27
Jul
Daga IBRAHIM HAMISU a Kano A abinda ya bayyana na rikici da san'insa da ke wakana tsakanin Naziru M. Ahmad da aka fi sani da Naziru Sarkin Waƙa da Adamu Dauda Kahutu Rarara, abin ya yi ƙamari ne a shekarar 2023 inda a wata hira da tashar DCL ta yi da Naziru Sarkin Waƙa ya bayyana cewa, an bashi miliyan 150 da motar mliyan 80 don ya bar tafiyar Atiku Abubakar, inda Rarara ya fito ya ƙaryata Naziru a kan wannan furuci inda ya nuna cewa wannan ba abu ne mai yiwuwa ba sam. Wanda daga bisani Naziru ya fusata…
