17
Feb
Daga JOHN WADA a Keffi Wani matashi wanda gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya naɗa muƙamin mai taimaka masa na musamman a kwanan nan wato, Basiru Umar yace muƙamin bai da alaƙa da harkar siyasa kamar yadda wasu ke tunani. Ɗanmalikin Masakan Basiru Umar ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da 'yan jarida ciki har da wakilin mu a gidansa da ke Masaka a ƙaramar hukumar Karu kwanaki kaɗan bayan karramawar da gwamnan ya yi masa. Yace a matsayin sa na mai wannan sarautar Ɗanmalikin Masaka da ya daɗe yana tare da mai martaba sarkin Masaka…
