13
Sep
Daga AISHA ASAS Kiɗa da waƙa wata daɗaɗɗiyar al'ada ce ko in ce ɗab'i da ba kasafai kake samun al'ummar da ba ta da irin nata da ta ke nishaɗanta da ita ba. Wannan ne ya sa duk inda ka ratsa za ka tarar da kiɗa da waƙa ya rigaka zuwa, sai dai ka tarar da ba irin wanda ka baro ne a inda ka fito ba. Za mu iya kiran waƙa a matsayin wasiƙu zuwa ga zukatan mutane, hakan zai sa da wahala ka rasa wadda aka yi domin taka zuciyar. Kazalika bincike ya tabbatar waƙa na kan gaba…
