ukarofi

12485 Posts
Yari ya bada tallafin N12.5M ga zawiyyah 43 a Zamfara

Yari ya bada tallafin N12.5M ga zawiyyah 43 a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Sanata Abdulaziz Yari Abubakar, mai wakiltar mazaɓar Zamfara ta Yamma, ya bayar da gudunmuwar shanu 43, buhunan shinkafa 356 da Naira miliyan 12,500,000 ga zawiyyah guda 43 da ke faɗin ƙananan hukumomin jihar Zamfara 14 domin gudanar da bikin Mauludi. A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Hon. Ibrahim Muhammad, shugaban kwamitin yaɗa labarai, Sanata Yari ya buƙaci al’ummar Musulmi da su yi amfani da wannan damar wajen yi wa Nijeriya addu’ar zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa, tare da roƙon Allah ya ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnatinsa jagora. An…
Read More
Gwamna Dauda Lawal ya lashe kyautar Blueprint ta 2026

Gwamna Dauda Lawal ya lashe kyautar Blueprint ta 2026

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau An karrama Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal da kyautar ingancin gudanar da albarkatun jama'a da bayyana gaskiya ta 2026 ta Jaridar Blueprint. Kakakin Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ga 'yan jarida a Gusau ranar Talata. "Gwamnan ya sami kyautar ne a ranar Talata a taron shekara-shekara na muhadara ta takwas ta Jaridar Blueprint, jerin tasiri da kyaututtuka, wanda aka gudanar a cibiyar taro ta duniya ta Bola Ahmed Tinubu, Abuja". Jigon taron na wannan shekarar shine "Ƙalubalen tsaro da mutuncin zaɓen Najeriya na 2027." Da…
Read More
Sarkin Katsina ya sanar da naɗin sabbin Hakimai guda takwas

Sarkin Katsina ya sanar da naɗin sabbin Hakimai guda takwas

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Fadar Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji (Dakta) Abdulmumini Kabir Usman ta sanar da naɗin sabbin hakimai guda takwas a masarautar Katsina. Sarki Usman, ya umarci sakataren majalisar masarautar Katsina Alhaji Isah Ali Kankia da ya bayyana naɗin sabbin hakiman, waɗanda za ayi bikin naɗin a ranar 29 ga Agusta, 2026. Hakiman da za'a naɗa sun haɗa da Alhaji Sani Tukur Mu’azu Sarkin Rumah Katsina -( Hakimin BatsariDa Alhaji Abba Lawal Sani Dutsi (Gabasawan Katsina)Hakimin Dutsi, Sai Alhaji Gambo Abdullahi Dabai (Dausayin Katsina) – Hakimin Dabai akwai kuma Alhaji Zakari Maina (Dan Yusufan Katsina)Hakimin Bindawa. Da…
Read More
Gidaje da dama sun rushe a Katsina sakamakon ruwan sama

Gidaje da dama sun rushe a Katsina sakamakon ruwan sama

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Katsina (SEMA) ta kai ziyarar gani da ido zuwa ƙaramar hukumar Kankia domin tantance ɓarnar da ambaliyar ruwa ta haddasa. Ziyarar ta gudana ne bisa umarnin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, domin duba irin asarar da aka samu tare da jajanta wa al’ummomin da iftila’in ya shafa. Shugabar SEMA, Hajiya Binta Hussaini Dan-Gani, ta ce manufar ziyarar ita ce jajanta wa waɗanda abin ya shafa da kuma tattara sahihan bayanai kan ɓarnar da aka samu, domin gwamnati ta ɗauki matakan da suka dace. Ta bayyana cewa…
Read More
Zuwa ga masu shirin aure (II)

Zuwa ga masu shirin aure (II)

Assalamu alaikum, kamar yadda muka faɗa a makon da ya gabata cewa, za mu ci gaba daga inda muka tsaya. Abu na biyu da zan gaya muku shi ne yana da kyau ku fahimci cewa waɗannan abubuwa ba a samunsu haka kawai, wato ba sa samun mutum haka kawai, dole ne ku yi ƙoƙari wajen samar da su. Hanyar samar da su kuwa ita ce dukkan ma'auratan su so junansu. Wataƙila ku tambaya ta ya ya? Kamar yadda ake cewa ne, "ba a iya tabbatar da so da ƙauna ta hanyar ƙarfi da tursasawa", lalle haka ne don kuwa so…
Read More
Ranar Hausa yaudara ce!

Ranar Hausa yaudara ce!

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Bikin Ranar Hausa ba shi da asali ko kaɗan kuma waɗanda ke kanbama yin sa ba Hausawa ba ne. Mutane masu sa ka hula hana sallah wai su ne za su yi taron raya al’adun Hausawa! Wannan biki da wasu matasa su ka kirkira ba tare da tuntuɓar dattawa da sauran manyan malaman jami’a ba musamman ABU, BUK da UDUS na nuna yadda tarbiyya ta taɓarɓare a tsakanin matasa da ke yin abun da su ka ga dama don sun ga yadda Dan Daudu ma zai yi ta yin shakiyancinsa amma ba a damu ba, in…
Read More
Yunƙurin Tinubu na farfaɗo da tsaron Nijeriya 

Yunƙurin Tinubu na farfaɗo da tsaron Nijeriya 

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A yayin da nake wannan rubutun iyalai da ’yan uwan jami’an ’yan sandan nan su 10 da ’yan ta'adda suka hallaka a yayin artabun da suka yi a yankin Makuku na ƙaramar Hukumar Sakaba a Jihar Kebbi, suna nan cikin alhini da jimami, sakamakon kisan gillar da aka yi musu. Wannan babban koma baya ne ga harkar tsaro, da kuma yaƙin da ake yi da ’yan ta'adda da masu ɗauke da makamai suna cutar da al'umma. A yayin da ake kukan jami’an tsaro sun yi ƙaranci, ’yan ta'adda na samun goyon bayan matasa zauna-gari-banza don cimma…
Read More
Ana zargin rufe otel ɗin Sandaji a Lafia na da alaƙa da siyasa

Ana zargin rufe otel ɗin Sandaji a Lafia na da alaƙa da siyasa

Daga JOHN D. WADA a Lafia Rufin wucin gadi na otel ɗin Sandanji da ke Lafia wanda Alhaji Abubakar Shehu Usman na rukunin kamfanonin Sandanji Group of Companies ke mallaka ya haifar da ayar tambayoyi kan ko wannan matakin gwamnatin jihar lamari ne na tsaftar muhalli kawai ko kuma yana da alaƙa da siyasa. A kwanan nan ne dai gwamnatin jihar ta Nasarawa ta ma'aikatar muhalli da albarkatun ƙasa ta rufe otel ɗin bayan wani ambaliyar ruwa da ya auku a kewayen wurin da otel ɗin ya biyo bayan wani ziyarar duba da ido da kwamishiniyar ma’aikatar muhallin ta jihar…
Read More
Ba a ƙetare Kudancin Nasarawa ba a kasafin 2026, inji Akolo Peters

Ba a ƙetare Kudancin Nasarawa ba a kasafin 2026, inji Akolo Peters

Daga JOHN D. WADA a Lafia Daraktan kasafi a ma’aikatar kuɗi da kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki ta jihar Nasarawa Akolo Peters Ataka ya musanta zargin cewa gwamnatin jihar ta yi watsi da mazaɓar Sanatan Kudancin jihar musamman ƙananan hukumomin Obi da Doma da Awe da kuma Keana a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026. Peters Ataka wanda ya bayyana kasafin a matsayin “kasafin haɗin kai na dabaru”, yana mai cewa an tsara shi ne domin ya shafi kowane fanni a jihar kuma ya tabbatar da cewa mazaɓu uku na sanata da ake dasu a jihar duk sun amfana da shirye-shirye…
Read More
Dakta Steven ya gargaɗi matasa kan tayar da zaune tsaye

Dakta Steven ya gargaɗi matasa kan tayar da zaune tsaye

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Babban sakatare a ma’aikatar matasa da raya wasanni ta jihar Nasarawa Dakta Stephen Iliya Sasetu ya yi kira na musamman da a riƙa shigar da matasa cikin ayyuka masu amfani domin daƙile zaman banza da kuma inganta zaman lafiya a jihar. Sasetu ya bayyana haka ne ranar Talata na mako da ake ciki yayin da yake jawabi ga manema labarai a ofishinsa dake ma'aikatar a Lafia gabanin gudanar da ayyukan bikin ranar matasa ta duniya na bana. Yace akwai buƙatar a haɗa kan matasa tare waje guda a kuma yi musu jawabi don a…
Read More