09
Feb
Daga MOHAMMED ALI a Gombe Zannan Askan mai Martaba Sarkin Gombe, kuma Sarkin Askan Bolari ta Gabas a Jihar Gombe, Dokta Yunusa Adamu, ya nuna matuƙar farin cikin shi akan ziyarar da Hukumar Lafiya ta Duniya, wato World Health Organization (WHO) ta kai mishi a harabar warakar shi kwanan nan, inda jami’an hukumar suka yi bincike da nazari a kan irin ayyukan shi daga bisani kuma suka gamsu da su. Malam Yunusa Adamu wanda ya yi wannan tsokacin a Gombe a makon jiya yayin wata zantawa da ya yi da manema labarai, ya furta cewa, ziyarar da jami’an na WHO…
