Buhari ya jajanta wa iyalan waɗanda haɗarin jirgin ruwa ya ratsu da su a Neja

Daga FATUHU MUSTAPHA

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya nuna alhinisa dangane da haɗarin jirgin ruwan da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 28 a jihar Neja.

Kamar yadda hadiminsa kan sabbin kafafen yaɗa labarai, Bashir Ahmad, ya wallafa a shafinsa na twita a wannan Litinin, Shugaba Buhari ya nuna tausayawarsa kan ibtila’in, kana ya jajanta wa ahalin waɗanda suka rasu a haɗarin da ma waɗanda suka ji rauni.

A cewar Buhari haɗarin abin tashin hankali ne musamman ma kasancewar wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa ‘yan gudun hijira ne masu neman mafaka.

Buhari ya yaba da ƙoƙarin duka waɗanda suka bada gudunmawarsu wajen ceto mutane da kuma gano gawarwakin waɗanda suka rasu a haɗarin.

A yammacin Asabar da ta gabata wannan mummunan abin tashin hankali ya faru a yankin ƙauyenTijana da ke cikin ƙaramar hukumar Munya bayan da matafiyan suka baro Zumba daga ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *