Canjin ‘yan takara: INEC ta gindaya sharuɗɗa ga jam’iyyun APC, LP da sauransu

Daga AMINA YUSUF ALI

Hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) a ranar Juma’ar da ta gabata ta zana sharuɗɗan da ya kamata jam’iyyu su cika kafin su samu damar canza ‘yan takarar mataimakin shuganan ƙasa kafin nan da kakar zaɓen ta 2023.

INEC ta ba a wannan sharaɗin ne duba a yadda wasu jam’iyyun suka tsayar da sojan gona da suka aike da sunansa zuwa ga INEC, kafin su samu ɗan takarar na din-din-din.

Wato dai kamar yadda ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya miƙa sunan Doyin Okupe a atsayin mataimainsa na wucin gadi. Sannan shi ma Bola Ahmed Tinubu, tsohon gwamnan Jihar Legas kuma ɗan takarar shugabancin ƙasar nan a ƙarƙashin jam’iyya APC shi ma ya ba da sunan Ibrahim Masari, a matsayin mataimakinsa na wuccin gadi.

Kwamishinan yaɗa labarai da ilimtar da masu zaɓe na INEC, Festus Okoye, shi ya yi wannan bayani a wani shiri na tashar gidan Talabijin na Channels Television. Inda ya ƙara da cewa, har sai jam’iyyun siyasa sun cikasa waɗannan sharuɗɗan da ta gindaya na canjin ‘yan takara sannan hukumar za ta karɓi wasu sunayen bayan sunayen da aka tura mata tun farko.

Sharuɗɗan kuwa a cewar Mista Okoye su ne: babu jam’iyyar da aka yarda ta sauya ɗan takararta sai dai a yanayi guda biyu: Ko dai idan ɗan takarar ya mutu ko kuma idan ya janye daga takarar don ƙashin kansa.

“Kuma kowanne ɗan takara da ya janye dole a aike da rubutacciyar wasiƙa daga zaɓaɓɓen ɗan takarar zuwa ga jam’iyyar da yake wa takara yana shaida cewa, ya janye daga takarar don ra’in kansa tare da shaidar rantsuwar kotu”.

“ Daga nan kuma sai jam’iyyar ta tura wasiƙar zuwa ga Hukumar ta INEC. Waɗannan su ne takardun shaidar janyewar waɗanda a tare da su za a haɗa da sunan wanda zai gaji takarar”.

A cewar INEC, maganar janyewar takarar ra’ayin ɗan takara ne. Kuma shi ke da wuƙa da nama. Bayan shi ba wanda yake da wannan ikon.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *