07
Jan
Daga AISHA ASAS Mai karatu barkanmu da sake ganin zagayowar sati lafiya, Allah Ya sa mu dace da rahmar duniya da ta lahira. A makon da ya gabata, mun fara kwararo bayani kan ƙarin aure, inda muka soma da bayanin halaccin yin mace fiye da ɗaya, zuwa inda muka soma bayani akan ababen da ya kamata a yi dubiya kafin a ƙara aure. Mun kawo ƙarfin aljihu a matsayin ɗaya daga cikin ababen da ya kamata a yi dubiya kansu kafin ƙarin aure, kasancewar ci da sha da kuma muhalli yana wuyan miji. Abu na biyu, wanda za mu soma…
