Batun Miƙa ‘yan gudun hijira ya nuna halayyar ƙasashen Yamma

Daga BELLO WANG

‘Yan gudun hijira mutane ne mafi fama da mawuyacin hali a duniya. Idan dai akwai dama, to, ba za su yi watsi da gidajensu, da barin iyalai, har su fita zuwa wata ƙasa ta daban ba, inda suke jure zaman rayuwa cike da wahalhalu. Sai dai yanzu har ana ƙara wulakanta su: Ƙasar da suke ƙaura cikinta ka iya tusa keyarsu zuwa wani wuri mai nisa, inda ba su taba tunani ko tsammanin zuwa ba.

A ranar 14 ga wata, kotun kare haƙƙin dan Adam ta nahiyar Turai ta hana tashin wani jirgin sama mai daukar nauyin jigilar ‘yan gudun hijira daga ƙasar Birtaniya zuwa Rwanda. Kafin afkuwar lamarin, ƙasar Birtaniya da Rwanda sun ƙulla wata yarjejeniya, inda aka daddale cewa, Birtaniya zata biya kuɗi fam miliyan 120 ga Rwanda, don ƙasar Rwandan ta karbi ‘yan gudun hijira da suka yi satar ƙetarawa zuwa ƙasar Birtaniya. Ko da yake, ba a fara gudanar da yarjejeniyar ba tukuna, sakamakon kin amincewar da ɓangarorin ƙasa da kasa suka nuna, ciki har da hukumar ‘yan gudun hijira ta MƊD suka nuna. Amma gwamnatin ƙasar Birtaniya tana ci gaba da neman aiwatar da yarjejeniyar.

Me ya sa ake kin amincewa da matakin da ƙasar Birtaniya ta ɗauka?

Saboda da farko dai, ƙasar Birtaniya, da Amurka, da sauran ƙasashen yammacin duniya, laifinsu ne yadda suka haddasa matsalar samun tarin ‘yan gudun hijira a duniya. Wadannan ƙasashe sun kaddamar da yake-yake a ƙasashen Iraki, da Afghanistan, da tsoma baki tare da tsananta yanayin rikici a Syria, da Libya, da Venezuela, da dai sauransu. Irin matakan da suka ɗauka su ne ainihin dalilan da suka haddasa ƙaruwar ‘yan gudun hijira a duniya. Saboda haka ya kamata ƙasashen yamma su dauki nauyin kula da ‘yan gudun hijira, maimakon a tusa ƙaryarsu zuwa wata ƙasar dake nahiyar Afirka.

Ban da wannan kuma, matakin ƙasar Birtaniya ya nuna wani yanayi na rashin adalci, inda matukar akwai kuɗi, to, ana iya yin kome. Su ƙasashe masu sukuni, sai su biya kuɗi, sa’an nan za su iya magance ɗaukar nauyin kulawa da ‘yan gudun hijira. Ganin haka zai sa su ta da rikici, da lalata yanayin zaman rayuwar jama’ar sauran ƙasashe, ba tare da wata damuwa ba. Idan an samu ‘yan gudun hijira, sai a tusa ƙaryarsu zuwa ƙasashe masu tasowa, ba tare da tsoron samun wani tasiri daga lamarin ba.

‘Yan gudun hijira

Sa’an nan lamarin ya nuna halayyar ƙasashen yamma a fannin haƙƙin dan Adam. Da ma ƙasashen suna kallon kansu a matsayin “Masu kare haƙƙin dan Adam a duniya”, har ma su kan tsoma baki a harkokin cikin gida na sauran ƙasashe. Sai dai ko da gaske ne suna kare haƙƙin dan Adam a duniya?

Idan mun dauki ƙasashen Amurka da Birtaniya a matsayin misali. Ƙasar Amurka ta yi ta ƙaddamar da yaƙe-yaƙe a kasashe da dama, inda take kisan mutanen ƙasashen, da aiwatar da mulkin danniya a duniya. Yayin da a nata ɓangaren, ƙasar Birtaniya tana kallon ‘yan gudun hijira a matsayin kayayyaki, tana neman mika su ga sauran ƙasashe ba tare da kulawa da yanayin da waɗannan mutane suke ciki ba. Ta waɗannan batutuwa, za mu iya ganin cewa, ƙasashen yamma kullum suna neman sanya sauran ƙasashe kulawa da haƙƙin dan Adam, maimakon su da kansu su yi haka.

Batun nan ya shaida gaskiyar wata tsohuwar magana dake cewa: “A yi bincike kan halayyar wani mutum bisa aikace-aikacensa, maimakon kalmomin da ya faɗa”.