Rahoto

POS: Tarihinsa da hukuncin amfani da shi wajen kasuwanci da fitar da kuɗaɗe da tura su

POS: Tarihinsa da hukuncin amfani da shi wajen kasuwanci da fitar da kuɗaɗe da tura su

Daga FARFESA AHMAD MURTALA Bismillahir rahmanir rahim. Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga Annanbinmu Muhammad da alayensa da sahabbansa bakiɗaya. Bayan haka, a yau Laraba 23 Jumada Ula, 1442 H.-06 Janairu, 2021 M., na sami tambaya ta fuskoki da yawa har sai da aka rubuto cewa: “Malam ana cikin bukatuwar yin cikakken bayani a dangane da POS. Wasu malaman sun haramta, wasu kuma sun halatta, Mun gode”. Wannan ita ce tambayar. Amma jin akwai wannan sabani na malamai a nan Kasar, ya sa na yi kamar ba zan bada amsa ba. Saboda ban cika son shiga irin mas’alolin…
Read More
Iran fa ta shirya yaƙi

Iran fa ta shirya yaƙi

Daga ALI ABUBAKAR SADIK Kusan duk abinda kasar Iran ta alƙawarta cewa za ta aiwatar matukar Amurka da Israila su ka kai mata hari, to a kwana na ukun wannan yaki babu Wanda ba ta aiwatar ba. Sun lashi takobi kaiwa duk kadarorin Amurka da ke Gabas ta tsakiya da Israila hari. Sannan za su rufe zirin mashigar Tekun Pasha, wato Straight of Hormuz. Zuwa yanzu sun kai hari a wurare 27 a kasashen Israila, Saudi Arabia, UAE, Kuwait, Bahrain, ƙatar, Jordan, Oman da sauransu. Sakamakon kashe Ayatollah Ali Khamenei, mutane da dama sun dauka Iran zata maida martani cikin…
Read More
Tarihin muhimman abubuwan da suka faru a Musulunci cikin watan Ramadan

Tarihin muhimman abubuwan da suka faru a Musulunci cikin watan Ramadan

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ga Musulmin duniya, watan Ramadan wata ne mai tsarki kuma mai cike da alfarma, wanda ya ƙunshi manyan abubuwa masu muhimmanci a tarihin Musulunci. Wata ne na ibada, tausayi da kusantar Allah, inda Musulmai ke gudanar da azumi – ɗaya daga cikin ginshiƙan Musulunci guda biyar. Baya ga kasancewarsa watan ibada da tsarkake zuciya, Ramadan ita ce wata ta tara a kalandar Musulunci, kuma ta zamo shaida ga muhimman abubuwa da suka sauya akalar tarihin addinin Islama. Saukar da Al-ƙur’ani: Mafi girman abin da ya faru a watan Ramadan shi ne saukar da Al-ƙur’ani mai tsarki…
Read More
Motsa jiki da muhimmancinsa ga rayuwar al’umma

Motsa jiki da muhimmancinsa ga rayuwar al’umma

Tare da BILKISU YUSUF ALI Motsa jiki muhimmin al’amar ne, wanda kowa ya kamata ya riƙe wajibi ko farilla a rayuwa. Ana son kowa ya riƙi motsa jiki wani sashe na rayuwa ba tare da an kai jallin likita ya bayar da umarni ko dole ta janyo a yi, don wata larura ta musamman. Motsa jiki wani makami ne da ya kamata kowa ya riƙe a matsayin riga-kafi wanda Bahaushe ya ke cewa ya fi magani.  Amfanin motsa jiki 1. ƙarfafa zuciya da ingata bugun zuciya Motsa jiki na taimakawa wajen rage haɗarin ciwon zuciya da hawan jini. Nazarin masana…
Read More
Waken soya da lafiyar fata: Kyau daga ciki zuwa waje

Waken soya da lafiyar fata: Kyau daga ciki zuwa waje

Daga AISHA ASAS  Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Kwalliya na jaridar Blueprint Manhaja, sannunku da jimirin bibiyarmu. Ya ibada, Allah Ya karɓa daga gare mu. A yau shafin zai waiwaye abincin da ke da tasiri a lafiyar fata wanda yake ɗauke da sinadarai da ke iya ba mu fiye da abinda muke samu a mayukan da muke siya da tsada. Mutane da dama na mayar da hankali kan man shafawa da kayan kwalliya wajen neman fata mai haske da santsi. Sai dai masana sun tabbatar da cewa ainihin kyawun fata yana farawa ne daga ciki, wato daga…
Read More
Hon. Mutu Nicholas Ebomo: Dan majalisa mafi daɗewa a tarihin Nijeriya

Hon. Mutu Nicholas Ebomo: Dan majalisa mafi daɗewa a tarihin Nijeriya

*Shekaru 27 jere a majalisar tarayya tun daga 1999 Daga AISHA ASAS A cikin tarihin siyasar Nijeriya, sunan Hon. Nicholas Mutu Ebomo ya zama ɗan gida, ba baƙo ba, ba kuma mai je-ka-ka-dawo ba, ɗan majalisar mai wakiltar mazaɓar Bomadi/Patani ta Jihar Delta ya zama ɗan majalisar wakilai mafi daɗewa a tarihin ƙasar nan, bayan ya kwashe shekaru 27 ba tare da yankewa ba a zauren Majalisar Wakilai tun daga dawowar mulkin dimokuraɗiyya a 1999. Tun bayan kafuwar Jamhuriya ta Hudu, babu wani ɗan majalisa da ya yi irin wannan dogon zama ba tare da tsayawa ko sauya kujera ba.…
Read More
Me ke kawo lalata da ɗalibai a jami’o’in Nijeriya?

Me ke kawo lalata da ɗalibai a jami’o’in Nijeriya?

Assalamu alaikum, da fatan kowa yana lafiya? Ga duk mai bibiyar al’amuran da suka shafi shafin yanar gizo, ko kuma in ce harkar yaɗ0a labarai a ƙasar nan ya san yadda a ’yan watannin nan ake yawan samun koke-koken game da yadda wani Malaman Jami’o’i ke lalata da ɗalibansu don su ba da maki, ko kuma don a kai su inda ba su kai ba a harkar jarabawa. Ko ba a ce komai ba, wannan wani mummunan abu ne da za a iya cewa bai kama da hakali ba, ko kuma mu ce wani abu ne da ya zama bala’in…
Read More
RAMADAN: Watan kyautatawa maƙwafta da mabuƙata

RAMADAN: Watan kyautatawa maƙwafta da mabuƙata

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Kwanci tashi ba wuya ga mai yawan rai, ga shi yau har an cinye gaɓa ta farko daga cikin gaɓoɓi uku na azumin watan Ramadan. Kamar yadda muka sani azumin watan Ramadan yana da kwanaki talatin ne ko ashirin da tara, kuma ana kasafta shi zuwa gaɓoɓi uku, wato goman farko, goma ta tsakiya da kuma goman ƙarshe. Musulmi a ko’ina a faɗin duniya, suna shagaltuwa da ayyukan ibada da neman ƙarin kusanci ga Allah maɗaukakin sarki, wajen kamewa daga ci da sha da jima’i a lokacin wuni, wato daga ketowar alfijir zuwa faɗuwar rana, da…
Read More
Addinan ’yan Nijeriya sun kore ta’addanci

Addinan ’yan Nijeriya sun kore ta’addanci

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Gaskiyar magana sai dai ɗan ta’adda ko mai zuga tada fitina ya fake da wani addini ko ƙabila don samun mafaka ko dalilin aikata mugun aikinsa. Ba yadda za a yi mai yin sallah da gaskiya ya zama ɗan ta’adda sai dai gafalalle ko munafuki. Kazalika ba mabiyin addinin Kirista na gaskiya da zai yi ta’addanci ko tare matafiya ya sheke su kuma ya iya kafa hujja a BIBLE. Kazalika kawo kabila ko ƙabilanci a lamuran ta’addanci mugun zalunci ne da wasu ke yi don cimma muradin ƙiyayya da ta yi kanta a zuciyarsu. Kama daga…
Read More
Bin doka: Muhimmancinsa da tasirinsa wajen gina al’umma ta gari

Bin doka: Muhimmancinsa da tasirinsa wajen gina al’umma ta gari

Tare da BILKISU YUSUF ALI Bindoka ginshiƙi ce ta zaman lafiya, adalci da daidaito a kowace al’umma. Doka ita ce ke tsara rayuwar jama’a, tana fayyace haƙƙoƙi da nauye-nauyen mutane, tare da samar da tsarin hukunci ga masu karya doka. A duk inda bindoka ta tsaya ƙafafunta, al’umma kan samu kwanciyar hankali, ci gaba da walwala. A gefe guda kuma, inda aka yi watsi da bindoka, rikice-rikice, zalunci da koma bayan tattalin arziƙi kan yawaita. A tarihi da zamani, masana siyasa, shari’a da zamantakewa sun jaddada cewa ba za a iya gina al’umma ta gari ba sai an gina bindoka…
Read More