Hidimar aika saƙonni na ƙasar Sin ya ƙaru da kashi 3.3 a watan Mayu

Daga CMG HAUSA

Kamfanonin dake ayyukan hidimar aika sakonni na ƙasar Sin ya samu bunƙasuwa a cikin watanni biyar na farkon wannan shekarar, kamar yadda alƙaluman da hukumar ƙididdigar aika sakonni ta ƙasar suka nuna.

A cewar hukumar, daga watan Janairu zuwa Mayun bana, kamfanonin aika sakonnin sun gudanar da ayyukan hidimomin aika kayayyaki da ya kai biliyan 40.95, inda ya ƙaru da kashi 3.3 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin lokacin bara.

Adadin kuɗaɗen shigar da aka samu daga hada-hadar cinikayyar, ya kai RMB yuan biliyan 400.55, kwatankwacin dala biliyan 60 a cikin wannan wa’adi, inda ya karu da kashi 2 bisa 100 bisa na shekarar bara.

Shanghai shi ne ke sahun gaba daga cikin biranen ƙasar Sin ta fannin samar da kuɗaɗen shiga daga ɓangaren hada-hadar hidimar aika saƙonni kayayyaki a cikin watanni biyar ɗin da suka gabata, sai biranen Guangzhou, da Shenzhen, da Jinhua da Hangzhou dake bi masa baya.

Alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa, adadin kuɗaɗen shigar kasar Sin a fannin aika sakonni ya ƙaru da kashi 5.9 idan an kwatanta da na makamancin lokacin bara, adadin ya kai RMB yuan biliyan 531.78 tsakanin watan Janairu zuwa Mayu. A watan Mayu kaɗai, fannin ya samu bunƙasuwar kashi 4.4 bisa 100.

Fassarawa: Ahmad