Nishadi

Lagbaja: Mawaƙin da ba a taɓa ganin fuskarsa ba

Lagbaja: Mawaƙin da ba a taɓa ganin fuskarsa ba

Daga AISHA ASAS Bisade Ologunde, wanda duniya ta fi sani da suna Lagbaja, mawaƙin Nijeriya ne da Allah Ya wadata da baiwar waƙa. Mawaƙi ne da ke da hikimar rera waƙa da mabambantan kiɗa, domin ya ƙware ƙwarai wurin sarrafa waƙz'a mai amfani da kifan zamani da kuma na al’adarsu, wato Yarbanci. Kamar yadda muka sani, kaso mai rinjaye na masu harkar nishaɗantarwa, kama daga waqa, kixa zuwa wasan kwaikwayo ko wasannin barkwanci zuwa na wasan motsa jiki, za ka tarar da a layin farko ko na biyu na burukansu akwai shahara, duniya ta san da su, duk inda suka…
Read More
Mawaƙiya Tina Turner ta kwanta dama

Mawaƙiya Tina Turner ta kwanta dama

Daga AISHA ASAS Fitacciya kuma shahararriyar mawaƙiyar Tina Turner, wadda ta kafa tarihi a duniyar waƙa ta mutu tana da shekara 83. Mawaƙiyar, wadda aka haifa a Tennessee da ke Amurka, ta rera waƙoƙi da dama kamar, 'Mountain High', 'What's Love Got to Do With It', 'River Deep' da dai sauransu. Za mu iya cewa, matsalolin rayuwar aure da mawaƙiyar ta fuskata ne suka zama sanadin ɗaukakar ta, domin kamar yadda aka tabbatar kusan duk waƙoƙin da ta ke rerawa na ɗauke da kukan zuci na daga rashin jin daɗin zamantakewarta da tsohon mijinta mai suna IkeTurner. Turner daɗaɗɗiyar mawaƙiya…
Read More
MOPPAN ta taya Abba Kabir murnar zama Gwamnan Kano

MOPPAN ta taya Abba Kabir murnar zama Gwamnan Kano

Daga BASHIR ISAH Ƙungiya Masu Shirya Fina-finai ta Nijeriya, MOPPAN, ta miƙa saƙon taya murna ga sabon Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf. Cikin sanarwar manema labarai da ƙungiyar ta fitar mai ɗauke da sa-hannun Babban Sakatare na Ƙasa, Salisu Muazu, MOPPAN ta ce a madadin mambobinta tana taya murna ga Injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayinsa na sabon Gwamnan Jihar Kano. A cewar ƙungiyar, nasarar Gwamna Abba nasara ce ga kowa a jihar Kano ba tare da la'akari da bambancin siyasa ko makamancin haka ba. MOPPAN ta nusar da Gwamnan kan cewa, alƙawarin sake gina Jihar Kano da ya…
Read More
Masari ya ba wa Rarara da Baban Chinedu tallafin N80m

Masari ya ba wa Rarara da Baban Chinedu tallafin N80m

Daga Umar Garba a Katsina Gwamnatin jihar Katsina, qarqashin jagorancin Aminu Bello Masari ta bawa fitaccen mawaqin siyasa, Adamu Abdullahi Rarara tallafin kuxi naira miliyan 50. A yayin da aka bawa xan wasan barkwanci Kuma Mawaqin Hausa, wato Baban Chinedu Naira miliyan 30. Bayanin hakan dai na qunshe ne a cikin wata takarda mai xauke da sa hannun Saminu Muhammad K. Soli, kwamishinan kasafin kuxi da tsare-tsare na jihar. Ma’aikatar kasafin kuxin ta ce an amince da sakin Naira miliyan 80 ga mutanen biyu a matsayin taimako kan lalata gidajensu a jahar Kano.
Read More
Ban shigo Kannywood don neman kuɗi ba – Sadiya Sokoto

Ban shigo Kannywood don neman kuɗi ba – Sadiya Sokoto

Daga IBRAHIM HAMISU Sadiyya Muazu wacce aka fi sani da Sadiya Sokoto, jaruma ce da ta ke tashe a masana'antar fim ta Kannywood, musamman a fim ɗin 'Rumfar mai Shayi'. A tattaunawarta da wakilin Manhaja a Kano, za ku ji tarihinta da kuma faɗi-tashin da ta yi har zuwa wannan lokacin. Ku biyo mu: MANHAJA: Da wa muke tare? SADIYA SOKOTO: Sunana Sadiya Muazu, wadda aka fi sani da Sadiya Sokoto. Ko za ki ba mu taqaitaccen tarihinki? Ni 'yar asalin Sakkwato ce, amma yanzu Ina zaune a Kano, na yi Primary da Secondary dukka a Sokoto, sannan na yi…
Read More
Rikicin Sudan: An kashe fitacciyar mawaƙiya Shaden Gardood

Rikicin Sudan: An kashe fitacciyar mawaƙiya Shaden Gardood

Daga AISHA ASAS An kashe ɗaya daga cikin fitattun mawaƙan Sudan Shaden Gardood, a wata musayar wuta tsakanin ɓangarori biyun da ke faɗa da juna a ƙasar. Misis Gardood ta rasa ranta ranar Juma'a a birnin Omdurman sakamakon faɗa tsakanin sojojin qasar da dakarun RSF. Mutuwar mawaƙiyar mai shekara 37 na zuwa ne kwana guda bayan ɓangarorin da ke rikici da juna sun rattaba hannu kan yarjejeniyar kawo ƙarshen wahalar da fararen hula ke fuskanta. Gardood dai na zaune ne a al-Hashmab, inda dakarun RSF ke ƙaruwa a 'yan kwanakin nan. Wani bidiyo da ya yaɗu a shafukan sada zumunta…
Read More
Daraja da girmamawar da ake bai wa mawaƙa ba ta kai yadda ake buƙata ba – Tijjani Gandu

Daraja da girmamawar da ake bai wa mawaƙa ba ta kai yadda ake buƙata ba – Tijjani Gandu

(Ci gaba daga makon jiya) Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A satin da ya gabata, mun faro firarmu da neman sanin ko waye mawaƙi Tijjani Gandu, kafin mu garzaya kan dalilin tattaunawar tamu, wato waƙoƙi, inda ya yi mana bayyanin yadda ya faro da kuma yadda ya sauya akalan waƙoƙinsa daga na soyayya da kuma yabon fiyayyen halitta zuwa na siyasa, da ma wanda ya zama silar faruwar hakan. Kamar yadda muka yi alƙawarin kawo maku ci gaban wannan tattaunawa, Allah Ya kawo mu, lokaci ya yi, don haka a sha karatu lafiya. MANHAJA: Shin kana ganin ýan siyasa na rama…
Read More
Jarumin Nollywood, Saint Obi ya riga mu gidan gaskiya

Jarumin Nollywood, Saint Obi ya riga mu gidan gaskiya

Fitaccen jarumi a masana’antar shirya fina-finai ta Nollywood, Saint Obi, ya bar duniya yana da shekara 57. Jarumin ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya. Bayanai sun ce jarumin ya cika ne a ranar Lahadin da ta gabata, 7 ga Mayu, a gidan wata 'yar uwarsa. A cewar rahotanni, rashin jituwa a tsakanin ‘yan uwansa ya haifar da tsaiko wajen sanar da rasuwar marigayin a hukumance. Majiya ta ce bayan rasuwar marigayin a ranar Lahadin, an ɗauke gawarsa zuwa ɗakin adana gawarwaki na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH). Jaridar Intel Region ta rawaito cewar, a baya-bayan nan Saint…
Read More
Soyayyata ga Kwankwaso ta sa ni sauya akalar waƙoƙina zuwa na siyasa – Tijjani Gandu

Soyayyata ga Kwankwaso ta sa ni sauya akalar waƙoƙina zuwa na siyasa – Tijjani Gandu

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Ga duk mai bibiyar harkokin siyasa a Nijeriya, musamman abin da ya shafi ɓangaren waƙoƙi, ba zai rasa jin labarin Tijjani Gandu ko waƙoƙinsa, musamman waɗanda yake yi wa jagoran Kwankwasiyya Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso, ko kuma Bakandamiyarsa ta Abba Gida Gida, da ya yi wa zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf. Ahmad Tijjani Hussaini Gandu kamar yadda cikakken sunansa yake, fitaccen mawaƙin siyasa ne, da ake jin amonsa a duniya ba a Jihar Kano kaɗai ba, saboda salon waƙoƙinsa da yadda yake kwarzanta jagoransa kuma madugun Kwankwasiyya, wanda ya ce yana alfahari da…
Read More
Jarumi Uzee ya zama jakadan Bankin Musulunci na TajBank

Jarumi Uzee ya zama jakadan Bankin Musulunci na TajBank

Daga AMINA YUSUF ALI Fitaccen jarumin nan na Kannywood da Nollywood, Usman Uzee, ya zama jakadan bankin nan na Musulunci, wato TajBank. A ranar Alhamis, 4 ga Mayu, 2023, jarumin ya rattaba hannu kan yarjejeniyar da bankin tare da manyan jami’an bankin. Idan dai za a iya tunawa, bankin na TajBank yana daga cikin kalilan din bankuna a Nijeriya da ba su mu’amula da kudin ruwa. Shi kuwa Jarumi Uzee yana daga kalilan din jarumin Nijeriya da suke fitowa a finafinan Arewa da na Kudu. Daya daga cikin fitattun finafinan da ya fito shine, Voiceless, wanda ya samu hawa manhajar…
Read More