18
Mar
Tare da BILKISU YUSUF ALI Haɗin kai yana daga cikin manyan ginshiƙai da suke tabbatar da zaman lafiya, cigaba da ɗorewar kowace irin al’umma. Al’umma ba ta iya bunƙasa sai idan mutane suna yin aiki a tare, suna girmama juna, suna taimakon juna tare da fifita muradun kowa a kan na kansa. A tarihi da al’adance, Hausawa sun gina rayuwarsu bisa haɗin kai, wanda ya bayyana ta hanyar karin maganganu kamar “Hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka” da “Taimakon juna ke kawo arziƙi”. Ma’anar haɗin kai Haɗin kai na nufin aiki tare tsakanin mutane ko ƙungiyoyi domin cimma wata manufa…
