Nishadi

Ba Ned ne uban cikin da nake ɗauke da shi ba – Jaruma Chika Ike

Ba Ned ne uban cikin da nake ɗauke da shi ba – Jaruma Chika Ike

Daga AISHA ASAS A 'yan kwanakin nan ne kafafen sada zumunta suka yi amo da labarin ciki da fitacciyar jaruma a masana'antar Nollywood Chika Ike ke ɗauke da shi, wanda aka shiga muhawar wanda ya zama silar samun cikin nata. kasancewar jarumar ba ta ce kamai ba, ya sa 'yan gulmamaki ke yawo daga nan zuwa can, saidai ba wadda ta yi ƙarfi kamar ta alaƙanta cikin da fitacce kuma shahararren mai kuɗin nan kuma mijin jaruma a masana'anatar Regina Deniels, wato Ned Nwoko, wanda ya yi fice a yawan auren mata. Lamarin wanda ya haifar da maganganu masu ƙarfi…
Read More
Lenscope Media sun rattaba hannu kan kwangilar da Gwamnatin Tarayya ta ba su ta gina gidan shirya finafinai na Jos 

Lenscope Media sun rattaba hannu kan kwangilar da Gwamnatin Tarayya ta ba su ta gina gidan shirya finafinai na Jos 

Daga AISHA ASAS A ƙoƙarin kawo gagarumin cigaba a masana'antar finafinai ta Nijeriya, Gwamnatin Tarayya a ƙarƙashin jagorancin Hukumar Kula da Gidajen Tarihi, wato NCMM, ta ba wa kamfanin Lenscope Media aikin gina gidan shirya finafinai na Jos, wato Film ɓillage, tare da haɓaka wasu wuraren tarihi da ke Zariya, Kano da kuma Katsina. Aikin wanda aka sa hannu kan sa a ranar 7 ga watan Fabrairi, na wannan shekara zai mayar da hankali ne kan mayar da wasu wuraren wasan kwaikwayo wurin horas da 'yan wasa da sauransu. sannan za a yi ginin ne a wani ɓangare na gidan…
Read More
67th Grammys: Yadda mawaƙan Nijeriya suka ci baya, kuma suka ci gaba a dare ɗaya

67th Grammys: Yadda mawaƙan Nijeriya suka ci baya, kuma suka ci gaba a dare ɗaya

Daga AISHA ASAS  Sanannen abu ne cewa, a 'yan shekarun nan, mawaƙan Nijeriya ne suka amshe kaso mafi rinjaye na waƙoƙin da aka fi ji da tashe a duniya. wannan ne ya sa duniya ba ta da zaɓi face ayyana su a matsayin manyan mawaƙan duniya, wanda hakan ya kawo tazgaro ga manyan mawaƙan Turawa da wasu ƙasashen waɗanda a baya suke a layin farko da ake ji da ganinsu a kodayaushe. Mawaƙa irin su Rema, Daɓido, Burna Boy da makamantansu sun kasance masu jan zare a waƙoƙin duniya na ɗan tsayin lokaci, wanda hakan ya sanya suke wasan ƙwallon…
Read More
Baɗala: Masarauta ta tuge sarautar Sojaboy bayan dakatarwar hukamar tace finafinai

Baɗala: Masarauta ta tuge sarautar Sojaboy bayan dakatarwar hukamar tace finafinai

Daga AISHA ASAS Masarautar Gidan Igwai ta Jihar Sakkwato, ta sanar da tuɗe mawaƙi Usman Umar, wanda aka fi sani da Sojaboy daga muƙamin da aka naɗa shi na Yariman Gidan Igwal. Dalilin yanke wannan hukunci kuwa bai kaucewa irin wanda ya kai hukumar tace finafai dakatar da mawaƙin ba, wato yaɗa baɗala. Idan mai karatu na bibiye da lamarin, a satin da ya gabata ne Humumar tace finafinal ƙarƙashin jagorancin Abba El-Mustapha ta dakatar da mawaƙi Sojaboy daga duk wasu harkoki da suka shafi Kannywood a Jihar Kano, sakamakon yaɗuwar wani faifan bidiyon waƙarsa da ya sanyawa suna 'Bugun…
Read More
Nijeriya za ta kafa hukumar basirar ƙirƙira da yawon buɗe ido – Musawa

Nijeriya za ta kafa hukumar basirar ƙirƙira da yawon buɗe ido – Musawa

Daga AISHA ASAS  Gwamnatin Tarayya ta amince da kafa hukumar kula da basirar ƙirƙira da yawon buɗe-ido, wanda wani muhimmin shiri ne da aka tsara, domin haɓaka ƙarfin tattalin arzikin masana’antun ƙere-ƙere da yawon buɗe ido na Nijeriya ta hanyar haɗin gwiwa da hukumomi masu zaman kansu (PPP). Ministar ƙirƙira, al’adu, yawon buɗe ido, da kuma tattalin arziki ta fuskar fasaha, Hannatu Musawa, ce ta bayyana hakan a ranar Litinin bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya, wanda shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a fadar shugaban ƙasa, Abuja. Ta bayyana hakan a matsayin wani babban yunƙuri na sauya fasalin al'ummar…
Read More
Akasarin waɗanda suka fara fim ɗin Hausa a Kaduna ‘yan Kabala Costain ne – Mawaƙi Baban Khausar 

Akasarin waɗanda suka fara fim ɗin Hausa a Kaduna ‘yan Kabala Costain ne – Mawaƙi Baban Khausar 

Daga AISHA ASAS Malam Sagir Baban Khausar shahararren mawaƙin Hausa, wanda waƙoƙinsa suka fi mayar da hankali fannin ilimantarwa, faɗakarwa da nuni cikin nishaɗi. A wannan makon Manhaja ta samu damar tattaunawa da shi, don kawo wa masu karatu wani abu da ba su sani ba game da shi. Idan kun shirya, Aisha Asas ce tare da mawaƙi Baban Khausar: MANHAJA: za mu so jin taƙaitaccen tarihinka.  BABAN KHAUSAR: Assalamu alaikum. Da farko dai sunana Sagir Mustapha Danyaro, jama'a sun fi sani na da Sagir Baban Kausar. Ni haifaffen Lungun Liman ne da ke gidan Liman a Kabala Coastain da…
Read More
Gobarar Los Angeles: Hollywood ta shiga muhawara kan bikin Oscar na bana

Gobarar Los Angeles: Hollywood ta shiga muhawara kan bikin Oscar na bana

Daga AISHA ASAS  Yayin da gobarar daji ke ci gaba da mamaya a birnin Los Angeles, a karon farko cikin shekaru goma, bikin Oscar ya shiga a babin ƙila-wa-ƙala, yayin da masana'antar Hollywood ta dasa alamar tambaya kan, ko ya kamata a gudanar da taron na bana? Idan kuma amsar e ce, to me ake nufi da yin hakan a yanzu? Girman ɓarnar da aka yi a Kudancin Kalifoniya ya yi tasirin da ya kawo tazgaro ga manyan shagulgulan bukukuwan shekara-shekara da suke da tarihi a masana'antar fim, wanda hakan ya faru cikin ƙanƙanin lokaci.  Lokacin da gobarar Palisades ta…
Read More
Jarumi Saif Ali Khan ya baro gadon asibiti

Jarumi Saif Ali Khan ya baro gadon asibiti

Daga AISHA ASAS  Likita ya ba wa jarumi a masana'antar finafinai ta Indiya, wato Bollywood, Saif Ali Khan sallama daga asibitin Lilaɓati da ke birnin Mumbai kwanaki biyar bayan an caka masa wuka, inji kamfanin dillancin labarai na PTI. Rahoton ya rawaito cewa, jaruma Kareena Kapoor, kuma mata ga jarumin ce ta ɗauko maigidan nata daga asibiti. Manhaja ta ruwaito dlilin kwamciyar jarumin asibiti a makon da ya gaba, inda a safiyar ranar Alhamis ne wani mutum ya shiga gidan Saif Ali Khan da ke Bandra inda ya caccaka masa wuka a wurare da dama, lamarin da ya sa ya…
Read More
Manyan fitattun jaruman Kannywood na 2024

Manyan fitattun jaruman Kannywood na 2024

DAGA MUKHTAR YAKUBU Shekarar ta 2024 ta zo ƙarshe kuma a yanzu an shiga sabuwar shekara ta 2025 ga mai yawan rai. Abubuwan da dama sun faru na ci gaba a cikin masana'antar finafinai ta Kannywood tun daga farkon ta zuwa ƙarshen ta waɗanda idan aka ce za a yi bayanin su ɗaya bayan ɗaya za a ɗauki tsawon lokacin ana bayani a kansu. Amma da yake an ce abin da yawa, wai mutuwa ta je kasuwa, bari mu ɗauki wani ɓangare mafi muhimmanci a cikin harkar fim musamman ga masu kallo. Wannan ɓangaren kuwa shi ne na jaruman da…
Read More
Hukumar NDLEA ta yi ram da wani jarumin fim kan safarar tabar wiwi 

Hukumar NDLEA ta yi ram da wani jarumin fim kan safarar tabar wiwi 

Daga AISHA ASAS  Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA ta kama wani mai fasahar zance, Emeka Emmanuel Mbadiwe da laifin safarar kashi 33 na Loud, wato tabar wiwi mai nauyin kilogiram 17.30. Hakan ya fito ne a wata sanarwa da Daraktan yaɗa labarai da bayar da shawarwari na hukumar Femi Babafemi ya fitar a ranar Lahadi. A cewar Babafemi, Mbadiwe, wanda kuma ɗan wasan finafinan Hollywood da na Nollywood ne da Amurka ta horar, an kama shi ne a ɗakinsa na otal ɗin Lekki ranar Juma’a 27 ga watan Disamba, 2024, biyo bayan kama abokin…
Read More