26
Jun
Daga AISHA ASAS Mawaƙi Rema ya kafa tarihi a duniyar waƙoƙi ko in ce a mawaƙan Afrika, inda waƙarsa ta 'Baby Calm Down' ta zama waƙar Afirka da aka fi sauraro a Amurka. Waƙar Calm Down ta mawaƙin Najeriya, Rema ta ci gaba da kafa tarihi, inda ta zamo ta ɗaya a cikin waƙoƙin ƴan Afirka (Afrobeats) da aka fi sauraro a Amurka. Haka nan ta zamo waƙar ƴan Afirka ta farko a tarihi da aka saurara sama da sau biliyan ɗaya a Amurka, kamar yadda shafin lura da waƙoƙi na Chart Data ya bayyana a shafinsa na X. Ko…
