Nishadi

Abin da ya sa ban damu da saka fitattun jarumai a finafinaina ba – Kabiru Musa Jammaje

Abin da ya sa ban damu da saka fitattun jarumai a finafinaina ba – Kabiru Musa Jammaje

DAGA MUKHTAR YAKUBU Bayan tsawon lokacin da ya shafe ba tare da ya fito da sabon fim ba, fitaccen furodusa Kabiru Musa Jammaje, wanda ya saba shirya finafinai da harshen Turanci a masana'antar Kannywood. A yanzu haka dai ya ci gaba da shirya sabon fim ɗin sa mai suna 'Princess of Galma,'. Wakilinmu ya tattauna da shi a game da yadda aikin fim ɗin yake da kuma manufarsa ta shirya wannan sabon fim ɗin, don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance MANHAJA: Kai ba sabo ba ne a cikin harkar fim a wannan masana'anta ta…
Read More
Zambo cikin aminci: Waƙoƙin Rarara a siyasar Kano

Zambo cikin aminci: Waƙoƙin Rarara a siyasar Kano

Daga FARFESA ABDALLA UBA ADAMU Fassara: HASSAN AUWALU MUHAMMAD A cikin shekaru 43 da suka gabata da na kasance mai bincike, akwai ɓangarori biyu da na ƙi karkatar da aikin bincikena akai: siyasa da addini. Idan kun ga hannuna a cikin ɗayan waɗannan biyun, wajen da na shahara ne, wato kan al'adun yaɗa labarai. Misali, da na yi rubuce-rubuce da yawa na Zikirin Anfasu na ‘yan Ƙadiriyya, ba na yi a matsayin ɗaya daga cikin mabiyan ɗariqar ba, sai dai a matsayina na mai binciken harkar kiɗe-kiɗe - na mai da hankali kan yadda suke dukan jikinsu tare da motsa…
Read More
Na jima Ina kallon harkar fim a matsayin sana’a mai kyau – Habiba Ɗorayi

Na jima Ina kallon harkar fim a matsayin sana’a mai kyau – Habiba Ɗorayi

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Habiba Isa Dorayi da aka fi sani da Habiba Dorayi matashiya ce da ta taso a masanaantar fim ta Kannywood. A tattaunawar ta da Ibrahim Hamisu, a Kano, za ku ji cikakken tarihinta da kuma yadda frodusoshi suke ribibin saka ta a fim, ku biyo mu: MANHAJ: Za mu so ki gabatar mana da kanki? HABIBA ƊORAYI: Sunana Habiba Isah, an fi sani na da Habiba Dorayi. Ko za ki ba mu taƙaitaccen tarihinki? An haife ni a Rano. Da kakanina suka rasu sai muka dawo cikin garin Kano. Na yi Primary, na yi secondry,…
Read More
Taron Afirika KILAF Award 2023: shirye-shirye sun kankama

Taron Afirika KILAF Award 2023: shirye-shirye sun kankama

DAGA MUKHTAR YAKUBU A daidai lokacin da a ke ci gaba da shirye shiryen bikin Bajekolin finafinai na Afirka 'African Indigenous Language Filims'. Mai taken 'Kano Indigenous Languages Of Africa Film Market & Festival' KILAF AWARD, da aka saba shiryawa duk shekara a garin Kano. A yanzu haka dai an kai ga matakin tantance finafinan da suka shiga gasar domin fitar da waɗanda za su kai matakin matakin cancanta da kuma wadanda ba su kai ba. Alƙalan gasar dai su bakwai ne da suka haɗa da Victor Okhoir, Emmanuel Emascalu, Charlas Okwuowulu, Falakemi Ogungbe, Izu Ojukwu, Charity Torut, da Alwine…
Read More
Jaruma Tonto Dikeh ta sauya sheƙa zuwa APC

Jaruma Tonto Dikeh ta sauya sheƙa zuwa APC

Jaruma a masana'antar Nollywood wadda ta tsunduma harkar siyasa, Tonto Dikeh, ta sauya sheƙa ta koma Jam'iyya mai mulki ta APC. Jarumar ta koma APC ne bayan da ta fice daga Jam'iyyar hamayya ta African Democratic Congress (ADC). Jarumar ta yi takarar mataimakin gwamna ƙarƙashin ADC yayin zaɓen 2023 a Jihar Ribas. A wannan Litinin ɗin ake sa ran Shugabar Matan APC ta Ƙasa, Dr Mary Alile, za ta karɓi Tonto Dikeh a Sakatariyar APC da ke Abuja da misalin ƙarfe 3 na rana. A shekarun baya-bayan nan, an ga yadda jaruman fina-finai na Arewaci da Kudancin Nijeriya suka ba…
Read More
Kusan duk wani fim da ake saka wa Arewa24 na ɗora murya akwai ni a ciki – Maryam Hotoro

Kusan duk wani fim da ake saka wa Arewa24 na ɗora murya akwai ni a ciki – Maryam Hotoro

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Maryam Ibrahim Hotoro da aka fi sani da Maryam Hotoro, jaruma ce a masana'antar fim ta Kannywood kana ma'aikaciya ce a tashar Arewa24, ƙwararriya a wajen fassara da kuma ɗora murya. A tattaunawar ta da wakilin Manhaja a Kano, Ibrahim Hamisu, za ku ji tarihinta da kuma yadda ta zama mawaƙiya inda har ta buɗe kamfanin waƙoƙin bikin aure. Ku biyu mu: MANHAJA: Za mu so ki gabatar mana da kanki? MARYAM HOTORO: Sunana Maryam Ibrahim Hotoro, amma anfi kirana da Maryam Hotoro. Za mu so ki ba mu taƙaitaccen tarihinki? An haife ni a…
Read More
Rasuwar Jaruma Binta Ola: Ba rabo da gwana ba…

Rasuwar Jaruma Binta Ola: Ba rabo da gwana ba…

Daga UMAR GARBA, a Katsina A ranar 3 ga Oktobo, 2023, Allah ya karɓi rayuwar shahararriyar jarumar Kannywood kuma ɗaya daga cikin mata da suka fara gudanar da wasan kwaikwayo a Arewacin Nijeriya, wato Hajiya Binta Suleiman, wadda aka fi sani da Hajiya Binta Ola Katsina. Marigayiya Hajiya Binta ta fara wasan kwaikwayo tun lokacin da ake wasan daɓe, wato kafin zuwan wasan kwaikwayo na talabijin da kuma fina finan zamani irinsu Kannywood.Wakilin Jaridar Blueprint Manhaja a Katsina, Umar Garba ya samu damar halartar gidan marigayiyar a Sabuwar Unguwa cikin garin Katsina inda iyalanta ke zaman ta'aziya. An haifi Hajiya Binta…
Read More
Allah Ya yi wa Jarumar Kannywood, Hajiya Binta Ola asuwa

Allah Ya yi wa Jarumar Kannywood, Hajiya Binta Ola asuwa

Daga UMAR GARBA a Katsina Allah Ya yi wa shahararriyar jarumar fina-finan Hausa, Hajiya Binta Ola rasuwa. Hajiya Binta ta rasu ne da misalin ƙarfe 3 na daren jiya Talata, a gidanta dake Sabuwar unguwa Ƙofar Ƙaura, dake jihar Katsina bayan gajeruwar rashin lafiya. Majiyar mu ta ce za a yi jana'izar marigayiyar a wannan Laraba da misalin ƙarfe 10 na safe a gidanta dake Sabuwar unguwa cikin garin Katsina.
Read More
Dalilin da ya sa na tsunduma siyasa duk da kasancewa ta limamin coci – Mawaƙi Banky W 

Dalilin da ya sa na tsunduma siyasa duk da kasancewa ta limamin coci – Mawaƙi Banky W 

Daga AISHA ASAS  Shahararren mawaƙin Nijeriya Olubankole Wellington, wanda aka fi sani da Banky W, ya bayyana dalilin sa na shiga siyasa har ya tsaya takara, duk da cewa, a yanzu shi limami ne na Coci. A cikin wata tattaunawa da ya yi da BBC, mawaƙin wanda a halin yanzu yake jagorantar wata Coci ya bayyana cewa, ya shiga harkar siyasa ne don ya canza ma'anar da mutane da yawa suke yi wa siyasa, inda suke kallon dukka wani ɗan siyasa a matsayin mutumin banza. Mawaƙin ya ce, shigar tasa siyasa har ya tsaya takara, zai zama wata ishara da…
Read More
Jaruma Anita ta yi allawadai da masu neman a yi gwajin DNA ga ɗan Mawaƙi Mohbad

Jaruma Anita ta yi allawadai da masu neman a yi gwajin DNA ga ɗan Mawaƙi Mohbad

Daga AISHA ASAS  Biyo bayan mutuwar mawaƙi Mohbad mai shekaru 27 da haihuwa, mutuwar da ta taɓa mutane da dama, wanda ta sa aka tada ƙura, da ta yi sanadin samun shahara ga mawaƙin fiye da lokacin da yake raye. Mutuwar wadda take ɗauke da ruɗani da neman sanin ababe da dama dangane da silar mituwar matashin mawaƙin. Da yawa sun zargi ubangidan mawaƙin, wato fitaccen mawaƙi Naira Marley, wanda aka ruwaito cewa, mawaƙi Mohbad ya jima yana kai kuken cin zafarin da yake masa a matsayin sa na ubangidansa, wanda har a wasu waƙoƙinsa yana ƙoƙarin bayyana halin da…
Read More