Nishadi

Mutane sun yi wa jaruma Tonto Dikeh ca kan shawarar da ta ba wa matan aure

Mutane sun yi wa jaruma Tonto Dikeh ca kan shawarar da ta ba wa matan aure

Daga AISHA ASAS A 'yan kwanakin nan ne labarin cin amanar da aka yi wa jaruma a masana'antar Nollywood, Mimi Linda Yina, wadda aka fi sani da Medlin Boss, ya ja hankalin mutane, ba ma kamar samun masaniyar cewa, ba wai kawai mijinta ya ci amanar ta da mace ne kawai ba, ya ci amanar ta da babbar ƙawarta. Da wannan mutane suka dinga zaro maganganu daga zuciya suna ajiye wa a duk inda maganar zata yi tasiri, musamman ma mata. Da yawa suna tofin Allah tsine ga wannan cin amanar da ƙawa da mijin jarumar suka aikata, a wani…
Read More
Ka adana kuɗinka, shawarar Ɗangote ga mawaƙi Davido

Ka adana kuɗinka, shawarar Ɗangote ga mawaƙi Davido

Ɗangote na siyan mota biyu kacal a shekara takwas - Davido Daga AISHA ASAS Shahararren mawaƙi David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, a cikin wata tattaunawar da ya yi da Forbes, ya bayyana kyakyawar alaƙa da ke tsakanin sa da babban ɗan kasuwa, Aliko Ɗangote. A cikin tattaunawar, Davido ya yi muhimman batutuwa da suka haɗa da irin shawarar da Ɗangote ya fi yawan ba shi a duk lokacin da suka haɗu. Shawarar da za mu iya cewa, da yawa mutane sun yi mamakin fitowarta daga babban mai kuɗi irin Ɗangote. Da yawa idan ka tarar da wani…
Read More
Yadda ɗan ƙwallo, Achraf ya sha matarsa tauraruwar fim, Hiba da basilla

Yadda ɗan ƙwallo, Achraf ya sha matarsa tauraruwar fim, Hiba da basilla

Daga AISHA ASAS  A 'yan kwanakin nan ne dai kafafen sada zumunta suka yi sabon ango, wanda ya kasance abin sha'awar kowacce uwa, mafi wayo a wurin kowanne magidanci, kuma abin haushin mafi yawa daga cikin mata. Achraf Hakimi, ɗan wasan tamaula da ya kafa tarihin da ba a taɓa samun sa ba a tsakanin mutane masu suna da shuhura. Kamar yadda yake sananne a tsakanin ƙasashe da dama idan ka cire Nijeriya, saki wani abu ne mai matuƙar wahalar yi, tare da hasara musamman ma ga miji, domin doka ce, mace na da dama kan wani kaso na dukiyar…
Read More
Wanene Jarumi Justus Esiri?

Wanene Jarumi Justus Esiri?

Daga AISHA ASAS Justus Esiri na ɗaya daga cikin tushe da asalin masana'antar finafinai ta Nollywood, kasancewar sa ɗaya daga cikin waɗanda suka fara yin fim tun kafin ta amshi sunanta na Nollywood a shekarar 1960, inda ya soma da wasan kwaikwayo ta gidan talabijin na NTA, wato Nigerian Television Authority, inda ya fara da wani shiri mai dogon zango da aka yi wa suna da 'The Village Headmaster', wanda kusan za a iya cewa ya zama silar shuhurar sa. Justus Esiri ɗan asalin Jihar Delta ne a Oria-Abraka. An haife shi a ranar 20 ga watan Nuwamban shekarar 1942.…
Read More
Kotu ta sake aike wa Rarara sammaci

Kotu ta sake aike wa Rarara sammaci

Daga AISHA ASAS Wata Babbar Kotun Shari’ar Musulunci a Kano ta bada umarnin sake rubuta wa mawaƙi Dauda Adamu Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara wata takardar sammaci sakamakon ƙin halartar zamanta da ya yi. Kamar yadda jaridar Aminiya ta rawaito, Kotun wacce ke zamanta a unguwar Rijiyar Zaki da ke birnin Kano, ƙarƙashin Mai Shari’a Halhalatul Khuza’i Zakariyya, ta bayar da umarnin yayin zamanta na ranar Talata. Kamar yadda aka faɗa, ana ƙarar mawaƙin ne kan taurin bashin wasu wayoyin da yake karva, yana rabawa mutane daga wurin wani ɗan kasuwa da ake cewa, Muhammad Ma’aji. Kuɗin wanda…
Read More
Ina raye ban mutu ba, inji Jarumi Al-Amin Ciroma, Baban Lukman

Ina raye ban mutu ba, inji Jarumi Al-Amin Ciroma, Baban Lukman

Daga BASHIR ISAH Da SANI AHMAD GIWA a Abuja Fitaccen ɗan jaridar nan kuma jarumin Kannywood, har wa yau Kakakin Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), Al-Amin Ciroma, wanda mutane suka fi sani da Baban Lukman na cikin shirin fim ɗin nan mai dogon zango, 'Labarina', ya bayyana cewa, yana nan da ransa, bai mutu ba saɓanin wata sanarwar mutuwarsa da aka yaɗa. Ciroma ya bayyana haka ne cikin wani faifan bidiyo mai tsawon daƙiƙa 46 da ya yi aka kuma yaɗa a soshiyal midiya da yammacin ranar Alhamis bayan da labarin ‘mutuwarsa’ ya karaɗe kafafen sada zumunta,…
Read More
Rubuta fim ɗin da zai amfanar da al’umma ne babban burina – Yusra Yusuf

Rubuta fim ɗin da zai amfanar da al’umma ne babban burina – Yusra Yusuf

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano Yusra Yusuf Yunusa wadda aka fi sani da Yusra AGM matashiyar da ta yi fice a wajen rubuta labarin fim a masana'atar Kannywood. A tattaunawarta da wakilin Manhaja a Kano, Ibrahim Hamisu, za ku ji tarihinta da kuma irin faɗi-tashin da ta yi har ta kai ana karbar rubutunta a Kannywood. A sha karatu lafiya: MANHAJA: Muna son ki gabatar mana da kanki ga masu karatunmu? YUSRAH YUSUF: Sunana Yusrah Yusuf Yunusa, wacce aka fi sani da Yusra AGM Bashir kamar yadda ake kira na. Ko za ki ba mu taƙaitaccen tarihinka? Nayi karatu a Mai…
Read More
Jaruma Mercy Aigbe ta musulunta

Jaruma Mercy Aigbe ta musulunta

Daga WAKILINMU Fitacciyar jaruma a masana'antar fina-finai ta Nollywood, Mercy Aigbe, ta bayyana sunanta na Musulunci biyo bayan musuluntar da ta yi. Ta bayyana sunan ne a wajen taron lacca na Ramadan da addu'a ta musamman da suka shirya ita da mijinta, Kazeem Adeoti. Hakan na ƙunshe ne cikin wani faifan bidiyon tattaunawar da aka yi da ita wanda aka yaɗa a kafar sada zumunta na zamani. An jiyo ta tana cewa, “Insha Allah, sabon sunana shi ne Hajiya Meenah Mercy Adeoti. Meenah mai ɗauke da harafin H."
Read More
Da yawan mawaƙan Arewa ba su san ta yadda za su amfana da basirarsu ba – Haidar Blog

Da yawan mawaƙan Arewa ba su san ta yadda za su amfana da basirarsu ba – Haidar Blog

Daga ADAMU YUSUF INDABO a Kano Fasihin mawaqin Hausa, kuma ɗan kasuwar dake dillancin waƙoƙin Hausa a yanar gizo, mai suna Aliyu Abubakar, da ake wa laƙabi da Haidar Blog, ya bayyana wannan kyakkyawan fata da buri da yake da shi ne a kan mawaqa da dukkan waɗanda Allah Ya yi wa baiwar basirar na suna amfanuwa da basirar tasu don ƙara samun ƙwarin gwiwa gare su. Tare kuma da yin kira ga matasa da su ƙara ƙaimi wajen neman ilimi, wanda da shi ne rayuwar bawa take yin haske kuma komai ke zuwar masa a sauqaqe, a wata tattaunawa…
Read More
Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga Jarumi Adam A. Zango

Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga Jarumi Adam A. Zango

Daga LARABI LARABEEN Zuwa ga jarumi Adam A. Zango, Ina fata wasiƙata ta same ka cikin ƙoshin lafiya. Game da maganar da ka yi cewa, ba za ka ƙara aure ba har abada, haba don Allah! Bai kamata ka ce haka ba. Da ma tin filazal fitattun mutane kan sha fama da matsaloli kala-kala. Amma kai naka kuskuren ya samo asali a kan yadda kake zaɓen macen aure mai kyawu fuska fiye da kyawun ɗabi'a da tarbiyya. Wata matsalar taka kuma ita ce, ka daina auren macen da take son Adam A. Zango na Film. Ka nemi macen da take…
Read More