29
Jun
Daga KHALIFA MUHAMMAD Wata babbar mota ɗauke da kaya ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 19 biyo bayan ƙwacewa da ta yi a garin Imawa da ke ƙaramar hukumar Kura, a Jihar Kano. Haɗarin, ya faru ne a ranar juma'a yayinda wasu masallata ke kan hanyar komawa gida bayan gabatar da sallar juma'a inda nan take ya yi sanadiyyar mutuwar mutane goma sha huɗu tare da raunata wasu da dama. A lokacin da yake jawabi, Kwamandan reshen jihar Kano na hukumar kula da haɗurra ta ƙasa (FRSC), Ibrahim Abdullahi, ya ce sun tabbatar da aukuwar lamarin wanda ya faru da misalin…
