23
Aug
Daga AISHA ASAS Waƙar 'Dai Dai' ta mawaƙin Najeriya Burna Boy da fitacciyar mawaƙiya 'yar Colombia Shakira ta ci gaba da riƙe matsayi na ɗaya a jadawalin Billboard Global 200, inda ta shafe mako na biyar a jere tana kan gaba. Billboard ta bayyana cewa waƙar, wadda ta kasance waƙar gasar cin kofin duniya ta FIFA 2026, ta ci gaba da samun gagarumar karɓuwa duk da cewa an kammala gasar tun kusan wata ɗaya da ya wuce. A jadawalin da aka sabunta a ranar 18 ga Agusta, Dai Dai ta ci gaba da kasancewa a matsayi na ɗaya. Bayanan Luminate…
