23
Mar
Daga AISHA ASAS A makon da ya gabata ne Jarumar TikTok Murja Ibrahim Kunya ta shiga komar Hukumar Yaƙi da Masu yi wa Tattalin Arziƙin ƙasa Zagon ƙasa, wato EFCC ta shiyar Jihar Kano, inda suka kama jarumar da laifin wulaƙantawa da lalata takardun Naira. Hukumar ta yi ram da jaruma Murja Ibrahim Kunya ne kan laifin fesa takardun Naira da ta yi don jin daɗi a lokacin da take zaune a ɗakin otal da ke cikin Tahir Guest Place a Kano. Za a iya kiran kamen da 'faɗuwa ta zo daidai da zama', domin ya faru ne a daidai…
