ukarofi

12485 Posts
Kwamred Maiwada ya zama shugaban NLC na riƙo a Katsina

Kwamred Maiwada ya zama shugaban NLC na riƙo a Katsina

ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa reshen jihar Katsina, ta naɗa Kwamared Nasiru Wada Mai'adua a matsayin zhugaban ƙungiyar na riƙon ƙwarya. Naɗa shi shugaban ƙungiyar na riƙon ƙwarya ya biyo bayan, aje muƙamin da shugaban ƙungiyar na Jiha Comrade Hussaini Hamisu Yanduna ya yi bayan zama babban Sakatare a Gwamnatin Jihar Katsina. Kwamred Nasiru Wada Mai'adua kafin naɗa shi muƙamin shugaban ƙungiyar ƙwadagon na riƙon ƙwarya, shine shugaban ƙungiyar ma'aikatan ƙananan hukumomi ( NULGE )ta Jihar Katsina.
Read More
Mutane biyar sun mutu sakamakon rushewar gine-gine a Kano

Mutane biyar sun mutu sakamakon rushewar gine-gine a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Mutane biyar ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 10 suka tsira bayan rushewar wasu gine-gine guda biyu da suka faru a ƙananan hukumomin Kumbotso da Fagge na Jihar Kano. Lamarin ya faru ne a ranar Asabar a unguwar Gaida da ke Kumbotso, da kuma Kurna da ke Fagge. Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano ta ce ta samu kiran neman agaji da misalin ƙarfe 2:34 na rana da kuma 2:40 na rana, bi da bi. A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano Saminu Abdullahi, ya…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe mutum bakwai a Katsina

‘Yan bindiga sun kashe mutum bakwai a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ƙasurgumin ɗan bindiga Kachalla Maha da mutanen sa sun kashe mutum bakwai a ƙauyen Guru garin Sukuntuni na ƙaramar hukumar Kankia. A hira da yayi a wata kafar sadarwa ta JBC Malam Abubakar Tijjani daga garin Sukuntuni ya bayyana cewa Kachalla da mutanen sa sun shiga gida gida su kai ta harbin mutanen ƙauyen tare da Kona Gidaje. Yace wannan hari da Kachalla ya kai a ƙauyen ramakon gayyace domin a kwanakin baya sun shiga ƙauyen da niyar satar dabbobi amma mutanen ƙauyen su kai fito na fito da 'yan bindigan har ta kai ma…
Read More
‘Yan sanda sun kama wani mutum bisa laifin cin mutuncin Alqur’ani a Kebbi

‘Yan sanda sun kama wani mutum bisa laifin cin mutuncin Alqur’ani a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Rundunar 'yan sandan jihar Kebbi ta kama wani mutum mai suna Abubakar Musa ɗan asalin ƙauyen Rafin Mose da ke ƙaramar hukumar Zuru bisa ga laifin cin mutuncin Alqur'ani mai tsarki. Da ya ke zantawa da wakilin Jaridar Blueprint Manhaja, Kakakin rundunar 'yan sanda Sufurtanda Bashir Usman ya bayyana cewa an kama wannan mutum ne bisa zargin haɗa baki da Rabi'u Tela da matar sa Zara'u Hassan da kuma Hamza Zango bisa ga laifin surkulle da keta haddin al'umma da kuma cin mutuncin Alqur'ani mai tsarki. Ya ƙara da cewa bincike ya nuna sauran abokan…
Read More
Gambo Sawaba: Matar da ta ƙwato ’yancin matan Arewa da gwagwarmayarta

Gambo Sawaba: Matar da ta ƙwato ’yancin matan Arewa da gwagwarmayarta

“Ta ɗaga murya kan matsalolin da mata ke fuskanta” Daga AISHA ASAS  Ci gaba daga makon jiya. Nasarorin da Hajiya Gambo Sawaba ta samu: Kodayake tarihin Hajiya Gambo Sawaba ya cika da wahalhalu, hakan bai hana ta barin gado mai ɗorewa ba. A zahiri ma, irin ƙalubalen da ta sha ne suka ƙara bayyana girman nasarorin da ta cimma, domin ta yi tasiri a lokacin da mata ba su da isasshen damar shiga harkokin jama'a. Daga cikin manyan nasarorinta akwai karya shingen da ya hana mata shiga siyasa a Arewacin Najeriya. A lokacin da aka ɗauki siyasa a matsayin abin…
Read More
Yahaya Augie ya yaba wa gwamnan Kebbi kan zaɓen Ibrahim Augie

Yahaya Augie ya yaba wa gwamnan Kebbi kan zaɓen Ibrahim Augie

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Shugaban ƙaramar hukumar Augie Honarabul Yahaya Muhammed Augie ya yaba wa Gwamna Nasir bisa ga zaƙulo Alhaji Ibrahim Augie a matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar Kebbi.Ya bayyana haka ne a garin Augie mahaifar sabon ɗan takarar mataimakin gwamnan.Ya ce ba shakka gwamnan ya ɗauko mutum mai dattako da kuma sanin makamar aiki wanda ya goge. Ya bayyana cewa wannan ya nuna irin soyayya da mutuntawar sa da mutanen masarautar Argungu saboda wannan ba ta tsaya ga Ibrahim Augie ko ƙaramar hukumar Augie kaɗai ba ce.Ya kuma bayar da tabbacin goyon bayan sa tare da yin…
Read More
Nagarta ke sa a bai wa mutum sarauta – Sarkin Zabarmawan Kabi

Nagarta ke sa a bai wa mutum sarauta – Sarkin Zabarmawan Kabi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Sarkin Zabarmawan Kabi Honarabul Sama'ila Abdulmumini Kamba (Ganda) tsohon kakakin majalisar dokoki ta jihar Kebbi ya bayyana cewa nagarta ce sanya a bai wa mutum sarauta.Ya yi wannan bayanin ne jim kaɗan bayan kammala naɗin sa a matsayin Kakakin Gwandu a fadar Sarkin Gwandu ƙarshen makon nan lokacin da ya ke zantawa da manema labarai. Alhaji Sama'ila Ganda ya ce na farko dai ya yi aiki da mai martaba Sarkin Kabin Argungu a baya wanda kuma basaraken ya ga irin ƙoƙarin da ya ke yi a wajen aiki da kuma fafutukar da ya ke yi…
Read More
Ƙirƙiro masarautu ke janyo mutane kusa da gwamnati – Garba Zarummai

Ƙirƙiro masarautu ke janyo mutane kusa da gwamnati – Garba Zarummai

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Sabon Uban ƙasar Shiko Alhaji Garba Zarummai Fana ya bayyana ƙirƙiro masarautu a matsayin wata hanya ta kusantar al'umma ga gwamnati.Ya bayyana haka ne lokacin da ya ke zantawa da wakilin Jaridar Blueprint Manhaja a garin Fana. Sabon basaraken ya bayyana cewa sanin kowa ne yanzu akwai yawan al'umma saɓanin inda aka fito saboda haka akwai buƙatar al'ummar da a ke jagoranci su kusanci hukumomi tun kama daga masarautu zuwa gwamnati. Ya kuma yi kira ga hakiman sa da limamai da ke yankin masarautar sa da su ba shi goyon baya domin samun nasara a…
Read More
Sakataren Gwamnatin Yobe ya cancanci sarautar Jigon Fika – Fatima Paga

Sakataren Gwamnatin Yobe ya cancanci sarautar Jigon Fika – Fatima Paga

Daga ABUBAKAR A BOLARI Jami’ar kula da harkokin mata ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UN Women) a jihar Yobe ga gwamna Mai Mala Buni, Hajiya Fatima Muhammad Paga, ta bayyana naɗa Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG), Dakta Muhammad Goje, a matsayin Jigon Fika da Sarkin Fika, Alhaji (Dakta) Muhammadu Abali Ibn Muhammadu Idrissa, CON, ya yi, a matsayin abin da ya dace. A cikin saƙon taya murna da ta fitar, Paga ta ce karramawar ta nuna irin shekaru na sadaukarwar da Goje ya yi wajen hidimar jama’a da kuma gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban jihar Yobe da jin daɗin al’ummarta.…
Read More
Jagoran Iran ya naɗa sabbin shugabannin soji

Jagoran Iran ya naɗa sabbin shugabannin soji

Jagoran Iran, Mojtaba Khamenei, ya naɗa manyan hafsoshin sojin ƙasar guda biyu a wasu muƙamai masu matukar muhimmanci, yayin da ƙasar ke ci gaba da fuskantar matsin lambar tsaro da rikicin soja a yankin Gabas ta Tsakiya. A cikin sanarwar da ofishinsa ya fitar ranar Litinin, Khamenei ya naɗa Manjo Janar Ali Abdollahi a matsayin sabon shugaban hafsoshin rundunar sojin Iran, yayin da Birgediya Janar Ahmad Vahidi ya zama sabon kwamandan rundunar Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC). Kafin naɗin nasa, Abdollahi shi ne shugaban hedikwatar Khatam al-Anbiya ta tsakiya, wata babbar cibiyar rundunar sojin Iran da ke da alhakin haɗa…
Read More