Labarai

Abin da ya sa muka sadaukar da albashinmu ga mutanen Tudun Biri — Ndume

Abin da ya sa muka sadaukar da albashinmu ga mutanen Tudun Biri — Ndume

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 'Yan Majalisar Dattawan Nijeriya 109 sun sanar da sadaukar da albashinsu na wata guda ga dangin mutanen da harin kuskuren da rundunar sojin Nijeriya ta kai garin Tudun Biri, da ke Ƙaramar Hukumar Igabi, a jihar Kaduna ya yi ajalinsu. 'Yan Majalisar sun ce za a yi amfani da kuɗin, da yawansu ya kai Naira miliyan 109, wato miliyan guda daga kowanne sanata domin hidimtawa mutanen, da zummar rage masu raɗaɗin halin da suke ciki. Sanata Ali Ndume, mai tsawatarwa a majalisar dattawan Nijeriyar, wanda kuma ke cikin 'yan Majalisar da suka ziyarci jihar…
Read More
Amurka da Birtaniya sun ƙara wa Hamas takunkumai

Amurka da Birtaniya sun ƙara wa Hamas takunkumai

Amurka da Birtaniya sun sanar da ƙara wa Hamas sabbin takunkumai sakamakon harin da ƙungiyar ta kai wa Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoban, inda aka samu salwantar rayuka. Ma'aikatar Baitul Malin Amurka ta ce, wannan matakin ya shafi manyan jami'an da ke ruruta manufar ta'addacin Hamas ta hanyar wakiltar manufofin ƙungiyar a ƙasashen ƙetare tare da kula da asusunta. Tun bayan harin na Oktoba da ƙungiyar ta ƙaddamar da ya kashe kimanin mutane dubu ɗaya da ɗari biyu, akasarinsu fararen hula, tare da garkuwa da mutane 240, Amurka ke matsin lamba kan mayaƙan. Baitul Mali Amurka ya ce,…
Read More
Tsadar rayuwa: Ku ƙara haƙuri da lamarin Tinubu, roƙon Malagi ga ‘yan Nijeriya

Tsadar rayuwa: Ku ƙara haƙuri da lamarin Tinubu, roƙon Malagi ga ‘yan Nijeriya

Daga BASHIR ISAH Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan ‘Yan Ƙasa, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ya roƙi ‘yan Nijeriya da su ƙara haƙuri da lamarin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu dangane da sabbin tsare-taren da ta fitar da nufin daidaita tattalin arzikin ƙasa. Malagi ya yi wannan roƙo ne sa’ilin da yake jawabi a wajen taron ƙaddamar da littafi ranar Alhamis a Birnin Tarayya. Ministan ya yarda cewa lallai ‘yan Nijeriya na fuskantar tasku sakamakon sabbin tsare-tsaren gwamnati, yana mai ccewa gwamnatin na yin abin da take yi ne domin daidaita wa tattalin arzikin ƙasa zama yadda ya kamata.…
Read More
Gwamnan Zamfara ya jajanta wa al’ummar Zurmi bisa harin ‘yan bindiga, ya jinjina wa jami’an tsaro

Gwamnan Zamfara ya jajanta wa al’ummar Zurmi bisa harin ‘yan bindiga, ya jinjina wa jami’an tsaro

Gwamna Dauda Lawal ya jajanta wa al’ummomin da hare-haren ‘yan bindiga ya shafa a baya-bayan nan, ya kuma yaba wa sojoji bisa kokarinsu. Akwai rahotanni masu kyau da yawa na kawar da dimbin ‘yan bindiga a Zamfara da sauran dazuzzukan Arewa maso Yamma. A wata sanarwa da mai magana da yawun sa, Sulaiman Bala Idris ya fitar, gwamna Lawal ya nuna matuƙar damuwarsa kan hare-haren da aka kai a karamar hukumar Zurmi. Ya ce duk da hare-haren da ‘yan bindigar ke kai wa, rahotanni masu inganci sun nuna an kawar da fitattun shugabannin ‘yan bindigar da ke aiki a jihar…
Read More
Rashin lafiyar Gwamnan Ondo ya haifar da naɗa Mataimaki muƙaddashi

Rashin lafiyar Gwamnan Ondo ya haifar da naɗa Mataimaki muƙaddashi

Daga BASHIR ISAH Majalisar Dokokin Jihar Ondo ƙarƙashin jagorancin Kakinta, Olamide Oladiji, ta ayyana Mataimakin Gwamnan Jihar, Lucky Aiyedatiwa a matsayin muƙaddashin gwamna. Hakan ya biyo bayan wasiƙar da majalisar ta ce ta samu ne daga Gwamnan Jihar, Oluwarotimi Akeredolu, kan buƙatar miƙa ragamar mulkin jihar ga mataimakimsa kasancewar zai tafi hutun jinya. A ranar Laraba, Kakakin majalisar ya ayyana Aiyedatiwa a matsayin muƙaddashin gwamnan jihar a Akure, babban birnin jihar. A cikin sanarwar da ya yi a zauren majalisar, Kakakin ya ce: “Biyo bayan shawarar da likita ya bayar ta buƙatar zuwa duba lafiyarsa, Gwamnan Jihar Ondo, Oluwarotimi Odunayo…
Read More
Tonon Silili: Da hannun wasu ‘manyan ƙasa’ cikin ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda a Nijeriya, in ji Minista

Tonon Silili: Da hannun wasu ‘manyan ƙasa’ cikin ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda a Nijeriya, in ji Minista

Daga BASHIR ISAH Ministan Ma'adinai, Mr Dele Alake, ya bayyana cewa da hannun wasu manyan ƙasa a harkar ɗaukar nauyin 'yan ta'adda da haƙar ma'adinai ta ɓarauniyar hanya a Nijeriya. Jaridar News Point Nigeria ta rawaito cewar, Alake ya yi wannan tonon sililin ne sa'ilin da ya bayyana a gaban Kwamitin Majalisar Wakilai Kan Ma'adinai don kare kasafin ma'aikatarsa na shekarar 2024 a Abuja. Kazalika, Ministan ya yi zargin akwai baƙi da ke haƙar ma'adinai a Nijeriya ba bisa ƙa'ida ba. Don haka ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta maida hankali sosai kan fannin ma'adinai wanda ka iya samar wa…
Read More
Gwamnatin Zamfara ta kammala kashi na biyu na shirin kula da lafiya kyauta

Gwamnatin Zamfara ta kammala kashi na biyu na shirin kula da lafiya kyauta

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Jihar Zamfara ta kammala kashi na biyu na shirin kula da lafiyar al'ummar jihar kyauta da ta faro. Sanarwar da mai magana da yawun Gwamna, Sulaiman Bala Idris ya fitar ta ce, a watan Agustan da ya gabata kashin farko na shirin kula da lafiya kyautar ya kankama inda aka yi wa masu fama da lalurori daban-daban magani ba tare da sun biya ko taro ba. Idris ya ce mutum 1,858 ne aka samu nasarar yi musu magani a tsakanin kashin farko da na biyu na shirin. Ya ƙara da cewa, an fara kashi na biyu…
Read More
Tinubu ya yi matuƙar damuwa kan iftila’in Tudun Biri – Malagi

Tinubu ya yi matuƙar damuwa kan iftila’in Tudun Biri – Malagi

Daga BASHIR ISAH Ministan Labarai da Wayar da Kan 'Yan Ƙasa Mohammed Idris, ya bayyana cewa, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya nuna damuwa matuƙa kan iftila'in da ya auku a yankin Tudun Biri, Jihar Kaduna inda sojoji suka jefa wa masu taron maulidi bom bisa kuskure. Hadimin Ministan, Rabiu Ibrahim, ya bayyana a cikin sanarwar da ya fitar ranar Litinin cewa, Malagi ya bayyana haka ne a wajen taron Babban Kwamitin Shugabancin Jama’atu Nasril Islam (JNI) da ya gudana ran Litinin a Minna, babban birnin Jihar Neja. Ministan ya nuna godiyar gwamnatin ga sarakunan gargajiya da shugabannin addini bisa ƙoƙarin…
Read More
Fannin kare haƙƙin ɗan-Adam na buƙatar jajirtattun mutane – MƊD

Fannin kare haƙƙin ɗan-Adam na buƙatar jajirtattun mutane – MƊD

Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres ya jaddada ƙa'ida cewa, “an haifi kowani ɗan Adam da ‘yanci kuma suna da mutunci da haƙƙi." Guterres ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa don cika shekaru 75 da ƙaddamar da yarjejeniyar kula da haƙƙoƙin bil’adama na duniya a ranar 10 ga Disamba 2023. Ya ce, “Yarjejeniyar Haƙƙin ɗan-Adam ta Duniya tana da mahimmanci a yau kamar yadda take a lokacin da aka amince da ita shekaru 75 da suka gabata. “Yarjejeniyar duniya taswirar hanya ce, tana taimaka wa kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe da haɓaka rayuwar zaman lafiya da mutunci ga duka…
Read More
CBN ya dakatar da cajin da bankuna kan yi wa kostomomi yayin ajiyar kuɗaɗe

CBN ya dakatar da cajin da bankuna kan yi wa kostomomi yayin ajiyar kuɗaɗe

Daga BASHIR ISAH Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya dakatar da harajin da akan karɓa yayin da kostomomi suka kai kuɗi mai yawa ajiya a banki. Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da Muƙaddashin Daraktan Sanya Ido, Dr Adetona Adedeji, ya fitar a ranar Litinin. “Dukkanin bankunan da ke ƙarƙashin kulawar CBN su ci gaba da karɓar ajiyar kostomominsu ba tare da sun caje su komai ba," in ji CBN. Bankin ya kuma buƙaci bankuna da su bi wannan umarnin nasa sau da ƙafa. Sanarwar ta ce sabuwar dokar da aka samar a Disamban 2019, mai lamba FPR/DIR/GEN/CIR/07/042, ita ce ta…
Read More