28
Feb
Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Kotun Ɗaukaka Ƙarar, wacce ta ke zamanta a Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, ta tabbatar da cewa, masu gabatar da ƙara ba su iya tabbatar wa kotu da cewa, tsohon fitaccen ɗan Majalaisar Wakilai ta Nijeriya, Hon. Faruk Lawan, ya nemi attajirin nan, Mista Femi Otedola, ya ba shi cin hancin Dala Miliyan Uku, don ya zare sunan kamfaninsa, Zenon Oil and Gas Limited, daga jerin kamfanonin da suka damfari Nijeriya kan kuɗin tallafin mai ba a cikin rahoton Kwamitin Musamman na majalisar, wanda Hon. Lawan din ya jagoranta a 2012. Wannan dalili ya…
