18
Jan
Daga MUKHTAR YAKUBU A kwanakin baya kaɗan da suka gabata ne aka kammala ɗaukar wani sabon fim mai suna 'Kitso da Kwarkwata', wanda kamfanin shirya fina-finai mai suna Goldin Pin Multimedia ya ɗauki nauyin shiryawa. Mustapha Adam Muhammad shi ne ya zamo jagoran shirin, inda aka yi amfani da jarumai masu yawa – kama daga tsofaffin jarumai da kuma sababbi. Fim ne mai dogon zango, wanda da zarar an kammala shi za a nuna shi a manyan gidajen talabijin da kuma manhajar YouTube da sauran manhajojin kallo. Kamar yadda binciken Blueprint Manhaja ya tabbatar ma na, farkon shirya fim ɗin…
