Labarai

Amurka da Saudiyya sun gaza kawo ƙarshen rikicin Sudan

Amurka da Saudiyya sun gaza kawo ƙarshen rikicin Sudan

An gaza samar da cigaba a tattaunawar kawo ƙarshen rikicin Sudan da Saudiyya da Amurka suka kasance masu shiga tsakani, yayin da rashin jituwa tsakanin manyan hafsoshin sojin ƙasar biyu ta haifar da ƙalubale ga ayyukan jin ƙai a ƙasar. Rashin cigaba a tattaunawar da ke faruwa a birnin Jedda, ya rushe fatan da mutum sama da miliyan shida da rabi a ciki da wajen ƙasar ke yi, abin da ya ƙara haifar da taɓarɓarewar tattalin arziki da kuma rikicin ƙabilanci a Darfur. Yayin da rundunar sojin Sudan ɗin ta ce, ta ƙwace ikon babban birnin ƙasar, Khartoum, dakarun kai…
Read More
Mun shirya taron mata ne don ƙarfafa musu gwiwa kan sana’o’i – Stephanie Obia

Mun shirya taron mata ne don ƙarfafa musu gwiwa kan sana’o’i – Stephanie Obia

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano A ranar Asabar ɗin makon da ya gabata ne Zauren Mata da aka fi sani da "Mata Annual Conference" suka gudanar da taronsu na shekara a jihar Kano. Taron wanda ya samu halartar mata da kamfanoni daga ciki da wajen jihar Kano inda aka gudanar da jawabai na ƙarfafa gwiwar mata akan sana'o'i na dogaro da kai da kuma kyautata zamantakewa da mazajensu. Da take jawabi akan maƙasudin taron ɗaya daga cikin jami'ar da suka shirya taron, Stephnie Obia wacce 'yar ƙabilar Ibo ce haifaffiyar jihar Kano ta ce wannan shi ne taro karo na…
Read More
Masu buƙata ta musamman sun koka kan rashin wakilcinsu a gwamnatin Katsina

Masu buƙata ta musamman sun koka kan rashin wakilcinsu a gwamnatin Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Masu buƙata ta musamman a jihar katsina sun koka akan rashin wakilcinsu a majalisar zartaswa na gwamnatin Gwamna Dikko Umar Raɗɗa.            Hakan na faruwa ne duk da cewa an aiwatar da doka da ta bada kulawa na musamman a Nijeriya a lokacin gwamnatin Muhammadu Buhari da ta wuce.                              Shugaban ƙungiyar masu buƙata na musamman reshen jihar, Nasiru Dauda 'Yansiliyau ya faɗa wa manema labarai haka da yake magana akan ranar masa buƙata ta duniya.       …
Read More
An yanke hukuncin kisa ga sojan da ya kashe Sheikh Goni Aisami

An yanke hukuncin kisa ga sojan da ya kashe Sheikh Goni Aisami

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kotu ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga sojan da ya kashe fitaccen malamin Musulunci a Jihar Yobe, Sheikh Goni Aisami. Babbar Kotun Jihar Yobe da ke zama a garin Potiskum, ta yanke wa korarren sojan, Las Kofur John Gabriel hukuncin rataya ne a ranar Talata. Alƙalin kotun, Usman Zanna Mohammed, ya kuma yanke wa abokin lafinsa, Las Kofur Adamu Gideon, hukuncin ɗaurin shekara 10 a gidan yari. Mai shari’a Usman Zanna Mohammed ya yanke wa Gabriel hukuncin ne ƙarƙashin dokar soja. Sojan da za a rataye yana aiki ne da bataliya ta…
Read More
’Yan bindiga sun wawashe takardun kotun zaɓen gwamnan Kogi

’Yan bindiga sun wawashe takardun kotun zaɓen gwamnan Kogi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu 'yan bindiga sun kai hari kan magatakardan Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓen gwamnan Jihar Kogi, David Umar Mike, tare da kwashe takardun masu ƙara. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar (PPRO), SP William Aya, ya bayyana hakan a Lokoja ranar Laraba. Hukumomin 'yan sandan sun ce maharan da suka kai harin na sakatariyar kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar sun kwashe dukkanin takardun ƙarar da wasu jam’iyyun siyasa biyar suka shigar. A cewar hukumomin ’yan sanda, takardun da aka kwace daga hannun Mike sun haɗa da, ƙorafe-ƙorafen da jam’iyyu huɗu (4): Action Alliance…
Read More
Gwamnatin Zamfara ta ƙwato motoci 50 daga hannun Matawalle

Gwamnatin Zamfara ta ƙwato motoci 50 daga hannun Matawalle

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce, ta kwato motoci kusan 50 mallakin gwamnatin jiha da ake zargin tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle ya tafi da su. Da yake zantawa da manema labarai ranar Alhamis a Gusau, Sani Sambo, mai magana da yawun gwamna Dauda Lawal ya ce matakin ya biyo bayan hukuncin da wata babbar kotun tarayya da ke Sokoto ta yanke a ranar Juma’ar da ta gabata. Ya qara da cewa, an bi tsarin da ya dace domin kwato motocin daga gidajen Gusau da Maradun na tsohon gwamnan wanda a baya ya musanta cewa ya mallaki…
Read More
Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya 9,000 daga 13,000 sun faɗi jarrabawar ƙarin girma

Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya 9,000 daga 13,000 sun faɗi jarrabawar ƙarin girma

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Aƙalla ma’aikatan gwamnati 9,000 da suka zana jarrabawar ƙarin girman ma’aikatan Gwamnatin Tarayya na shekarar 2022 sun faɗi. An samu wannan adadi ne daga Hukumar Ɗa’ar Ma’aikata ta Tarayya.An ce aƙalla ma’aikatan gwamnati 13,000 ne suka zana jarrabawar ta shekarar 2022, wadda aka gudanar a kusan cibiyoyin gwajin kwamfuta 69. An zaɓo ma'aikatan ne daga manyan ma’aikatan gwamnati, ’yan sandan Nijeriya, da sauran jami’an soji da sauran hukumomin tsaro. Wasiƙar mai ɗauke da jerin sunayen ma’aikatan da suka yi nasara ta kasance a ranar 30 ga Nuwamba, 2023 kuma an aiko ta daga Hukumar Kula da…
Read More
’Yan bindiga sun sake sace ɗaliban jami’ar Nasarawa

’Yan bindiga sun sake sace ɗaliban jami’ar Nasarawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu ’yan ta'adda da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun afka wa al’ummar Gandu tare da yin garkuwa da wasu ɗalibai a Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Lafia. Wani ɗalibin jami’ar da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa manema labarai cewa 'yan bindigar sun zo ne da farko a yawansu da misalin ƙarfe 7:30 na yammacin ranar Laraba inda suka fara harbi a iska don tsoratar da mazauna yankin, amma daga baya sun fara harbi kan mai uwa da wabi, lura da cewa jami'an tsaro na tahowa sai suka tsere cikin daji domin…
Read More
Kotu ta yanke hukuncin kisa kan matashin da ya kashe abokinsa saboda N100 a Zamfara

Kotu ta yanke hukuncin kisa kan matashin da ya kashe abokinsa saboda N100 a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Wata Babbar Kotun Jihar Zamfara ta yanke wa wani Anas Dahiru hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsa da laifin kashe abokinsa a kan Naira 100. An gurfanar da Dahiru kotu ne a watan Yunin 2017 bisa zargin kashe abokinsa Shamsu Ibrahim inda ya daɓa masa wuƙa har lahira a lokacin da suke faɗa da juna saboda Naira 100. Da yake karanta hukuncin, Alƙalin Kotun, Mai shari’a Mukhtar Yusha’u ya ce wanda ake zargin Anas Dahiru da ke Unguwar Dallatu a garin Gusau a Jihar Zamfara, ya gurfana a gaban kotu a shekarar 2017 bisa…
Read More
Za a shiga mummunan bala’i a Gaza idan ba ku ɗauki mataki ba – MƊD

Za a shiga mummunan bala’i a Gaza idan ba ku ɗauki mataki ba – MƊD

Daga WAKILINMU Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya (MƊD), Antonio Guterres, ya rubuta wasiƙa ga kwamitin tsaro na majalisar, inda ya nemi ƴan kwamitin su taimaka don kauce wa mummunar annoba a Gaza. "Yayin da ake fuskantar shiga bala'in rasa agaji a Gaza, ina neman Kwamatin ya taimaka wajen kauce wa aukuwar bala'i, kuma ya nemi a tsagaita wuta don kai agaji," in ji Guterres a cikin wani saƙo da ya walafa ranar Laraba. Cikin wasiƙar da ya rubuta, Guterres ya nanata cewa yanayin na ƙara ƙazancewa cikin sauri, ta yadda ba za a iya gyara wa Falasɗinawa komai ba…
Read More