗaɗen jiragen ruwa da bunƙasa kasuwancin Nijeriya – Oyetola

Dage takunkumin Amurka zai rage kuɗaɗen jiragen ruwa da bunƙasa kasuwancin Nijeriya – Oyetola

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Masana’antar Harkokin Ruwa ta Nijeriya na shirin samun sabon ci gaba a fannin jigilar kayayyaki da kasuwancin ƙasa da ƙasa, bayan gwamnatin Amurka ta ɗage wani takunkumin tsaro da ta shafe tsawon shekaru 12 tana ƙaƙaba wa jiragen ruwa masu tutar Nijeriya da ke zuwa tashoshin jiragen ruwa na Amurka. Ana sa ran matakin zai rage wasu ƙarin kuɗaɗen tsaro da kuma matakan gudanarwa da a baya ake buƙatar masu jiragen ruwa su bi yayin zirga-zirga tsakanin Nijeriya da Amurka. Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka mai kula da Harkokin Afirka, Frank W. Garcia Jr., ne ya…
Read More
Kotu ta umarci bankin Zenith da ’yan sanda su biya miliyan N85 kan rufe asusun kwastoma

Kotu ta umarci bankin Zenith da ’yan sanda su biya miliyan N85 kan rufe asusun kwastoma

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya Abuja, wanda ya ɗora wa Bankin Zenith da Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya alhakin biyan diyyar Naira miliyan 85 saboda rufe asusun wani abokin ciniki ba bisa ƙa’ida ba, bisa wani umarnin kotu da bai da inganci. A wani hukunci da kwamitin alƙalai uku na Kotun ɗaukaka ƙara ya yanke baki ɗaya ranar Litinin, kwamitin da Mai Shari’a Adebukola Banjoko ta jagoranta ya yi watsi da ƙarar da Bankin Zenith ya shigar, yana mai cewa ba ta da hujjar da za ta…
Read More
Ba a kawar da wariyar launin fata a Afirka ta Kudu ba sai da taimakon Nijeriya – Obasanjo

Ba a kawar da wariyar launin fata a Afirka ta Kudu ba sai da taimakon Nijeriya – Obasanjo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya ce da ba don goyon bayan da Nijeriya ta bai wa gwagwarmayar yaki da mulkin wariyar launin fata ba, da Afirka ta Kudu ba ta kawo karshen mulkin wariyar launin fata a shekarar 1994 ba. Obasanjo ya bayyana hakan ne a wata hira da shirin C-Suite Cafe, inda ya ce Nijeriya ta shiga gwagwarmayar ne saboda imanin cewa babu wani bakar fata da ya kamata a dauke shi a matsayin dan kasa ko mutum marar daraja saboda launin fatarsa. Ya ce Nijeriya ta yi aiki tare da wasu…
Read More
ADC: Kotu ta ɗage sauraron ƙarar Nafiu Bala akan Mark da Aregbesola

ADC: Kotu ta ɗage sauraron ƙarar Nafiu Bala akan Mark da Aregbesola

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ɗage sauraron ƙarar da Nafiu-Bala Gombe ya shigar, wadda ya ke neman a hana shugabannin ADC  da Daɓid Mark ke jagoranta, ci gaba da gabatar da kansu a matsayin shugabannin jam’iyyar, zuwa ranar 28 ga watan Satumba. An sanya ranar Litinin domin sauraron dukkan ƙorafe-ƙorafen da ke gaban kotun dangane da ƙarar, sai dai zaman bai yiwu ba saboda Alƙalin da ke jagorantar shari’ar, Mai Shari’a Peter Lifu, bai zauna ba. Daga bisani, kotun ta sanya ranar 28 ga watan Satumba domin ci gaba da sauraron shari’ar.…
Read More
Wani babban jami’in EFCC na fuskantar zarge-zargen cin hanci da rashawa 

Wani babban jami’in EFCC na fuskantar zarge-zargen cin hanci da rashawa 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wani babban jami’in gudanarwa mai muƙamin Assistant Commander (ACE) a Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arziƙin ƙasa Ta’annati (EFCC) ya fuskanci zarge-zargen cin hanci da rashawa, amfani da muƙami ba bisa ƙa’ida ba, daƙile shari’a da kuma mallakar dukiya mai yawa wadda ake zargin ba ta dace da abin da yake samu a matsayin albashi ba. Zarge-zargen na ƙunshe ne cikin wata takarda mai shafuka shida da ƙungiyar Network for Justice Association of Nigeria (NJAN) ta miƙa wa Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ranar 9 ga Yuli, 2026, wadda Blueprint Manhaja ta samu…
Read More
Mulki zai dawo Arewa bayan wa’adin Tinubu biyu — Zulum

Mulki zai dawo Arewa bayan wa’adin Tinubu biyu — Zulum

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya ce shugabannin Arewa sun amince da goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ya sake samun wa’adin mulki na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, bisa fahimtar cewa bayan kammala wa’adinsa biyu, shugabancin ƙasar zai koma yankin Arewa. Zulum ya bayyana hakan ne ranar Lahadi a Kaduna, yayin da yake jawabi bayan wata ganawa da ƙungiyar mata malaman addinin Musulunci daga jihohin Arewa. Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa taron ya mayar da hankali kan ƙarfafa haɗin kai, zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al’ummar…
Read More
2027: Kungiyar mata Musulmi daga Arewacin Nijeriya ta goyi bayan Tinubu

2027: Kungiyar mata Musulmi daga Arewacin Nijeriya ta goyi bayan Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A ƙalla malaman addinin Musulunci mata 500 da suka fito daga jihohin Arewa 19 da Babban Birnin Tarayya Abuja sun bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ya sake tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027. Matan, ƙarƙashin ƙungiyar Muslim Intellectuals Forum, sun bayyana matsayinsu ne a wani taron tattaunawa da aka gudanar a Kaduna ranar Lahadi. Sun ce sun yanke wannan matsaya ne bisa la’akari da abubuwan da suka ce gwamnatin Tinubu ta cimma a fannonin ilimi, tsaro, samar da ababen more rayuwa da bunƙasa tattalin arziki. A cikin wata…
Read More