03
Feb
Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Wani shafin yanar gizo mai taken THE NIGERIAN BAHAUSHE ya yi wuf ya wallafa wani rubutu da ɗaya daga ‘yan Hausa zalla Aliyu Ammani ya rubuta tun 2019 ya na nuna fargaba cewa sunayen gargajiya na Hausawa za su bace don daukar na Larabawa. Ammani bai tsaya ba sai da ya caccaki wani abu da ya zayyana da wankewa Hausawa kwakwalwa da nau’in musulunci na daban da Jihadin Sakkwato (na Shehu Mujaddadi) ya kawo na goge duk wasu alamu da al’adu na Hausawa kafin zuwan Musulunci. Ammani dai a nan bai kawo aya ko Hadisi daga…
