Nishadi

Kisan jaruma Laila Khan da iyalinta ya shiga tarihi a kotun Mumbai

Kisan jaruma Laila Khan da iyalinta ya shiga tarihi a kotun Mumbai

Daga AISHA ASAS  Al’umma sun sake tunawa da Laila Khan, wacce ta fito a fim ɗin Wafa: A Deadly Loɓe Story tare da Rajesh Khanna a shekarar 2008. Laila da iyalinta guda biyar sun gamu da ajalinsu a shekara ta 2011, a wani kisan gilla da ya girgiza Bollywood. A wannan mako, kotun Mumbai ta bayyana cewa, wannan kisan ya zama abin ban mataki wajen irin mummunan laifi, inda alƙalin ya bayyana shi a matsayin “rarest of rare”. Wannan kalma na nufin cewa laifin ya sha bamban ko in ce ya zama ɗaya cikin dubu na yadda aka saba gani…
Read More
A baya ina ganin kamar Ɗankwairo ya fi Shata iya waƙa – Salma Sa’id 

A baya ina ganin kamar Ɗankwairo ya fi Shata iya waƙa – Salma Sa’id 

Ina da burika sosai a kan waƙoƙin gargajiya - Salma Sa'id Daga MUKHTAR YAKUBU A rayuwa Allah ya kan samar da wasu daga cikin mutane masu basira a fannoni daban daban walau a cikin yara ko a cikin manya. Salma Sa'id tana daga cikin yara 'yan baiwa masu fasahar waƙa. Sai dai ita fasahar da take da ita ta daban ce a fagen waƙa. Domin kuwa fasahar da take da ita tana ɗaukar waƙoƙin gargajiya irin na su Shata da Dankwairo da sauran mawakan gargajiya ta rera. Wannan ya ba ta damar samun gayyata daga manyan makarantu da jami'o'i idan…
Read More
Hukumar tantance fina-finai ta mallaki hedikwata a Abuja bayan shekaru 30

Hukumar tantance fina-finai ta mallaki hedikwata a Abuja bayan shekaru 30

Hukumar Tantance Fina-Finai da Bidiyo ta Kasa (NFVCB) ta samu hedikwatarta ta dindindin a Abuja bayan kusan shekaru 30 tana gudanar da aiki ba tare da na dindindin ba. Wannan ci gaban ya zama babban tarihi ga hukumar. Wannan lamari ya tabbata ne a ranar Talata, lokacin da shugaban hukumar, Dakta Shuaibu Husseini, ya jagoranci tawagarsa wajen kai ziyarar ban girma ga Ministar Al’adu, Yawon Buɗe Ido, da Tattalin Arzikin Kirkire-Kirkire, Hajiya Hannatu Musa Musawa, domin nuna godiya bisa rawar da ta taka wajen tabbatar da mallakar wurin. Dakta Husseini ya bayyana cewa, sabon ginin, wanda Hukumar Yaƙi da Cin…
Read More
An naɗa Mawaƙi Aminu Ala jakadan Jami’ar ‘North-Eastern 

An naɗa Mawaƙi Aminu Ala jakadan Jami’ar ‘North-Eastern 

Daga MUKHTAR YAKUBU Likkafar Mawaƙi Aminu Ladan Abubakar Ala ta ƙara ɗagawa zuwa mataki na gaba inda ya samu jakadancin Jami'ar Arewa maso gabas wato 'North-Eastern University' . Kamar yadda ya tabbatar a saƙon sa na ranar Juma'ar da ta gabata. Aminu Ladan Abubakar Ala mai riƙe da sarautar Sarkin ɗiyan Gobir daga Masarautar Gobir Tsibirin Sarkin waƙar Masarautar Dutse kuma Dan Amanar Gidan Dabo Ya wallafa cewar " Saƙon Barka da Juma'a na wannan sati ya zo da busharar shaidar Jakadancin 'Noth-Eastern University Gombe," tare da hoton sa tare da Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar tare da mataimakin…
Read More
Kiɗa a ƙasar Hausa 

Kiɗa a ƙasar Hausa 

Daga HAFIZ ADAMU KOZA Gabatarwa: Ana zaton ɗan Adam ya fara amfani da kiɗa ne a lokacin da ya fara neman abinci ta hanyar farauta. Daga nan kuma da mutane suka fara yaƙe-yaƙe a tsakaninsu, sai sana’ar kiɗa ta ƙasaita (Ibrahim, 1983:ɓii). Masana adabi da al'adun Hausawa suna ganin busa ita ce abu na farko da Hausawa suka fara fahimta a matsayin wani nau’i na kiɗa (Salihu, 1985:1). Hausawa mutanen farko, sun fara amfani da wannan amo don yin sadarwa da kuma faɗakarwa. Sukan yi amfani da ƙaho wajen faɗakar da junansu bisa wani abu na murna ko na tsoro…
Read More
Yaushe Mohbad zai ‘mutu’ ne?

Yaushe Mohbad zai ‘mutu’ ne?

Daga AISHA ASAS  *Na gane wasan kwaikwayon da CP Uche ke yi – Iyabo Ojo * Zan bayyana batutuwan DNA da Iyabo ta tattauna a sirrance - VDM  *Iyabo Ojo ta rungumi wanda ya kamata ta tambaya – ’Yar uwar Mohbad *Portable ga VDM: Ka yi watsi da tafarkin adalci ga Mohbad Sanannen abu ne, mutum kan shahara ne akan abinda yake yi da ya samu karɓuwa ga jama'a, sai su kama sunansa a baki, su sanya soyayyarsa a zuciya, wanda ke kai a wasu lokuta ya rasa walwalarsa sakamakon kowa ya san shi kuma ana muradin ganin shi. Wannan…
Read More
‘Dilwale Dulhania Le Jayenge’ da ‘Kaakha Kaakha’: Fina-finan da suka kafa tarihi a zukatan masu son soyayya

‘Dilwale Dulhania Le Jayenge’ da ‘Kaakha Kaakha’: Fina-finan da suka kafa tarihi a zukatan masu son soyayya

Daga AISHA ASAS  'Sun tabbatar da cewa soyayya ba kawai da baki ake furtawa ba, sai da jajircewa da sadaukarwa' A duk faɗin duniya, musamman a nahiyar Asiya, fina-finai sun daɗe suna taka rawar gani wajen bayyana labarai na zuciya, al’adu, ƙauna da gwagwarmaya. A sinimar Indiya da ta Tamil, fina-finai biyu sun fi fice wajen tabbatar da irin wannan tasiri, wato 'Dilwale Dulhania Le Jayenge' da 'Kaakha Kaakha'. Waɗannan fina-finai sun sauya fuskar sinima, sun gina wani sabon fahimta game da ƙauna da rayuwa, kuma har yau suna zaune a zukatan masu kallo, shekaru da dama bayan fitarsu. Dilwale…
Read More
Yadda Hamisu Breaker da G-Fresh suka shiga komar EFCC 

Yadda Hamisu Breaker da G-Fresh suka shiga komar EFCC 

Daga AISHA ASAS  Shahararren mawaƙin nan na Kannywood, Hamisu Breaker, tare da jarumin TikTok, Abubakar Ibrahim, wanda aka fi sani da Al-Amin G. Fresh, sun shiga hannun hukuma bayan da Kotun Tarayya a Kano ta same su da laifi kan cin zarafin takardun Naira. Kotun ta yanke musu hukuncin ɗaurin wata biyar a gidan kurkuku ko kuma zaɓin biyan tara ta Naira 200,000 ga kowannensu. Hukumar Yaƙi da Rashawa da Zagon ƙasa ga Tattalin Arzikin ƙasa (EFCC) ce ta gurfanar da su a gaban Mai Shari’a Sale Musa Shuaibu, inda kowannensu ya amsa laifin watsar da takardun kuɗin Naira a…
Read More
Kotun ƙasar Sin ta rataye jarumi Zhang Yiyang kan kisan budurwarsa

Kotun ƙasar Sin ta rataye jarumi Zhang Yiyang kan kisan budurwarsa

Daga AISHA ASAS  Wani hukunci mai ɗaukar hankali ya sauka a masana’antar nishadin ƙasar Sin, bayan da aka tabbatar da kisan gilla da Zhang Yiyang, fitaccen jarumi kuma mawaƙi, ya yi wa ƙaramar budurwarsa. Hukumar shari’a ta ƙasar ta tabbatar da zartas da hukuncin kisa a kansa. Zhang, mai shekaru 32, ya halaka budurwarsa mai shekaru 16 a cikin 2022 bayan wata gardama da ta shiga tsakaninsu. Hukumar shari’a ta bayyana cewa, ya sare jijiyoyin wuyanta da wuka, wanda ya janyo zubar jini sosai har ta rasa ranta. Binciken ‘yan sanda ya nuna cewa, suna tare tun 2021, amma matar…
Read More
‘Yan fim za su ci gaba da cin moriyar Gwamna Abba Kabir Yusuf – Jaruma Aina’u Ade

‘Yan fim za su ci gaba da cin moriyar Gwamna Abba Kabir Yusuf – Jaruma Aina’u Ade

Daga MUKHTAR YAKUBU A kwanakin baya ne mai bai wa Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf shawara Hajiya Aina'u Ade ta gudanar da taron bayar da tallafi ga mabuƙata musamman dattawan cikin Kannywood, in da a wajen taron aka ga ta bayar da wani ƙunshin kuɗi ga mahalarta taron, baya ga haka kuma aka bi waɗansu har gida wato marassa lafiya aka kai musu, wasu kuma suka je ofishinta suka karbi nasu. Ganin yadda rabon kuɗin ya kasance ne wakilinmu ya ji ta bakin Aina'u Ade dangane da wannan rabon kuɗin da ta yi. Don haka sai ku biyo mu…
Read More