06
Dec
Daga JAMIL GULMA a Legas A duk lokacin da mutane biyu ko fiye ke neman abu ɗaya kuma ko ta halin ƙaƙa su na ganin sai haƙarsu ta cimma ruwa dangane da samun abinda su ke so, to ba shakka akwai gumurzu. Yanzu haka dai iskar guguwar siyasa ta soma kaɗawa a faɗin Nijeriya, inda masu neman wakilci da kuma shugabanci a matakai daban-daban na siyasa sai kai-komo suke yi, don ganin sun sami cimma muradinsu. Jihar Legas ma ba a bar ta a baya ba, sai dai a jihar abinda ya fi ɗaukar hankali, musamman a ɓangaren ’yan Arewa,…
