Nishadi

Daga hasken kyamara zuwa hasken ganye: Yadda jarumi John Dumelo ya zama allon kwaikwayo ga Jaruman Afirka

Daga hasken kyamara zuwa hasken ganye: Yadda jarumi John Dumelo ya zama allon kwaikwayo ga Jaruman Afirka

Daga AISHA ASAS  A tsawon lokaci, rayuwar jarumai ta fi shahara ne a inda hasken fitilu yake, tarukan biki da kuma duk wata sharholiya da ake yi da sunan wayewa. Wannan ne ya sa ba kasafai ka ke iya samun jarumin da ya shahara da bai mayar da hankali kan tara kayan ƙawa da birgewa ba. Wannan kuwa ya zama ɗaya daga cikin ɗabi'un da ake faɗa cikin jerin ababen da ke iya kai fitaccen jarumi ga talauci bayan duniya ta ajiye shi. Sai dai a ɓangaren shahararren jarumin fim ɗan Ghana, John Dumelo, abin ba haka ba ne, domin…
Read More
Hukumar NFC a shirye take ta bada goyon baya ga masu harkar fim – Ali Nuhu 

Hukumar NFC a shirye take ta bada goyon baya ga masu harkar fim – Ali Nuhu 

Daga MUKHTAR YAKUBU  Shugaban Hukumar kula da bunƙasa harkokin fim ta Nigerian Film Corporation' Ali Nuhu, ya bayyana ƙudirin hukumar na bada goyon bayanta ga dukan ayyukan da suka shafi harkar fim a ƙasar nan. Ali Nuhu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron horar da marubutan labarin fim da aka gudanar a ranar Asabar ɗin da ta gabata a ɗakin taro na Kannywood TV dake titin Muhammadu Buhari a cikin garin Kano. Tun da farko ya bayyana muhimmancin rubutun labari wanda ya kasance kashin bayan duk wani fim da za a shirya. Inda…
Read More
A bikin Ranar Jammaje na wannan shekarar za a  kalli sabon fim ɗin mu – Kabiru Jammaje 

A bikin Ranar Jammaje na wannan shekarar za a  kalli sabon fim ɗin mu – Kabiru Jammaje 

Daga MUKHTAR YAKUBU  A yanzu haka dai shirye-shirye suna fara kankama na bikin ranar Jammaje ta wannan shekarar ta 2025 wanda za a gudanar a ranar 30 ga Disamba a cikin sabuwar Jami'ar Bayero dake Kano. A wata sanarwa da kwamitin shirya taron ya fitar ta bayyana cewa taron na bana zai kasance na daban ne domin baya ga jawabai da za a saurara daga bakin manyan malamai, to kuma a ranar ne za a haska sabon fim ɗin kamfanin Jammaje Production mai suna 'Jamila Jammaje'. Haka nan a wani ɓangare na gudanar da taron za a yi bajekolin litattafai…
Read More
Turanci da boko ne ke hana ‘yan Kannywood shiga KILAF AWARD – Ahmad Sarari

Turanci da boko ne ke hana ‘yan Kannywood shiga KILAF AWARD – Ahmad Sarari

Daga MUKHTAR YAKUBU An bayyana tsarin boko da kuma Turanci da yake cikin gudanar da bikin' 'Kano Indigenous Languages Afrka Film Market and Festival' (KILAF AWARD) da cewar shi ne yake hana shigar 'yan Kannywood tsarin wanda mutane suke ganin 'yan fim ɗin Kannywood ba sa shiga ana damawa da su.Tsohon shugaban ƙungiyar kwararru ta masu shirya fim ta ƙasa MOPPAN Dakta Ahmad Muhammad Sarari ne ya bayyana hakan a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu dangane da taron KILAF AWARD na wannan shekarar da ya gudana a watan  Nuwambar da ya gabata. Dakta Ahmad Sarari ya fara ne da…
Read More
Yadda Ali Nuhu maida ’yan Arewa saniyar ware a Hukumar NFC – Ƙungiyoyi

Yadda Ali Nuhu maida ’yan Arewa saniyar ware a Hukumar NFC – Ƙungiyoyi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Haɗaɗɗiyar ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya a Kannywood (MOPPAN) da haɗin gwiwar ƙungiyar ’Yan Fim ta Arewa (AFMAN) sun nuna damuwa kan yadda ake ƙoƙarin mayar da su saniyar ware a harkokin Hukumar Kula da Finafinai ta ƙasa (NFC) tun bayan da Jarumi Ali Nuhu ya zama shugaban hukumar. A wata wasiƙa zuwa ga shi Darakta Manaja na NFC, Ali Nuhu, wacce Shugaban MOPPAN fitaccen jarumi kuma shugaban MOPPAN na ƙasa, Shehu Hassan Kano da Shugaban AFMAN kuma fitaccen furodusa Salisu Mohammed Officer suka rattaɓa wa hannu, ƙungiyoyin sun bayyana damuwarsu bisa yadda…
Read More
Tashar Saira Movies ta yi zarra a Arewa akan manhajar YouTube

Tashar Saira Movies ta yi zarra a Arewa akan manhajar YouTube

Daga AISHA ASAS  Tashar nuna finafinai ta Saira Movies ta yi zarra a jerin tashoshin YouTube a faɗin Nijeriya, inda ta kasance ɗaya daga cikin tashoshi 10 da ke kan gaba a duka faɗin ƙasar, inda ta zamo ta huɗu kuma tilo guda ɗaya kacal a cikinsu daga arewacin Nijeriya. A ranar 9 Disamba 2025, YouTube Nigeria ta ƙaddamar da wani sabon jerin ƙididdiga da ta kira “2025 Nigeria Creators & Influencers Ranking & Recap Tool.” Wannan sanarwa ta zo ne ta kafar yanar gizo da kafofin sadarwa — inda aka jera mawaƙa, masu barkwanci, masu shirya bidiyo (content creators)…
Read More
Dayo Amusa ta zama Mataimakiyar Shugaban ƙungiyar Jarumai ta Nijeriya

Dayo Amusa ta zama Mataimakiyar Shugaban ƙungiyar Jarumai ta Nijeriya

Daga AISHA ASAS  A ranar 8 Disamba 2025, Dayo Amusa, fitacciyar ‘yar fim daga Najeriya, ta samu nasarar zama National Vice President ta Actors Guild of Nigeria (AGN) a zaɓen ƙarshe da aka gudanar a Benin, na Jihar Edo. Wannan mataki ya nuna sabon salo a harkar shugabanci a masana’antar Nollywood, inda ake neman gyara, tsari da inganta harkokin fina-finai a kasa baki ɗaya. Dayo Amusa ta bayyana wannan matsayin a matsayin alamar amincewa da ƙoƙarin ta, tare da tabbatar da cewa zata yi aiki tuƙuru domin ganin ‘yan fim sun samu kariya, horo, da dama don ci gaba a…
Read More
Deepika Padukone na shirin haɗa fuska da Vicky Kaushal a fim ɗin Mahavatar

Deepika Padukone na shirin haɗa fuska da Vicky Kaushal a fim ɗin Mahavatar

A ranar 9 Disamba 2025, masana’antar Bollywood ta fara tattaunawa da fitacciyar jarumar Deepika Padukone domin haska ta a fim ɗin Mahavatar, fim ne mai taken tarihi da al’ada (mythological) wanda za ta jagoranta tare da Vicky Kaushal. Wannan mataki ya motsa tsumin sha’awa tsakanin masoya fim, musamman ma waɗanda ke son ganin waɗannan manyan taurari biyu sun haɗu a fim mai girma irin wannan.  Haɗin taurari biyu masu tasiri kamar Deepika da Vicky zai sa masoyansu cika sinima da kuma yin tsokaci a kafafen sada zumunta kamar dai yadda ake yi a yanzu tun kan fitar fim ɗin. Wannan…
Read More
Cin zafarin mata a masana’antun fim: Al’ada ko ɓata suna

Cin zafarin mata a masana’antun fim: Al’ada ko ɓata suna

Daga AISHA ASAS Cin zarafin mata a masana'antun fina-finai wani labari ne da ba ya tsufa, kuma yake yawan taka rawa lokaci zuwa lokaci, wanda a duk lokacin da ya taso yakan yi amon da za a ajiye komai a ba shi masauki na ɗan lokaci kafin a koma kan wasu ababen na daban. Kuma abinda ke ɗaure kai shi ne, a duk lokacin da ya taso a wata masana'anta sautinsa kan kai ga takwaranta ta wani ɓangare na duniya har ido ya kai can wanda zai yi wuya ba a samu wani koke a ɓangaren ba. Da wannan wasu…
Read More
Malam Nata’ala: Ko Kannywood ta yi masa hallaci?

Malam Nata’ala: Ko Kannywood ta yi masa hallaci?

Daga AISHA ASAS  Fitaccen jarumin Kannywood, Yakubu Mato, wanda aka fi sani da sunan “Malam Nata’ala”, ya rasu a daren Lahadi, 2 Nuwamba 2025, a Asibitin Jami’ar Maiduguri, bayan ɗaukar lokaci mai tsawo yana fama da rashin lafiya. Wannan babban rashi ne ga masana’antar Kannywood da kuma al’umma baki ɗaya, musamman a Arewacin Najeriya. Malam Nata’ala ya shahara ne a matsayin jarumin barkwanci wanda tauraruwar sa ta haskaka a lokacin da aka ya fara fitowa a cikin shirin Dadin Kowa, inda ya fito a matsayin malamin almajiri mai barkwanci, wanda ya ja hankalin masu kallo da dama tun daga shekarun…
Read More