Rahoto

Yahaya Bello ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Sanata a Kogi ta tsakiya

Yahaya Bello ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Sanata a Kogi ta tsakiya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Sanatan Kogi ta tsakiya a zaɓen 2027 mai zuwa. Bello ya bayyana hakan ne a wata ziyara da ya kai fadar Ohinoyi na Ebiraland, inda ya gana da sarakunan gargajiya, malaman addini da masu ruwa da tsaki na yankin majalisar dattawa. An yaɗa bidiyon ziyarar da kuma bayaninsa a shafin Facebook mai tabbatar da Bello a ranar Litinin. "Na yarda in tsaya takarar majalisar dattawa a 2027," inji tsohon gwamnan yayin da yake jawabi a wurin taron. Gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman…
Read More
Wane ne Adolf Hitler kuma me ya sa ya yaƙi duniya?

Wane ne Adolf Hitler kuma me ya sa ya yaƙi duniya?

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD An aifi Adolf Hitler ranar 20 ga watan Afirilu na shekara 1889, ya kashe kansa ranar 30 ga watan Afirilu na shekara 1945 bayan an ci Jamus da yaki. An aifi Adolf Hitler ranar 20 ga watan Afrilu na shekara 1889 wato shekaru 122 kenan da suka gabata. An aife shi a wani gari mai suna Braunau-am Inn, a ƙasar Austriya kusa da iyakar ƙasar da Jamus. Shi ne na huɗu a gidansu. Mahaifinsa wani jami'in Custum ne, ya rasu a yayin da Hitler ke da shekaru 14 da aihuwa. Marubuta tarihin Hilter sun ce bai…
Read More
Karin aure a wurin Malam Bahaushe

Karin aure a wurin Malam Bahaushe

Daga AISHA ASAS Mai karatu barkan mu da sake kasancewa a shafin Iyali na jarida mai farin jini, Blueprint Manhaja. Allah ya sa mu amfani juna, amin. A yau darasin namu mai tsauri ne, don haka zan yi iya mai yuwa don ganin bai kasance rubutun da za a yi wa mummunar fahimta ba. Kafin mu kai ga darasin namu, bari mu waiwayi abinda littafi mai tsarki Al'ƙur'ani ya faɗa game da auren mace fiye da ɗaya. Allah mazaukakin Sarki Ya faɗa a cikin littafi mai tsarki, "Ku aura daga abinda ya yi muku daɗi na daga mataye, biyu, ko…
Read More
Warin baki: Dalilai, rigakafi da magani

Warin baki: Dalilai, rigakafi da magani

Tare da BILKISU YUSUF ALI Me yake kawo warin baki?  Warin baki (‘halitosis’ a Turance) na nufin ɗaukar warin da ba daɗi daga cikin baki wanda ke daɗewa ko komawa duk da wankin baki. Ana iya samun warin baki saboda dalilai da dama, waɗanda sun haɗa da: Rashin tsaftar baki Wanke baki da goge haƙora sau ɗaya kawai a rana, ko ma rashin goge haƙoran gaba ɗaya. Bakteria (kwayoyin Cuta) su kan taru a tsakanin haƙora da harshe, su fitar da sinadarai masu wari. Cin abinci mai wari A kula yayin cin albasa da tafarnuwa da daddawa da sauran abubuwa…
Read More
Anya Nijeriya za ta gyaru kuwa? 

Anya Nijeriya za ta gyaru kuwa? 

Daga UNCLE LARABI Bar batun gwamnati, mu ma mutanen da ake mulka muna da tamu irin matsalolin da ba su da iyaka. Akwai wata rana na hau Adaidaita Sahu (Keke Napep) daga titin Zoo Road ne zuwa Bata. Tun da akai ƙarin mai kowa ya san Naira 300 ne kuɗin, amma na miƙa wa Mai Napep kuɗi zai ba ni canji ya juya yana shirin tafiya wai ya gan ni Alhaji. Na ce, Alhaji bai san zafin nema ba? Me ya sa na hau Napep ɗinka na bar tawa motar? Ba ni canjina na wuce ko ka ɗauka yau na…
Read More
Dalilin da ya sa malamai kan yi kuskuren fatawa

Dalilin da ya sa malamai kan yi kuskuren fatawa

Daga ALI ABUBAKAR SADIK Akwai misalai da dama wadanda wasu malamai kan yi kuskuren bada fatawa. Amma babban dalilin yin irin wadannan kura-kurai sune: Na farko watsi da akan yi wajen daukar koyarwar ƙur'ani farko a kan duk wani irin hukunci. Sannan na biyu, watsi da ainihin duba yadda Annabi ya rayu a kan mas'alar da a ke kokarin bada fatawar a kai. Na uku shine fifita Fiƙihu akan wadancan guda biyun, da kuma wasu lokatai fifita al'adar larabci a kan ta musulunci. Sannan a karshe watsi da yin tunani a kan matsala domin yarda kawai da cewa wasu Salaf…
Read More
Illar da tsattsauran ra’ayi ke yi mana

Illar da tsattsauran ra’ayi ke yi mana

Daga ALI ABUBAKAR SADIK Wato ina wani shafi da turawa da yan hindu ke da yawa sai naga wani ya yi posting wani labari don a yi dariya tare da ci wa Musulmi mutunci... ga labarin... "Wai wani Musulmi ne a kasar Ingila ya shiga Tasi za a kaishi unguwa. Su na fara tafiya sai direban ya kunna kida. Karaf sai shi wannan Musulmi ya ce "Malam kashe kidan nan saboda musulunci ya haramta kida kuma annabi bai yi ba." Sai dan Tasi ya kashe kidan sannan ya nemi waje ya yi parking ya tsaya sannan ya juyo kan mutumin…
Read More
An samu daidaito tsakanin Nijeriya da Amurka – Idris

An samu daidaito tsakanin Nijeriya da Amurka – Idris

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya ce Nijeriya ta warware rikicin diflomasiyya da ya taso tsakaninta da Amurka, lamarin da ya ƙara ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu. Idris ya bayyana hakan ne a Abuja yayin taron manema labarai na ƙarshen shekara, inda ya ce an cimma matsaya ne ta hanyar tattaunawa mai ƙarfi da mutunta juna.  Ya ce yarjejeniyar haɗin gwiwar kiwon lafiya ta shekaru biyar da darajar dala biliyan 5.1 da aka kulla tsakanin ƙasashen biyu shaida ce ta ƙarfafa alaƙar. A cewarsa, yarjejeniyar za ta ƙarfafa tsarin kiwon…
Read More
Masarautar Katsina da Katsinawa

Masarautar Katsina da Katsinawa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Katsina, babbar masarauta ce, kuma mai daɗaɗɗen tarihi. Tana ɗaya daga cikin asalin garuruwan ƙasar Hausa. Kafin zamowarta wannan babban birni da a yau ya zama helikwatar Jihar Katsina sannan kuma fadar masarautar Katsina, ta taɓa zama a wani gari da yake da tazarar kimanin kilomita 32 daga Katsinan yau. Sunan wannan gari shi ne ‘Durɓi ta Kusheyi’. Wannan gari shi ne asalin fadar mulkin daular Katsina. Wannan masarauta cike take da ababen tarihi, a cikin wancan garin na Durɓi, akwai wannan kuka tana nan, akwai wani Dutse da su mutanen Durɓi suka taba bautawa, sannan…
Read More
Tasirin zagin malamai ga tarbiyyar ‘ya’ya (2)

Tasirin zagin malamai ga tarbiyyar ‘ya’ya (2)

Daga AISHA ASAS Mai karatu barkanmu da sake kasancewa da shafin Iyali na jaridar al'umma, Manhaja. Ya yanayin sanyi da haƙuri da rayuwa. Allah Ubangiji Ya shiga lamurranmu, Ya kyautata rayuwarmu. Idan mai karatu bai yi fashin karanta jaridar Blueprint Manhaja ta makon da ya gabata ba, yana da masaniya kan darasin da muka soma a satin baya, wanda muka yi alƙawarin kawo ci gabansa a wannan mako. Ga waɗanda suka yi fashi kuwa, mun soma darasin namu na tasirin zagin malamai ga tarbiyyar 'ya'ya ne da shimfiɗa kan ummul khaba'isin samuwar rarrabuwar kawuna a tsakanin al'ummar musulmai, wanda ya…
Read More