Rahoto

Yadda ya kamata ma’aurata su yi mu’amala ta zamantakewa a watan Ramadan

Yadda ya kamata ma’aurata su yi mu’amala ta zamantakewa a watan Ramadan

Daga SA'ADATU SAMINU KANKIA Ba wai kawai a wannan watan ake buƙatar ma'aurata su zama masu mu'amala mai kyau a tsakaninsu ba, a kullum, a kodayaushe ana buƙatar ganin cewa ma'aurata sun zama masu tafiyar da rayuwarsu ta zamantakewar aure cikin fahimta, mutuntawa da ganin girma da darajar junansu. Da yake wannan watan wata ne mai yawan darajoji da kuma albarka, yana da kyau musamman ga ma'auratan da ba su da ɗabi'ar daraja junansu da su yi amfani da wannan rubutu domin gyara zamantakewar zamansu na aure da niyar ci gaba da kyawawan ɗabi'un daga wannan lokaci har ya zuwa…
Read More
Muhimman hanyoyi 10 na kula da fata (4)

Muhimman hanyoyi 10 na kula da fata (4)

Daga AISHA ASAS Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Kwalliya na wannan makon. Sannunku da jimirin bibiyarmu.  A wannan satin da yardar mai kowa mai komai za mu kai ƙarshen wannan darasin da ya ɗauke mu tsawon sati huɗu. 8. Goge matattun ƙwayoyin fata cikin hikima: Akwai hanyar da ake bi wurin goge fata ta amfani da wasu amintattun kayan goge matattar fata cikin sauƙi. Saidai yana da kyau matuƙa lura da irin kayan da ya kamata a yi amfani da su. Za a goge a hankali sau ɗaya zuwa uku a mako (ya danganta da irin ƙarfin…
Read More
Zuwa ga masu tuƙin ganganci

Zuwa ga masu tuƙin ganganci

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Wannan wasiƙa an rubuta ta ne da zuciya ɗaya, da damuwa mai tsanani, da kuma fatan alheri. Ba da ƙiyayya ba, ba da tsinuwa ba, ba da zagi ba. Sai dai da ƙauna, nasiha, tunatarwa da kuma roƙo na gaskiya daga ɗan uwa zuwa ‘yan uwansa. Ina magana ne kai tsaye zuwa gare ku masu tuƙin ganganci – masu karya doka, masu sa rayuwar kansu da ta jama’a cikin hatsari a kullum. Direbobin motoci masu zaman kansu, masu kabu-kabu, musamman ’yan J5, Golf da Hiace. Masu adaidaita sahu da masu babur, musamman matasa. Da…
Read More
Babbar alamar tashin ƙiyama da ta bayyana

Babbar alamar tashin ƙiyama da ta bayyana

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ Wato idan Duniya ta doso karshenta, lokacin da mutane suka shagala daga barin ubangiji, masu addinai sun maida addini fanko, ba sa aikata abinda su ke ta wa'azi da shi a masallatai da coci-coci. Sannan akasarin al'ummomin Duniya sun raja'a ga Mulhidanci (a yanzu kasashen yamma, Amurka da Turai, da Rasha da China duk suna ta karkata ga Mulhidanci da dakile addini kowane iri). To, a wannan lokaci da mulhidai su ka mamaye dukkan kafafen ci gaban Dan Adam, kama daga na Ilimi, sadarwa, yada labarai dss sannan kuma kaso 1% na al'ummar duniya su ka…
Read More
Su waye ke satar yaran mu na Arewa zuwa Kudu?

Su waye ke satar yaran mu na Arewa zuwa Kudu?

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Wannan batun ba sabo ba ne. An daɗe ana tattaunawa kan yadda ake satar yara ƙanana ko sayar da su kamar gyaɗa ga masu buƙatar yara a wasu jihohin Kudu. Rahotanni da dama sun tabbatar da yadda aka riƙa sace ƙananan yara masu wayo da marasa wayo, daga gidajen iyayensu, a cikin unguwanni, da kasuwanni, zuwa jihohin Anambra, Inugu, Imo, Riba, Kuros Ribas da kuma Delta, har ma da Jihar Legas. Waɗannan yara da shekarun su ba su wuce 18 ba, waɗanda suka haɗa maza da mata, sun fito ne daga jihohin, Filato, Bauchi, Kano, Gombe,…
Read More
Yadda wasu manyan ma’aikatu ke fama da ƙarancin kuɗi a Nijeriya

Yadda wasu manyan ma’aikatu ke fama da ƙarancin kuɗi a Nijeriya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Sabbin alƙaluma daga Ofishin Kasafin Kuɗi na Tarayya sun nuna cewa manyan ma’aikatun da ke kula da muhimman ayyukan raya ƙasa na fuskantar matsananciyar matsalar kuɗi, bayan an gano cewa ƙasa da Naira tiriliyan ɗaya ne aka saki domin ayyukan gwamnati a watanni bakwai na farkon shekarar 2025. A wani rahoto da jaridar Newspoint ta wallafa, ta ce, binciken da aka yi kan bayanan kasafin kuɗi ya nuna cewa, duk da cewa an ware Naira tiriliyan 18.53 domin ayyukan jarin Ma’aikatun Tarayya da hukumomi a kasafin 2025, adadin da aka saki tsakanin Janairu zuwa Yuli bai…
Read More
Ko kun san daga ina ilimin lissafi ya samo asali?

Ko kun san daga ina ilimin lissafi ya samo asali?

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Duk da cewa babu wanda ya san asalin inda ilimin lissafi ya samo asali, amma a yau Blueprint Manhaja za ta yi duba ne kai tsaye zuwa ga ilimin lissafi, duk da cewa babu wani abu da ya rage game da daɗaɗɗen wajen tarihin lissafi da aka lalata a ƙarni na 13, amma mun binciko tare tattaro bayanan masana dangane da inda wajen yake da kuma yadda wajen yake. Sanin asalin ilimin lissafi abu ne mai wahalar gaske amma an fara ganin lissafai masu wahala ne a kusan shekara ta 3000 kafin bayyanar Annabi Isa (300…
Read More
Tumbi: Barazanar lafiya da yadda za a kare kai a zamanin yau

Tumbi: Barazanar lafiya da yadda za a kare kai a zamanin yau

Tare da BILKISU YUSUF ALI A wannan zamani da duniya ke tafiya da sauri, sauyin rayuwa da ɗabi’un cin abinci ya jefa mutane da dama cikin matsalolin lafiya da ba a fiye kulawa da su a baya ba. ɗaya daga cikin irin waɗannan matsaloli ita ce tumbi, wadda ta zama ruwan dare gama gari ga maza da mata, matasa da manya. Duk da cewa mutane da dama na kallon tumbi a matsayin matsalar kamanni kawai, masana lafiya sun jaddada cewa tumbi babbar barazana ce ga lafiyar ɗan Adam idan ba a ɗauki matakin da ya dace ba. Tumbi dai ba…
Read More
Haƙƙin Iyali: Ciyarwa

Haƙƙin Iyali: Ciyarwa

Daga AISHA ASAS Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Iyali na wannan mako, sannunku da jimirin bibiyar jarida mai farin jini, Blueprint Manhaja. A wannan makon, za mu tattauna kan darasin da a wannan zamani ya fi ci wa mata tuwo a ƙwarya tsayin lokaci, musamman ma a ƙasar Hausa. kafin mukai ga tattauna ƙorafin mata kan rashin ciyar da su da mazansu ke yi, bari mu fara kan mazan wanda wataƙila mu samo wata mafita ko fahimta a cikin lamarin. Akwai wani lokaci can bayan a kafar sadarwa ta ɗ wanda a baya aka fi sani da…
Read More
Rikicin cikin gidan PDP: Shin jam’iyyar za ta tsira a 2027?

Rikicin cikin gidan PDP: Shin jam’iyyar za ta tsira a 2027?

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Babbar jam’iyyar adawa ta ƙasa, wato PDP, tana tsaka mai wuya yayin da take tunkarar babban zaɓen 2027. Rikice-rikicen cikin gida, shari’o’in kotu da kuma sauya sheƙar manyan jiga-jigai sun jefa jam’iyyar cikin wani yanayi na rashin tabbas, lamarin da ya sa masana siyasa ke tambayar ko za ta iya sake farfaɗowa kafin babban zaɓe mai zuwa. Rikici mai zurfi tsakanin jiga-jigai: A halin yanzu, PDP ta kasu biyu, inda ɓangare ɗaya ke goyon bayan Nyesom Wike, wani kuma ke tare da Gwamna Seyi Makinde. Rikicin ya ƙara tsananta ne bayan wata kotu a Ibadan ta…
Read More