30
Mar
Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Ma su sana'ar kiwon kifi sun koka kan yadda kamfanonin sarrafa abincin kifi ke tsawwala farashin kayan abincin kifi, inda suka bayyana cewa hakan zai iya kawo matsanancin tsadar kifi a watan Ramadan mai zuwa. Wannan koke ya fito ne daga bakin shugabannin ƙungiyar masu sana`ar kiwon kifi a Nijeriya na ƙasa reshen Jihar Kano, wato Piratic Farmers Fish Association Of Nigeria, PFFAN a lokacin taron ƙungiyar da suka gabatar a Kano cikin makon jiya. Hudu Salisu Khalid, shi ne kakakin ƙungiyar ta PFFAN, ya ce suna fuskantar ƙalubale da matsaloli masu yawa a wannan…
