ukarofi

12471 Posts
Iyayen yara sun shiga tsaka mai wuya bisa tsadar kuɗin makaranta

Iyayen yara sun shiga tsaka mai wuya bisa tsadar kuɗin makaranta

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Iyaye da masu kula da yara a Nijeriya na fuskantar sabon matsin tattalin arziki yayin da farashin kuɗin makaranta, littattafan karatu, masauki da sauran kuɗaɗen komawa makaranta ke ƙaruwa gabanin fara sabuwar shekarar karatu. Bincike da aka gudanar a makarantun firamare, sakandare da manyan makarantun gaba da sakandare a faɗin ƙasar ya nuna cewa, iyalai da dama za su kashe kuɗi fiye da abin da suka kashe a shekarar karatu da ta gabata, yayin da makarantu da ’yan kasuwar kayan ilimi ke daidaita farashinsu da yanayin tsadar rayuwa. Rahotanni sun nuna cewa farashin littattafan…
Read More
Kisan Danshagamu: ’Yan sanda sun kama mutane biyu a Kano

Kisan Danshagamu: ’Yan sanda sun kama mutane biyu a Kano

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sanar da kama mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan shahararren mai sharhin siyasa, Ibrahim Khalil Danshagamu, wanda aka kai wa hari da makamai masu kaifi a gidansa da ke Unguwar Gaida, a ƙaramar Hukumar Kumbotso ta jihar. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na daren Litinin, bayan Rundunar ’Yan Sandan ta samu kiran gaggawa daga Kwamandan ƙungiyar ’Yan Sa-kai ta Gaida, inda ya sanar da cewa wasu ’yan daba da ba a san ko su waye ba sun kutsa cikin gidan marigayin da ƙarfi tare…
Read More
NURTW ta karrama Gwamna Lawal, ta goyi bayan tazarcensa a 2027

NURTW ta karrama Gwamna Lawal, ta goyi bayan tazarcensa a 2027

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kungiyar Ma’aikatan Sufurin Mota ta ƙasa (NURTW) ta karrama Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, bisa yadda ta ce ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta harkokin sufuri da samar da ababen more rayuwa a jihar. Kungiyar ta bai wa Gwamna Lawal lambar yabo ta ƙwarewa da Nagarta, wato Award of Excellence, a wani biki da aka gudanar ranar Laraba a Dome Paɓilion da ke harabar Gidan Gwamnatin Jihar Zamfara a Gusau. Baya ga karramawar, ƙungiyar ta kuma bayyana cikakken goyon bayanta ga Gwamna Lawal, inda ta amince da ya sake neman wa’adi na biyu a…
Read More
Ashiru Kudan ya zargi APC da tarwatsa masu goyon bayan ADC da barkonon tsohuwa a taron Kaduna

Ashiru Kudan ya zargi APC da tarwatsa masu goyon bayan ADC da barkonon tsohuwa a taron Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Dan takarar gwamnan Kaduna na Jam’iyyar ADC a zaɓen 2027, Isa Mohammed Ashiru, ya zargi gwamnatin Kaduna da amfani da jami’an tsaro da ’yan daba wajen tarwatsa masu goyon bayan jam’iyyar da suka gudanar da tattakin haɗin kai a Kaduna. Ashiru ya yi wannan zargin ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, bayan dubban magoya bayan ADC da wasu ’yan jihar suka taru a dandalin Murtala Sƙuare domin gudanar da tattaki. Ya ce mahalarta tattakin sun fito ne cikin lumana domin bayyana goyon bayansu ga ADC da kuma buƙatar sauyi a jihar.…
Read More
Kungiyar Kiristoci ta ayyana goyon bayan Tinubu a zaɓen 2027

Kungiyar Kiristoci ta ayyana goyon bayan Tinubu a zaɓen 2027

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kungiyar "Charismatic Bishops Conference of Nigeria" (CBCN) ta bayyana goyon bayan ta ga Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a babban zaɓen 2027. Shugaban CBCN, Archbishop Prof. Leonard Bature Kawas, shi ne ya bayyana matsayar ƙungiyar a ranar Laraba a Abuja, a lokacin da ake gudanar da babban taron Synod na 2026 na CBCN da ICCABA a Majami'ar Kiristoci ta ƙasa. Kawas ya ce ƙungiyar ta yi nazari kan ayyukan gwamnatin Tinubu, tare da bayyana shirin ta na ci gaba da mara wa shugaban ƙasar baya ta hanyar addu’a, bayar da shawarwari da kuma wayar…
Read More
Gwamna Abba ya buƙaci ’yan siyasa su guji tashin hankali a lokacin kamfe

Gwamna Abba ya buƙaci ’yan siyasa su guji tashin hankali a lokacin kamfe

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga dukkan ’yan takarar kujerar gwamna da ta Majalisar Dokokin Jiha da su gudanar da yaƙin neman zaɓensu cikin lumana, mutunci da sanin ya kamata, tare da yin cikakken biyayya ga dokokin ƙasa. Gwamnan ya yi wannan kira ne yayin da aka fara yaƙin neman zaɓen kujerun gwamna da na Majalisun Dokokin Jihohi a faɗin Nijeriya, inda ya buƙaci jam’iyyun siyasa, ’yan takara da magoya bayansu da su sanya zaman lafiya, haɗin kan al’umma da kare muradun jama’a a sahun gaba a duk tsawon lokacin…
Read More
‘Yan sanda sun kama mutum tara kan zargin karkatar da ‘yan ƙwamaso a Katsina

‘Yan sanda sun kama mutum tara kan zargin karkatar da ‘yan ƙwamaso a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina 'Yan sanda da haɗin gwiwa na kwamitin koda ta kwana da gwamnatin Katsina ta kafa sun sami nasarar kama mutane tara da ake zargi da karkatar da abincin gina jiki na ƙananan yara da ke fama da cutar tamuwa a Katsina. Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya fatar da sanarwar haka,mace ce, Amina Abdulrahaman aka fara kamawa yar shekara 46 da ke zaune a Mobil Quarters cikin garin Katsina ɗauke da 'yan ƙwamaso guda 600. Wanda ake zargi ta tabbatar da cewa ta saya a hannun…
Read More
Gwamnatin Tarayya da NYSC za su fito da tsarin adana bayanai domin daƙile takardun bogi

Gwamnatin Tarayya da NYSC za su fito da tsarin adana bayanai domin daƙile takardun bogi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Tarayya ta ce tana shirin ƙara haɗa tsarin adana bayanan ilimi na zamani da na Hukumar Kula da Hidimar Matasa ta ƙasa (NYSC), domin yaƙi da safarar takardun shaidar karatu na bogi, ƙarfafa tantance cancantar masu digiri da kuma tabbatar da cewa ba a hana waɗanda suka yi karatu na gaskiya damar samun ayyuka ba. News Point Nigeria ta ruwaito cewa Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin wata ganawa da Darakta-Janar na NYSC, Birgediya-Janar Olakunle Nafiu, wanda ya jagoranci tawagar hukumar zuwa ma’aikatar da ke Abuja.…
Read More
Matar da ta ƙirƙiri sanarwar cewa Opay zai daina aiki ta shiga hannun ‘yan sanda

Matar da ta ƙirƙiri sanarwar cewa Opay zai daina aiki ta shiga hannun ‘yan sanda

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta kama Hafsat Abubakar, mai shekara 27, bisa zargin ƙirƙira da yaɗa wata takardar bogi da ke cewa kamfanin OPay  zai daina aiki. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Anietie Iniedu, ya bayyana cewa an kama Hafsat ne ranar 4 ga Satumba 2026, bayan OPay ta kai ƙorafi ga rundunar ‘yan sanda a ranar 31 ga Agusta. Ya ce cibiyar yaƙi da laifukan yanar gizo ta ‘yansanda ta gudanar da binciken ƙwaƙƙwafi na Internet, inda aka gano cewa takardar ta samo asali ne daga wani shafin ɗ da Hafsat Abubakar…
Read More
Mashaƙo: Nijeriya na fuskantar barazanar cuta duk da samuwar rigakafi

Mashaƙo: Nijeriya na fuskantar barazanar cuta duk da samuwar rigakafi

Rufe giɓin cutar mashaƙo, wato diphtheria a Nijeriya ya zama abin damuwa, duk da cewa akwai ingantaccen allurar rigakafin cutar da aka tabbatar da amincinta. Yawaitar ɓullar cutar a sassa daban-daban na ƙasar na buƙatar ɗaukar matakin gaggawa da kuma haɗin gwiwar gwamnati a dukkan matakai. Hukumar Daƙile da Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Nijeriya (NCDC) ta ce an tabbatar da sama da mutane 10,000 da suka kamu da cutar mashaƙo a bana, inda jihohin Arewa da Tsakiyar Nijeriya, ciki har da Kano, Katsina, Bauchi da Filato, ke cikin jihohin da cutar ta fi ƙamari. Haka kuma, an samu…
Read More