29
Mar
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kwanaki kaɗan kafin cikar wa’adin ranar 31 ga Maris, 2026, ɓangaren bankunan Nijeriya ya samu gagarumin ci gaba bayan da bankuna 34 suka samu nasarar cika sabbin sharuɗɗan ƙarfafa jari da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya gindaya. Binciken da aka gudanar ya nuna cewa mafi yawan bankunan ƙasar, musamman manyan bankuna masu lasisin ƙasa da ƙasa da kuma wasu na ƙasa baki ɗaya, sun tsallake ƙalubalen ƙara jari, abin da ke nuna ɗaya daga cikin manyan nasarori a tarihin harkar kuɗi a Nijeriya. Ana sa ran Babban Bankin zai fitar da cikakken rahoto nan ba da…
