ukarofi

12485 Posts
Nijeriya na buƙatar haɗin kan addinai fiye da kowane lokaci

Nijeriya na buƙatar haɗin kan addinai fiye da kowane lokaci

Matsalolin tsaro da Nijeriya ke fama da su sun kai wani matsayi mai matuƙar tayar da hankali, yayin da illolinsu ke yaɗuwa a sassa daban-daban na ƙasar. Saboda haka, bai kamata ƙasar ta ci gaba da barin bambance-bambancen addini, ƙabila da siyasa su zama abin da ke raba kan al’umma ko ke gurgunta haɗin gwiwar da ake buƙata wajen tunkarar matsalar tsaro ba. A saboda haka ne kiran da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya yi na neman ’yan Nijeriya su haɗa kai wajen yaƙi da rashin tsaro ya dace da a mara masa baya sosai.…
Read More
Sani Tadurga zai jagoranci yaƙin neman zaɓen jam’iyyar ADC a Kebbi

Sani Tadurga zai jagoranci yaƙin neman zaɓen jam’iyyar ADC a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Jam'iyyar ADC a jihar ta tsayar da Honarabul Sani Tadurga a matsayin wanda zai jagoranci yaƙin neman zaɓen ta mai zuwa.Wannan ya biyo bayan wani zama da masu ruwa da tsaki suka gudanar a garin Birnin Kebbi ƙarƙashin jagorancin ɗan takarar kujerar gwamnan jihar Alhaji Abubakar Chika Malami SAN ranar Talatar da ta gabata.Da ya ke zantawa da wakilin Jaridar Blueprint Manhaja shugaban jam'iyyar ADC a jihar Kebbi Injiniya Sufiyanu ya bayyana cewaHonarabul Sani Tadurga wanda tsohon mataimakin kakakin majalisar dokoki ta jihar Kebbi ne kuma jigo a siyasar jihar kuma duk an amince da…
Read More
Masarautar Koko ta yaba wa Gwamna Nasir kan ƙirƙiro hakimai takwas

Masarautar Koko ta yaba wa Gwamna Nasir kan ƙirƙiro hakimai takwas

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Masarautar Uban ƙasar Koko da ke jihar Kebbi ƙarƙashin jagorancin Alhaji Mohammed Bello Koko II ta yaba wa Gwamna Malam Nasir Idris bisa ga ƙirƙiro sababbin hakimai guda takwas daga cikin masarautar. Ya yi wannan bayanin ne a fadar sa da ke garin Koko sa'ilin da ya ke zantawa da wakilin Jaridar Blueprint Manhaja ranar Larabar da ta gabata.Basaraken ya ce, A madadin sa da ilahirin al'ummar wannan masarautar ta Koko suna miƙa godiya ga mai girma gwamna Malam Nasir Idris da kuma masarautar Gwandu bisa ga wannan gagarumin mataki na ƙara yawan hakimai a…
Read More
Na daɗe ina tara labarai a kaina, ban san ta ina zan fara ba – Aishacool

Na daɗe ina tara labarai a kaina, ban san ta ina zan fara ba – Aishacool

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Aisha Adam, wacce aka fi sani da Aishacool, na daga cikin matasan marubuta mata da tauraron su ke haskawa a duniyar rubutun Hausa. Ta rubuta littattafai da yawansu ya zarta goma, waɗanda suka taɓo ɓangarori daban-daban da suka shafi zamantankewar al'umma. Marubuciyar ta kasance Ma'aikaciyar jinya ce kuma mai sha'awar aikin jarida. Ta shaidawa wakilin Manhaja Blueprint, Abba Abubakar Yakubu cewa abin da ya fi bata sha'awa a harkar rubutun adabi shi ne yadda rubutun da take yi yake tasiri a rayuwar wasu. A yi karatu lafiya.  MANHAJA: Ina so ki gabatar mana da kan ki. …
Read More
Abin da ya sa na rubuta labarin ‘Yar Mulki – Faridat Hussaini Masheliya 

Abin da ya sa na rubuta labarin ‘Yar Mulki – Faridat Hussaini Masheliya 

Daga MUKHTAR YAKUBU A yanzu haka dai mawaƙiyar yabon Manzon Allah Kuma 'yar gwagwarmaya Faridat Hussaini Masheliya ta rikide ta zama cikakkiyar marubuciya. Don kuwa a 'yan kwanakin nan ta fara tallan sabon littafin ta da take shirin fitar da shi a nan da ɗan lokaci mai zuwa. Littafin mai suna 'Yar Mulki' wanda kuma an fassara shi zuwa Turanci, don haka zai fito kala biyu ne na Turanci da kuma na Hausa. Domin jin abubuwan da littafin ya ƙunsa da dalilin ta na fito da shi, wakilinmu ya tattauna da ita don haka sai ku biyo mu ku ji…
Read More
Majalisar dokokin Nasarawa ta tantance sabbin kwamishinoni da Gwamna Sule ya naɗa

Majalisar dokokin Nasarawa ta tantance sabbin kwamishinoni da Gwamna Sule ya naɗa

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Majalisar dokokin jihar Nasarawa ta tantance tare da tabbatar da sabbin kwamishinoni takwas da gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule ya gabatar ma ta domin a naɗa su cikin majalisar zartarwa ta jihar. Shugaban majalisar dokokin Rt. Hon. Dr. Danladi Jatau ne ya bayyana haka yau Laraba yayin zaman majalisar a Lafiya bayan an yi tantancewar ga waɗanda aka zaɓa. Shugaban bayan ya taya su murna kan wannan naɗin da ya cancanta ya kuma buƙace su riƙa aiki da gaskiya da riƙon amana bayan an rantsar da su. Wakilin mu a jihar ya kuma ruwaito…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da rabon hatsi ga masu buƙata ta musamman a Katsina

Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da rabon hatsi ga masu buƙata ta musamman a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya ƙaddamar da rabon buhunan hatsi mai nauyin kilogiram 100 ga masu buƙata ta musamman da matan da suka rasa mazajen su a Jihar. Kayan abincin sun haɗa da buhunan masara ,dawa da gero buhu 30,000 kowanne. A jawabin sa Gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa wannan tallafi ba shine na farko ba, ya ce a kwanan baya gwamnati ta tallafa wa masu sana'ar koko da ƙosai da kuma tallafin kuɗi a cikin watan azumin Ramadan. Ya ƙara da cewa gwamnatin sa ta tallafa wa mata 7,220 a…
Read More
Gwamnan Kano Ahmed Daku

Gwamnan Kano Ahmed Daku

Ahmed Mohammad Daku an haife shi kuma ya yi karatunsa a Katsina. Ya halarci Barewa College daga shekarar 1958 zuwa 1962, sannan ya ci gaba da karatu a Okene Secondary School daga 1962 zuwa 1965. Aikin Soja: A shekarar 1967, Ahmed Daku ya shiga Nigerian Defence Academy, inda aka ba shi muƙamin Second Lieutenant shekara guda bayan haka. Ya shiga yakin basasar Nijeriya a matsayin jagoran dakaru da kwamanda, sannan daga shekarar 1969 zuwa 1972 ya kasance kwamandan batir. An horar da shi a fannin makaman harbo-harbo (Artillery). Ya halarci Royal School of Artillery da ke Larkhill sau biyu, daga…
Read More
Me ya sa wasu ‘ya’ya ke bijire wa iyayensu?

Me ya sa wasu ‘ya’ya ke bijire wa iyayensu?

Daga MUKHTAR YAKUBU  Tasirin rikicin iyaye ga ƙwaƙwalwar yara Allah maɗaukakin Sarki ya ce:"Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku tsare kanku da iyalanku daga wuta." (Suratut-Taḥrīm: 6) Iyaye da yawa suna tambaya: "Me ya sa ɗana ko 'yata ba sa jin magana?"  Ko kuma: "Me ya sa yaro yake da taurin kai?" Sau da yawa ana kallon yaro ne kawai. Amma ilimin halayyar ɗan adam yana nuna cewa dole ne a kalli gidan da yaron ya taso kafin a yanke hukunci a kansa. ƙwaƙwalwar yaro tana gina kanta ne daga abin da take gani. Lokacin da yaro yake ƙarami,…
Read More
Me ya sa ake yawan mantawa da ƙafa a kwalliya?

Me ya sa ake yawan mantawa da ƙafa a kwalliya?

Daga AISHA ASAS  Akwai abubuwan da mutum kan yi wa kansa ba tare da ya ɗauke su a matsayin wani nau'in kulawa ta musamman ba. Wanke fuska, shafa mai, gyaran gashi, tsaftace farce da neman kayan kwalliya masu kyau duk suna daga cikin abubuwan da mutane da dama suka saba yi domin su kasance cikin tsari. Amma idan aka tambayi mutum yadda yake kula da ƙafafunsa, akwai yiwuwar amsar ta zama daban. Wataƙila ya tuna da lokacin da zai yi pedicure, ya shafa mai ko ya gyara farcen ƙafa. Amma kulawar kafa ta fi haka nisa. Domin kafin takalmi ya…
Read More