Nishadi

Mawaƙi Ado Gwanja zai angonce yau Juma’a

Mawaƙi Ado Gwanja zai angonce yau Juma’a

Daga AISHA ASAS An kwana biyu ana raɗe-raɗen shahararren mawaƙin mata, Ado Gwanja, zai yi sabon aure bayan rabuwarsa da matarsa ta farko wadda suke da ‘ya ɗaya tilo da ita, sai dai babu wata hujja da ke nuna gaskiyar zancen, wanda hakan ke sa lokacin ya zo ya wuce ba tare da an ji labarin ɗaura auren ba. Sai dai a wannan karon labarin ya bambanta, domin ya samu isnadi mai ƙarfi da za a iya cewa ƙamshin gaskiyarsa ya rinjaye warin ƙaryarsa, domin labarin ya fito ne daga bakin yayan mawaƙin Alhaji Sa’idu Gwanjo, wanda ya sanar da…
Read More
Fitattun mawaƙan Nijeriya da suka taɓa zaman gidan kaso

Fitattun mawaƙan Nijeriya da suka taɓa zaman gidan kaso

(Ci gaba daga makon jiya) Daga AISHA ASAS A satin da ya gabata, mun kawo wasu daga cikin mawaƙan da suka ɗanɗani zaman gidan yari da kuma dalilan da ya kai su. Sannan mun yi ma ku alƙawarin ci gaba da wannan darasi, don samun kawo ƙarin wasu kafin mu rufe darasin. Shahararrun mawaƙa da suka yi rayuwar gidan kaso na ɗan da dama, don haka ba za mu iya kawo wa masu karatu dukka ba, saboda haka za mu tsakuro ne daga ciki. A sha karatu lafiya. Burna Boy: Mawaƙi Burna Boy ba ya buƙatar gabatarwa a wannan zamani…
Read More
Fitattun mawaƙan Nijeriya da suka taɓa zaman gidan kaso

Fitattun mawaƙan Nijeriya da suka taɓa zaman gidan kaso

Daga AISHA ASAS Sau da dama shahara kan ruɗi wasu daga cikin masu tare da ita, har su fara tunanin za su aikata kowanne irin laifi su sha. Sukan ruɗu da cewa, ƙasarsu cike ta ke da masoyansu wanda za su iya samun alfarma ta kowanne ɓangare. Da wannan ne suke ganin taka doka bai zama wani babban lamari a wurin su ba. Wasu kuwa ba wannan tunanin ne ke aika su ƙa saɓa wa doka ba, giyar ɗaukaka ce da suka ɗirka ta bugar da su, ta hana su tunanin makomarsu yayin da suka hasala hukuma. Don haka sai…
Read More
Shahara da karɓuwa ce babbar nasarar kowanne jarumi – Baba Ɗan Audu

Shahara da karɓuwa ce babbar nasarar kowanne jarumi – Baba Ɗan Audu

Daga AISHA ASAS A kowacce irin sana’a da mutum zai yi, yakan yi fatan samun nasara da kuma ɗaukaka, kamar yadda masu azancin magana ke cewa, “ka nemi sa’a ba iyawa ba, domin sa’a ta fi iyawa.” Da wannan ne ake samun wasu su fi wasu a harkokin da suka sa a gaba. Da yawa sun fahimci nasara daga Allah ce, duk ƙoƙarinka za ka iya tarar da wanda bai fi ka ba ya zama sama da kai, wannan ne ke taimako wurin yaƙar shaiɗan wurin hana shi sanya ma ka hassadar waɗanda suka fi ka. Hakazalika, akan samu wasu…
Read More
Yadda mutuwar mawaƙi Mahmud Nadanko ta girgiza al’umma

Yadda mutuwar mawaƙi Mahmud Nadanko ta girgiza al’umma

Daga AISHA ASAS A safiyar Lahadin da ta gaba ta ne, aka tashi da mummun labarin rashin ɗaya daga cikin 'ya'yan masana'atar finafinai ta Kannywood, jarumin barkwanci kuma mawaƙi, Mahmud Nadanko, wanda ya haɗu da ajalinsa a kan hanyarsa ta zuwa Jihar Kano tare da ƙaninshi da kuma mai ɗakinsa da ke tare da jaririn ɗansu. Wani abin tausayi da jan hankali ga mai rabo, wanda zai ƙara wa mai rabon shirya imani ya ƙara tabbatar da ba mai kashewa ko rayawa ba ya ga Allah shi ne, mai ɗakin tasa da ke tare da jinjirin ɗan mawaƙin, majiya mai…
Read More
Yadda MOPPAN ta bunƙasa ƙarƙashin Dr Sarari

Yadda MOPPAN ta bunƙasa ƙarƙashin Dr Sarari

Daga AISHA ASAS A ranar Asabar 10 ga Yunin 2023 ne ƙungiyar MOPPAN ta ƙasa ta gudanar da taronta na ƙarshen shekara, inda ta gayyaci dukkanin shugabanni a matakin ƙasa da jihohi. Taron, wanda ya gudana a babban zauren taro na Kannywoo TV da ke Tudun Yola a cikin birnin Kano, ya kafa babban tarihi a masana’antar shirya finafinan Hausa. Babban abin da ya fi ba wa mahalarta taron sha’wa, ciki, har da wakilan kwamitin Amintattu da na kwamitin ayyuka na musamman da tsare-tsare, shi ne yadda Shugaban qungiyar Dr. Ahmad Muhammad Sarari ya ɗauki lokaci wajen bayyana ayyukan ci…
Read More
Yadda MOPPAN ta bunƙasa ƙarƙashin Dr Sarari

Yadda MOPPAN ta bunƙasa ƙarƙashin Dr Sarari

A ranar Asabar 10 ga Yunin 2023 ne ƙungiyar MOPPAN ta ƙasa ta gudanar da taronta na ƙarshen shekara, inda ta gayyaci dukkanin shugabanni a matakin ƙasa da jihohi. Taron, wanda ya gudana a babban zauren taro na Kannywoo TV da ke Tudun Yola a cikin birnin Kano, ya kafa babban tarihi a masana'antar shirya finafinan Hausa. Babban abin da ya fi ba wa mahalarta taron sha'wa, ciki, har da wakilan kwamitin Amintattu da na kwamitin ayyuka na musamman da tsare-tsare, shi ne yadda Shugaban Ƙungiyar Dr. Ahmad Muhammad Sarari ya ɗauki lokaci wajen bayyana ayyukan ci gaba da mulkinsa…
Read More
Yadda jaruma Rashida Maisa’a ta jagoranci kai wa Aisha Buhari ziyarar karramawa a Daura

Yadda jaruma Rashida Maisa’a ta jagoranci kai wa Aisha Buhari ziyarar karramawa a Daura

Daga AISHA ASAS Larabawa na wani karin magana, “lli kulli bidayyatin nihaya” Bahaushe kuwa na cewa, komai ya yi farko zai yi ƙarshe. A daidai lokacin da wa’adin mulkin shugaba Muhammadu Buhari ya kawo ƙarshe, wasu da dama daga cikin alkhairan da makusantanshi ke yi suka tsaya tare da shi, don haka ɗinbin mutane suka shiga alhenin rashin majingin da suke jingina da shi a tsakanin ahalinsa ko makusantansa. A ranar 29 ga watan Mayu ne Nijeriya ta yi sabon ango, wanda hakan na nufin karɓar ragamar mulkin ƙasa daga hannun Muhammadu Buhari zuwa ga sabon Shugaban Ƙasa Bola Ahmad…
Read More
Lagbaja: Mawaƙin da ba a taɓa ganin fuskarsa ba

Lagbaja: Mawaƙin da ba a taɓa ganin fuskarsa ba

Daga AISHA ASAS Bisade Ologunde, wanda duniya ta fi sani da suna Lagbaja, mawaƙin Nijeriya ne da Allah Ya wadata da baiwar waƙa. Mawaƙi ne da ke da hikimar rera waƙa da mabambantan kiɗa, domin ya ƙware ƙwarai wurin sarrafa waƙz'a mai amfani da kifan zamani da kuma na al’adarsu, wato Yarbanci. Kamar yadda muka sani, kaso mai rinjaye na masu harkar nishaɗantarwa, kama daga waqa, kixa zuwa wasan kwaikwayo ko wasannin barkwanci zuwa na wasan motsa jiki, za ka tarar da a layin farko ko na biyu na burukansu akwai shahara, duniya ta san da su, duk inda suka…
Read More
Mawaƙiya Tina Turner ta kwanta dama

Mawaƙiya Tina Turner ta kwanta dama

Daga AISHA ASAS Fitacciya kuma shahararriyar mawaƙiyar Tina Turner, wadda ta kafa tarihi a duniyar waƙa ta mutu tana da shekara 83. Mawaƙiyar, wadda aka haifa a Tennessee da ke Amurka, ta rera waƙoƙi da dama kamar, 'Mountain High', 'What's Love Got to Do With It', 'River Deep' da dai sauransu. Za mu iya cewa, matsalolin rayuwar aure da mawaƙiyar ta fuskata ne suka zama sanadin ɗaukakar ta, domin kamar yadda aka tabbatar kusan duk waƙoƙin da ta ke rerawa na ɗauke da kukan zuci na daga rashin jin daɗin zamantakewarta da tsohon mijinta mai suna IkeTurner. Turner daɗaɗɗiyar mawaƙiya…
Read More