Labarai

Sarkin Katsina bai kori shirin AGILE a jihar ba

Sarkin Katsina bai kori shirin AGILE a jihar ba

Daga UMAR GARBA a Katsina A ƙarshen makon da ya gabata wasu kafafen yaɗa labarai sun ruwaito cewar, Mai Martaba Sarkin arkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir Usman, ya kori shirin nan da ke inganta ilimin 'ya'ya mata wato AGILE a taƙaice, a wasu jihohin ƙasar nan ciki har da jihar Katsina. Lamarin ya jawo cece-kuce musamman a kafafen sada zumunta bayan da wani babban malami da wasu jama'ar arewacin ƙasar nan suka zargi shirin da lalata tarbiyyar 'yan mata ta hanyar koya masu wasu ɗabi'u da ka iya sa 'yan matan su bijire wa addini da ma al'ada. Sarkin labarai…
Read More
Mutanen Tudun Biri sun yi shahada, in ji Shugaba Tinubu

Mutanen Tudun Biri sun yi shahada, in ji Shugaba Tinubu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake nuna baƙin cikin sa kan harin bom da ya kashe mutane a garin Tudun Biri. Ya kuma yi wa mamatan fatan samun shahada. Da yake jawabi a Masarautar Maiduguri a ziyarar da ya kai Jahar borno don halartar taron Chief of Army Staff Conference a yau litinin Shugaban ya ce: "Har yanzu ina ƙara jaddada mana ta'aziyya kan asarar rayukan da muka yi a Kaduna, abin babu dadi Sam, amma a matsayin mu na mutanen da suka yi imani da ƙaddara dole mu karɓi wannan lamari a matsayin ƙaddara, sannan mu jajirce wajen…
Read More
Za a iya amfani da Zakkat da Waƙafi a yaƙi da talauci a Nijeriya – AZAWON

Za a iya amfani da Zakkat da Waƙafi a yaƙi da talauci a Nijeriya – AZAWON

Daga MUKHTAR A. HALLIRU TAMBUWAL a Dutse Shugaban ƙungiyar Hukumomi da ƙungiyoyin da ke aikin tattara Zakka da Waƙafi a Nijeriya, AZAWON, Malam Muhammad Lawal Maidoki, ya bayyana cewa, matuƙar za a yi amfani da kuɗaɗen da ake tattarawa daga Zakka da Waƙafi da sadakoki da masu hannu da shuni ke fitarwa, domin yaƙi da talauci, yunwa, da ƙuncin rayuwa da ake fuskanta a ƙasar nan. Malam Muhimmad Lawal Maidoki (Sadaukin Sokoto) ya bayyana haka ne a yayin ƙaddamar da fara babban taron haɗaɗɗiyar ƙungiyar AZAWON ta ƙasa karo na 3, a garin Dutse, Babban Birnin Jihar Jigawa. A cewarsa,…
Read More
Fitacciyar ma’aikaciyar NTA, Aisha Bello ta kwanta dama

Fitacciyar ma’aikaciyar NTA, Aisha Bello ta kwanta dama

Daga BASHIR ISAH Allah Ya yi wa fitacciyar ma'aikaciyar tashar talabijin ta tarayyar (NTA), Aisha Bello Mustapha, rasuwa. A ranar Lahadi Aisha ta rasu amma sai a Litinin aka yaɗa batun rasuwar wanda ya zuwa haɗa wannan labari ba a bayyana abin da ya yi ajalin marigayiyar ba. A halin rayuwarta, marigayiyar ta yi fice musamman a fagen karanta labatai a tashar NTA. 'Yan ƙasa da dama sun bayyana kaɗuwarsu game da Aisha duba da irin gudunmawar da ta bayar ga ɓangaren yaɗa labarai. Da misalin ƙarfe ɗaya na ranar Litinin aka yi wa marigayiyar sallar janaza a Babban Masallacin…
Read More
Shugabanci nagari ne kaɗai hanyar magance matsalar juyin mulki – ECOWAS

Shugabanci nagari ne kaɗai hanyar magance matsalar juyin mulki – ECOWAS

Shugaban Ƙungiyar ECOWAS, Bola Tinubu, ya roƙi shugabannin ƙasashen yammacin Afirka da su ba da fifiko wajen gudanar da shugabanci nagari da samar da walwalar jama’a, a matsayin wani muhimmin makamin yaƙar juyin mulki a yankin. Da yake jawabi a wajen taron ECOWAS karo na 64 da ya gabata a ranar Lahadi, shugaban ya bayyana gudanar da shugabanci nagari a matsayin wani babban ginshiƙi na samar da goyon bayan jama'a ta hanyar kawo sauyi ga al'umma da tattalin arziki da cigaban yammacin Afirka. “Samar da shugabanci nagari ba wai kawai zallar nasarar samin shugabanci ba ce, hanya ce ta magance…
Read More
Tudun Biri: Sanatoci sun sadaukar da albashinsu na wata guda ga waɗanda harin bom ya shafa

Tudun Biri: Sanatoci sun sadaukar da albashinsu na wata guda ga waɗanda harin bom ya shafa

Daga BASHIR ISAH Baki ɗayan sanatocin Tarayyar Nijeriya su 109 sun yanke shawarar sadaukar da albashinsu na wata guda da ya kai Naira miliyan 109 ga waɗanda iftila'in harin bom ya shafa a Tudun Biri, cikin Ƙaramar Hukumar Igabi, Jihar Kaduna. Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin ne ya bayyana haka ranar Lahadi a Fadar Gwamnatin Jihar Kaduna yayin da ya jagoranci tawagar Majalisar Dattawa zuwa jihar don miƙa ta'aziyya da kuma jajantawa. Gwamnan Jihar, Sanata Uba Sani, shi ne ya tarbi tawagar yayin ziyarar. Cikin sanarwar da ya fitar ta hannun hadiminsa Ismail Mudashir, Sanata Barau ya ce…
Read More
Kisan masu mauludi: Za a hukunta masu hannu ciki – Tinubu

Kisan masu mauludi: Za a hukunta masu hannu ciki – Tinubu

*A na cigaba da tir da kisan ’yan mauludi a Kaduna*Za mu biya diyya, inji Gwamnatin Tarayya *Fasahar zamani za ta rage tashin boma-bomai – Amurka ga sojojin Nijeriya Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa al’ummar ƙasar cewa duk wanda aka samu da hannu a harin bom da aka kai ƙauyen Tudun Biri wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 90 za a hukunta shi. Shugaban Ƙasar ya kuma bayar da tabbacin cewa, za a kula da duk waɗanda abin ya shafa a ƙarƙashin shirin tallafi na Folako Initiative da za a…
Read More
Kashi 70 na ma’aikatan kamfanin Mamuda ‘yan Kano ne – Gaddafi

Kashi 70 na ma’aikatan kamfanin Mamuda ‘yan Kano ne – Gaddafi

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Gaddafi Isyaku Hassan, jami'in cinikayya na kamfanin Mamuda, ya ce suna bada gudunmuwa ga mata domin ƙara musu ƙwarin gwiwa wajen sana'ar dogaro da kai, tarbiyya a zamantakewarsu na rayuwar aure a tarukansu daban-daban. Ya bayyana hakan ne ga manema labarai a wani taro da wasu mata suka gudanar da kamfanin ya bajekolin kayyakinsa da makarantu don qara musu ƙwarin gwiwa. Jami'in ya ce irin gudummuwar da suke bayarwa bai tsaya ga cigaban mata kaɗai ba har da ɓangaren ilimi har sai da ma'aikatar ilimi ta jihar Kano ta karramasu bisa irin jajircewa da  taimako…
Read More
Gwamnan Katsina ya bada umarnin dakatar da malami bisa zargin lalata da ɗalibarsa

Gwamnan Katsina ya bada umarnin dakatar da malami bisa zargin lalata da ɗalibarsa

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnan jihar Katsina Umar Dikko Raɗɗa, ya bayar da umarnin dakatar da wani shugaban makarantar sakandare ta gwamnati da ke garin Ɗantankari a ƙaramar hukumar Ɗandume, bisa zarginsa da neman ɗalibarsa da lalata. Bayanin haka na ƙunshe cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na ofishin sakataren gwamnatin jihar Abdullahi Aliyu 'Yar'adua ya saka wa hannu. A cewar sanarwar "Mai girma Gwamna ya karvi rahoton dake nuni da cewa ana zargin wani Lawal Ibrahim akan cin zarafin wata ɗaliba ta hanyar nemanta da lalata wanda shugaban makarantar sakandaren Ɗantankari ne dake ƙaramar hukumar Ɗandume. "Saboda…
Read More
Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda da dama a Zamfara

Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda da dama a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau Dakarun rundunar haɗin guiwa ta arewa maso yammacin Najeriya Operation Hadarin Daji (OPHD) sun daƙile harin da 'yan ta'adda suka kai kauyen Danjibga dake ƙaramar hukumar Tsafe tare da daƙile ɓarnar amfanin gona a ƙauyen Faru dake ƙaramar hukumar Maradun duk a jihar Zamfara inda suka samu nasarar Kashe wasu da dama a batakashin da suka yi. Sojojin sun ce a yayin arangamar da ‘yan ta’addan sun samu nasarar hallaka guda uku daga cikin 'yan ta'addan, an kuma ƙwato bindigogi kirar AK-47 guda 3, kwanson alburusai 3, da kuma babura biyu. "A ranar 7 ga…
Read More