Rahoto

Gwamnatin Kebbi ta ja kunnen ‘yan kwangila kan bikin kamun kifi na Argungu 

Gwamnatin Kebbi ta ja kunnen ‘yan kwangila kan bikin kamun kifi na Argungu 

Daga JAMIL GULMA a Kebbi  Gwamnatin jihar Kebbi ta yi kira ga waɗanda aka bai wa kwangilar gyare-gyaren wuraren da za a gudanar da bikin al'adu da kamun kifi na Argungu da su hanzarta su kammala ayyukansu cikin lokaci. Mataimakin gwamnan jihar Kebbi Sanata Umar Abubakar Tafidan Kabi ne ya yi wannan kira a wani rangadin gani da ido a wuraren da za a gudanar da bukukuwan a garin Argungu. Sanata Umar Abubakar ya ce ya kamata 'yan kwangilar su yi aiki tuƙuru ba dare ba rana tare da tabbatar da sun yi aiki mai inganci bisa la'akari da ƙurarren…
Read More
Patrice Lumumba: Gwarzon ’yancin ƙasar Congo

Patrice Lumumba: Gwarzon ’yancin ƙasar Congo

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Patrice Emery Lumumba na daga cikin fitattun jaruman Afirka da suka yi gwagwarmaya wajen kwato ’yanci daga Turawan mulkin mallaka. Sunansa ya shiga tarihi a matsayin Firaminista na farko na Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo bayan samun ’yanci daga Belgium a shekarar 1960. Lumumba ya shahara wajen tsayuwa tsayin daka, kishin ƙasa da kuma adawa da danniya da cin zarafin Afirka. An haifi Patrice Lumumba a ranar 2 ga Yuli, 1925, a ƙauyen Onalua, cikin yankin Katanga na wancan lokaci a Belgian Congo (wanda yanzu ake kira Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo). Ya fito ne daga ƙabilar Tetela. Tun yana…
Read More
Fahimtar juna ko soyayya: Wanne ginin aure ne ya fi ƙarko?

Fahimtar juna ko soyayya: Wanne ginin aure ne ya fi ƙarko?

Tare da BILKISU YUSUF ALI Gabatarwa Auren zamani na fuskantar barazana iri-iri. Sau da yawa muna jin "sun yi shekara biyu da aure, amma sun rabu" ko "aure ya tashi saboda rashin jituwa. “ta kasha mijinta alhali ita ta kawo shi ta ce “ta ji ta gani" “Satinmu biyu da aure amma ya fara faɗamin maganganu marassa daɗin ji” da sauran halaye da ma’aurata kan fuskanta kafin auren ya ci talata da laraba. Waɗannan lamura sun sa mutane da dama tambaya. Shin aure ya fi dorewa ne idan an fara da soyayya mai zafi, ko idan an gina shi bisa…
Read More
Shaye-shaye: Wuta ce da ke cin ginin al’umma cikin sirri

Shaye-shaye: Wuta ce da ke cin ginin al’umma cikin sirri

Daga AISHA ASAS  'Idan ba ka koya wa yaro bin hanya ba, sai ka biyo shi da kuka a bayan titi.' Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Iyali. Sannunku da jimirin bibiyar mu. A wannan mako, za mu yi dubiya ne kan ɗabi'a ta shaye-shaye wadda a can da ana mata kallon ɗabi’a ta 'yan iska, ko waɗanda ba su da mafaɗi. Saidai a yanzu ta zama ruwan dare, game gari, domin za ka iya samun ta har a wurin ɗalibai masu hazaƙa a ƙoƙarin ganin ba su faɗi jarrabawa ba su afka shaye-shaye da sunan maganin hana…
Read More
Ciwon haƙora da yadda za a magance shi

Ciwon haƙora da yadda za a magance shi

Daga AISHA ASAS  (Ci gaba daga makon jiya) A wasu lokuta rashin hasken haƙora kan zama matsala ga mai tare da shi, saboda sau da yawa idan aka kalli haƙoran sai a yi wa mai su kallon ƙazami, duk da cewa, yana wanke su yadda ya kamata.  Sau da dama akan bazama neman man wanke baki da ya dace da haƙoran, a namu tunanin rashin dace da man baki na ƙwarai ne ya janyo hakan. Sai dai abinda ba mu sani ba, wannan matsala ce da ke buƙatar a magance ta kamar kowacce, kafin a ga haƙoran a yanayin da…
Read More
Wani mazaunin Gusau ya yi kira ga Shugaba Tinubu ya sallami Bello Matawalle

Wani mazaunin Gusau ya yi kira ga Shugaba Tinubu ya sallami Bello Matawalle

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau Wani mazaunin Gusau Babban Birnin Jihar Zamfara, Sanusi Lalan Gusau, yayi Kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya sallami ƙaramin ministan Tsaro Hon Bello Mohammed Matawalle daga muƙamin sa. Yayi wannan kiran ne a hirarsa da manema labarai yau Litinin a Gusau. A cewar sa, ƙaramin ministan tsaron ya gaza a ɓangaren kawo karshe ta'addanci da ya addabi al'ummar Jihar ta Zamfara tun lakacin da ya zama ministan. Sanusi Lalan ya bayyana cewar kiran ya zama wajibi la'akari da halin ƙuncin rayuwa da alummar jihar Zamfara su ka samu kansu, sakamakon ayyukan ta'addanci.…
Read More
Burin Biyafara bai cika ba bayan taron Aburi

Burin Biyafara bai cika ba bayan taron Aburi

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Daga ranar 4-5 ga Janairu 1967 wakilan gwamnatin soja ta Nijeriya ƙarƙashin Laftanar Kanar Yakubu Gowon da na ‘yan aware ƙarƙashin gwamnan mulkin soja na jihar kudu maso gabar su ka yi zama a garin Aburi da ke gabashin ƙasar Ghana don kawo maslaha. Dalilin neman maslahar shi ne bayan juyin mulkin soja ranar 15/1/1966 da a ka hakikance ‘yan kabilar Igbo ne su ka shirya har su ka kashe Firaminista Sir Abubakar Tafawa Balewa, Firimiyan Arewa Sir Ahmadu Bello, gwamnan kudu maso yamma Chief Ladoke Akintola; Nijeriya ta shiga zaman zullumi a gwamnatin soja ta…
Read More
Manufar Amurka na kai hari kan mayaƙan Lakurawa

Manufar Amurka na kai hari kan mayaƙan Lakurawa

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A ranar 25 ga watan Disamba na shekarar 2025 da ta gabata, wanda ya zo daidai da ranar da mabiya addinin Kirista a faɗin duniya ke bikin Kirsimeti, Shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya fitar da wata sanarwa a shafinsa na manhajar Trust, cewa dakarun sojan Amurka sun ƙaddamar da mummunan hari kan sansanonin wasu mayaƙa ’yan ta'adda masu alaƙa da Al-ƙaida a Arewa maso yammacin Nijeriya, sakamakon barazanar tsaro da suke haifar wa a yankin sahel dake Afirka ta Yamma. Ba da jimawa ba, Ministan Harkokin ƙasashen Waje, Yusuf Maitama Tuggar ya fito ya shaida…
Read More
Gwamnatin Nijeriya ta ɓullo da sabbin hanyoyin magance satar amsa a jarrabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Nijeriya ta ɓullo da sabbin hanyoyin magance satar amsa a jarrabawar WAEC da NECO

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  A ranar Litinin gwamnatin Nijeriya ta sanar ɗaukar sabbin matakai na magance matsalar satar jarrabawa a yayin rubuta jarrabawar kammala makarantar sakandare (SSCE). Akwai hukumomi da ke shirya jarrabawa da suka haɗa da: WAEC da NECO da NABTEB da sauransu. Kuma wajibi duk mai neman gurbin karatu a manyan makarantu ya gabatar da shaidar samun nasarar a ɗaya daga ciki ko biyu daga cikin waɗanna jarrabawowi. A cikin jawabin mai magana da yawun ma’aikatar ilimi, Folasade Boriowo, ya fitar, ya ce, gwamnati ta sanar da ɗaukar matakai da nufin kyautata sahihancin jarrabawar da dawo…
Read More
Muhimman abubuwan da suka faru a 2025

Muhimman abubuwan da suka faru a 2025

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shekara ta 2025 ta kasance mai cike da sauye-sauye masu zurfi a Nijeriya, inda aka samu mubimman sauye-sauyen tattalin arziki, canjin siyasa da tsanantar ƙalubalen tsaro. Waɗannan abubuwa ne suka fi ɗaukar hankalin jama’a, tare da barin tasiri mai zurfi a rayuwar al’umma da tafiyar dimokuraɗiyyar ƙasar. A ɓangaren ilimi, shekarar ta fara da taƙaddama tsakanin ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya, ASUU, da Gwamnatin Tarayya. Wannan ne karo na farko da ASUU ta shiga yajin aiki tun bayan hawar Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan mulki a 2023. A ranar 13 ga Oktoba, 2025, ASUU ta shiga…
Read More