ukarofi

12484 Posts
Jirgin helikwafta mai ɗauke da masu yawon buɗe ido ya faɗi a Kenya

Jirgin helikwafta mai ɗauke da masu yawon buɗe ido ya faɗi a Kenya

Wani jirgin helikwafta da ake zargin yana ɗauke da masu yawon bude ido ya yi hatsari a gundumar Samburu da ke arewacin Kenya. Kafofin yada labarai na cikin ƙasar, ciki har da The Star da Standard, ne suka fara kawo rahoton hatsarin a ranar Laraba, 19 ga Agusta, 2026.  Rahoton farko bai bayyana cikakken adadin mutanen da ke cikin jirgin ko adadin waɗanda suka mutu ko suka jikkata ba, yayin da hukumomi ke ci gaba da tattara bayanai kan abin da ya faru. Samburu na daga cikin wuraren da suka shahara a yawon buɗe ido a Kenya, musamman saboda namun…
Read More
Amurka da Koriya ta Kudu sun rage girman atisayen soji da suka yi niyya

Amurka da Koriya ta Kudu sun rage girman atisayen soji da suka yi niyya

Amurka da Koriya ta Kudu sun rage tsawon babban atisayen sojinsu na shekara-shekara, bayan umarnin Shugaban Amurka Donald Trump na a rage yawan atisayen. Atisayen Ulchi Freedom Shield, wanda aka fara a wannan makon, yanzu za a kammala shi bayan kwanaki biyar maimakon kwanaki 11 da aka tsara a baya. Haka kuma an rage wasu daga cikin atisayen sojin kasa.  Matakin ya zo ne bayan Trump ya nuna cewa ba ya son yawan atisayen soji da Koriya ta Kudu, yana mai cewa yana son sake buɗe ƙofar tattaunawa da shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un.  Sai dai wasu masana…
Read More
Turkiyya ta yi tir da hare-haren Isra’ila a Syria

Turkiyya ta yi tir da hare-haren Isra’ila a Syria

Turkiyya ta yi kakkausar suka ga hare-haren sama da Isra'ila ta kai wani sansanin soji a Syria, tana mai cewa bayanan da Isra'ila ta bayar wajen kare matakin nata ba su da tushe. Isra'ila ta kai hare-hare takwas kan sansanin Abu al-Duhur da ke kusa da Aleppo a ranar Talata, a cewar kafafen yaɗa labaran Syria. An ce hare-haren sun shafi titin saukar jiragen sama da wasu wuraren ajiye kayan aiki, amma ba a samu rahoton mutuwar mutane ba.  Isra'ila ta ce matakin nata ya kasance ne saboda damuwar cewa Syria na shirin barin sojojin Turkiyya su yi amfani da…
Read More
Trump ya musanta tattaunawa da Iran, yayin da rikicin Hormuz ke ƙara tsananta

Trump ya musanta tattaunawa da Iran, yayin da rikicin Hormuz ke ƙara tsananta

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce babu wata tattaunawa da ke gudana tsakanin Amurka da Iran, yayin da Tehran ta ce har yanzu mashigar ruwan Hormuz a rufe take, lamarin da ya sake jefa shirin kawo ƙarshen rikicin ƙasashen biyu cikin rashin tabbas. Trump ya bayyana hakan ne ranar Talata, 18 ga Agusta, 2026, inda ya ce babu wata tattaunawa da aka shirya yi tsakanin Washington da Tehran. Ya kuma dage cewa mashigar Hormuz a buɗe take, kuma ana iya zirga-zirgar jiragen ruwa a cikinta. Sai dai Iran ta musanta hakan, inda ta ce ba za ta buɗe mashigar ba…
Read More
Nijeriya na shirin zama cibiyar noma a Yammacin Afirka — AFAN

Nijeriya na shirin zama cibiyar noma a Yammacin Afirka — AFAN

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban ƙungiyar Manoma ta Nijeriya (AFAN), Dakta Farouk Rabiu Mudi, ya sake jaddada cikakken goyon bayan ƙungiyar ga Ajandar Sabonta Fata ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu, musamman ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na sauya fasalin harkar noma da tabbatar da wadatar abinci a ƙasar. Mudi ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai, inda ya ce AFAN, a matsayinta na babbar ƙungiyar da ke haɗa manoma, ƙungiyoyin kayan amfanin gona, ƙungiyoyin haɗin gwiwar manoma da sauran hukumomi masu alaƙa da noma, ta ƙuduri aniyar yin aiki tare da gwamnatin yanzu domin magance matsalar ƙarancin abinci tare da…
Read More
Ilimi ba ya cika sai da tarbiyya — Shugaban Makarantar Guidway

Ilimi ba ya cika sai da tarbiyya — Shugaban Makarantar Guidway

Daga WAKILINMU Shugaban Matarantar Guidway Islamic Science Academy, da ke Layin Awe Road, Kinkinau a Jihar Kaduna, Malam Muhammad Surajo Inace, ya yi kira ga iyaye da su ƙara mayar da hankali kan tarbiyya da karatun ’ya’yansu. Malam Surajo ya ce, duk wanda Allah Ya azurta shi da ’ya’ya, ya samu babbar ni’ima da alheri, don haka ya kamata iyaye su kasance masu kulawa da tarbiyya da kuma ilimin ’ya’yansu. Ya ja hankalin iyaye da kada su ɗora wa malamai alhakin tarbiyyar ’ya’yansu su kaɗai, domin iyaye ma suna da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ɗa ya tashi cikin tarbiyya…
Read More
Makarantar Nuru Raudatur Nabiyyu ta gudanar da saukar Alƙur’ani ta farko ga ɗalibai 40

Makarantar Nuru Raudatur Nabiyyu ta gudanar da saukar Alƙur’ani ta farko ga ɗalibai 40

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan Yaɗa Labarai, Malam Abdul’azeez Abdul’azeez, ya yaba da ƙoƙarin masu gudanar da Madarasatur Nuru Raudatur Nabiyyu Litahfizul ƙur’ani Wal-Darasatul Islamiyya, da ke Fagge, Kano, bisa irin gudubmawar da suke bayarwa wajen samar da ilimin addini da na Alƙur’ani ga yara da matasa. Malam Abdul’azeez ya bayyana hakan ne a yayin bikin saukar Alƙur’ani ta farko da kuma taron karrama wasu fitattun mutane da suka taka rawa wajen tallafa wa ilimi da ci gaban makarantar, wanda aka gudanar ranar Asabar. Ya ce irin waɗannan makarantu…
Read More
MPM ta taya Yarima, Matawalle, da Lawal murna kan naɗa su cikin tawagar kamfen na Tinubu

MPM ta taya Yarima, Matawalle, da Lawal murna kan naɗa su cikin tawagar kamfen na Tinubu

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Ƙungiyar siyasa ta Matawalle, mai take Matawalle Political Movement MPM a Zamfara ta taya fitattun 'ya'yan jihar Zamfara guda biyar murna kan shigar da su cikin Majalisar kamfen ɗin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na 2027. A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na ƙungiya, Yusuf Idris Gusau, ya sanya wa hannu a yau Asabar a Gusau, ƙungiya ta ce naɗin ya ƙara sanya Zamfara a kan matsayi mai kyau a siyasar ƙasa. Kungiyar ta bayyana naɗin a matsayin wani muhimmin abin girmamawa ga gudummawar da jihar ta bayar ga APC. A cewar sanarwar, Shugaba…
Read More
Dakta Elayo ta raba tallafin buhunan shinkafa 600 ga mabuƙata a Keana

Dakta Elayo ta raba tallafin buhunan shinkafa 600 ga mabuƙata a Keana

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Gimbiya Dr. Margaret Elayo kwamishiniyar ma’aikatar muhalli da albarkatun ƙasa kuma kwamishiniya mai riƙon kwarya na ma’aikatar harkokin mata da ayyukan jin ƙai a jihar Nasarawa ta raba buhunan shinkafa 600 a faɗin mazaɓu 10 na ƙaramar hukumar Keana a jihar Nasarawa. Wannan tallafi ya kuma haɗa da rabon kuɗi domin ƙara wa tallafin abinci karfi. Wannan ya nuna jajircewar Dakta Elayo a matsayinta na mai fafutukar jin ƙai dake ƙoƙarin magance buƙatun al’ummar da ba su da ƙarfi. Yanzu da ake fuskantar wani zaɓe Dr. Elayo tace jam’iyyar All Progressives Congress APC mai…
Read More
Masarautar Koko ta nemi a sauƙaƙa aure

Masarautar Koko ta nemi a sauƙaƙa aure

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Mai girma uban ƙasar Koko, Alhaji Mohammed Bello Koko II, ya bayyana aniyar masarautar Koko na farfaɗo da dokokin da za su taimaka wajen sauƙaƙa yin aure ga matasa da kuma masu son ƙara mata ta hanyar rage nauyin kuɗi da al’adun da ke ƙara tsadar aure. Basaraken ya bayyana cewa tun da farko akwai irin wannan doka a masarautar Koko wacce manufarta ita ce kare matasa daga shiga cikin matsanancin nauyin da zai iya hana su yin aure ko kuma ya sa su fara rayuwar aure cikin matsalolin bashi ko faɗawa tarkon shaiɗan. Insha…
Read More