Labarai

NDLEA ta kama ton 15.7 na haramtattun ƙwayoyi a Kano

NDLEA ta kama ton 15.7 na haramtattun ƙwayoyi a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar NDLEA reshen jihar Kano a ranar Litini ta ƙona tan 15.7 na haramtattun ƙwayoyi da ta kama a jihar. Shugaban hukumar Buba Marwa ya ce dakarun hukumar da jami’an tsaron tashar jiragen saman Malam Aminu Kano MAKIA suka kama haramtattun ƙwayoyin tsakanin watan Oktoba 2020 zuwa Oktoba 2023. Marwa wanda Shugaban fannin gudanar da bincike na hukumar Samuel Bashir-Gadzama ya wakilta ya ce hukumar ta ƙona waɗannan muggan ƙwayoyi domin daƙile yaɗuwarsu cikin al’umma. Shugaban hukumar na jihar Kano Abubakar Idris-Ahmad ya ce daga cikin tan 15,193.365 da aka ƙona akwai kilogiram 9,824.098…
Read More
Gwamna Lawal ya sha alwashin ganin bayan ‘yan fashin daji a Zamfara

Gwamna Lawal ya sha alwashin ganin bayan ‘yan fashin daji a Zamfara

Daga BASHIR ISAH Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya sha alwashin kawo ƙarshen 'yan fashin dajin da suka addabi jihar. Ya bayyana haka ne a ranar Laraba sa'ilin da ya ziyarci sansanin bai wa Dakarun Rundunar Kare Alumma (CPG) inda suke karɓar horo, shirin da gwamnatin jihar ta ƙirƙiro domin daƙile 'yan fashin daji a faɗin jihar ta Zamfara. Cikin sanarwar da ya sanya wa hannu wadda MANHAJA ta samu kwafi, Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya ce horon da dakarun ke ci gaba da karɓa ya ƙara wa jihar da ma al'ummarta ƙwarin gwiwa dangane da sha'anin yaƙin…
Read More
‘Yan sanda sun hallaka shugabannin ‘yan bindiga a Katsina

‘Yan sanda sun hallaka shugabannin ‘yan bindiga a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Rundunar 'yan sanda ta Jihar Katsina ta bayyana cewar ta samu nasarar kashe wasu manyan shugabannin 'yan bindiga uku da su ka addabi al'umar jihar. Daga cikin waɗanda aka kashe akwai ƙasurgumin ɗan bindiga Bala wuta wanda ya addabi ƙaramar hukumar Jibiya, sauran su ne Dogo na Sahura da kuma Hassan Bukuru. Bayanin haka na ƙunshe cikin wata sanarwa da Kakakin rundunar, ASP Abubakar Aliyu ya fitar ranar Laraba a Katsina. Ya ce, arangamar ta faru ranar 25 ga watan Nuwamba,2023 da misalin ƙarfe 10:30 na safe lokacin da su ke gudanar da sintirin haɗin…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda biyu a Imo

‘Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda biyu a Imo

Daga BASHIR ISAH Aƙalla mutum uku ciki har da 'yan sanda biyu sun mutu sakamakon sabon harin da 'yan bindiga suka kai a yankin Ƙaramar Hukumar Ahiazu Mbaise, Jihar Imo. Rahotanni sun ce, harin ya auku ne a ranar Litinin, 27 ga Nuwamban 2023, inda ɓata-garin suka buɗe wa 'yan sandan wuta wanda a nan take suka hallaka jami'ai biyu da wani mutum guda. Majiyarmu ta ce harin ya auku ne a lokacin da sabon Kwamishin 'Yan Sandan Jihar, Danjuma Aboki, ya kai ziyarar aiki a yankin Mbaise domin ƙara wa jami'ansu ƙwarin gwiwa. Mai magana da yawun rundunar 'yan…
Read More
Babban Hafsan Tsaro ya buƙaci ƙarin tallafi ga fannin tsaro

Babban Hafsan Tsaro ya buƙaci ƙarin tallafi ga fannin tsaro

*Sojoji sun kammala atisayen "Operation Mugun Bugu" Daga BASHIR ISAH Babban Hafsan Tsaro na Nijeriya, Janar Christopher Musa, ya yi kira da a ƙara tallafin da ake bai fannin tsaro musamman ɓangaren mayaƙan sama domin ci gaba da ƙarfafa musu game da yaƙi da matsalar tsaro. Kiran na zuwa ne a lokacin da Rundunar Sojin Nijeriya ke kammala atisayen “Operation Mugun Bugu" na makonni wanda shi ne irinsa na biyu da ta shirya a 2023. Yayin atisayen wanda ya gudana a garin Kontagora, Jihar Neja, dakarun sun yi gwajin makamai tare da ɗaukar sabbin dabarun aiki. Da yake jawabi ta…
Read More
NARTO suna ƙoƙarin wajen wayar da kan direbobi – Muhammad Inuwa

NARTO suna ƙoƙarin wajen wayar da kan direbobi – Muhammad Inuwa

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano Alhaji Muhammad Inuwa Sakataren Ƙungiyar Masu Motocin Sufuri na Ƙasa, rashen Jihar Kano ya bayyana cewa, ƙungiyar su ta NARTO na taka muhimmiyar rawa wajen ganin ma'aikatan su sun bi duk kanin ƙa'idojin tuqi da kuma kula da lafiyar ababan hawan su a koda yaushe domin ganin an rage munanan haɗurran da akan samu akan hanyoyinmu na Nijiriya musamman a watanni huɗu ƙarshen kowacce Shekara. Kamar dai yadda sakataren ƙungiyar NARTO na Kano ya bayyana a lokacin taron wata ƙungiya mai suna MAMA da ta shirya don wayar da kan masu tuƙa ababan hawa da…
Read More
Gwamnan Kano ya naɗa sabon Shugaban Ma’aikatan Jihar

Gwamnan Kano ya naɗa sabon Shugaban Ma’aikatan Jihar

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin Alhaji Abdullahi Musa a matsayin sabon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar. Hakan dai na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya aiko wa Manhaja, Inda ya ce naɗin na zuwa ne bayan da tsohon shugaban ma’aikatan jihar Kano, Usman Bala ya kammala aikinsa, inda ya yi ritaya daga aikin gwamnati tun a watan Mayun shekara ta 2023, kamar yadda doka ta tanada . Sanarwar ta ce Alhaji Abdullahi Musa ƙwararen ma’aikacin gwamnati ne da…
Read More
Sai an tallafa wa ƙananan masana’antu idan ana son karya farashin shinkafar gida – Ambasada Ali

Sai an tallafa wa ƙananan masana’antu idan ana son karya farashin shinkafar gida – Ambasada Ali

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano Ambasada Alhaji Ali Idris Mai Unguwa Kura, Shugaban Ƙungiyar Masu Sarrafa Shinkafa, Sayarwa da Noma ta na Ƙaramar Hukumar Kura, kuma Shugaban Ƙungiyar Masu Ƙananan Masana'antu da Matsakaita na Sarrafa Shinkafa na Ƙasa, reshan Jihar Kano, ya bayyana cewa ƙorafi da koke-koke da ake yi na tsadar shinkafa, wannan ya samo asali ne daga ƙarancin masu sarafa ta. Alhaji Ali ya ƙara da cewa, "idan har ana son noma shinkafa ya bunƙasa cikin tsafta, ya kuma wadata, da babu tsakuwa ko ƙuƙus, a cikin ta cikin farashi mai sauƙi da rahusa, sai an tallafawa ƙanana…
Read More
Cece-kuce ba zai canja hukunce-hukuncenmu ba – Alƙalai

Cece-kuce ba zai canja hukunce-hukuncenmu ba – Alƙalai

Daga BASHIR ISAH Babban Alƙalin Najeriya (CJN), Mai Shari'a Olukayode Ariwoola, ya jaddada cewa cece-kucen da ake yi a ƙasa ba zai canja hukunce-hukuncensu kan shari'un siyasa ba. Kawo yanzu, hukunce-hukuncen da Kotun Ƙoli ta yanke kan batutuwan zaɓe, wanda hakan ya yi sanadiyar soke nasarar wasu gwamnoni da 'yan majalisu, ya haifar da zazzafar muhawara a tsakanin 'yan ƙasa musamman 'yan siyasa. Da yake jawabi a wajen buɗe zama na musamman na fannin shari'a na 2023/2024 da kuma rantsar da sabbin manyan lauyoyin Nijeriya su 58, Ariwoola ya buƙaci alƙalai da su yi tsayin daka game da ayyukansu. Ya…
Read More
2024: Babu abin da zai dakatar da ni daga takarar Gwamnan Edo – Shaibu

2024: Babu abin da zai dakatar da ni daga takarar Gwamnan Edo – Shaibu

Daga BASHIR ISAH Mataimakin Gwnan Jihar Edo, Philip Shaibu, ya bayyana aniyarsa ta neman shiga takarar gwamnan jihar ya zuwa 2024. Ya ce zai tsaya takarar ne a ƙarƙashin Jam'iyyar PDP, tare da cewa, babu abin da zai hana shi neman kujerar gwamnan jihar. Shaibu ya bayyana aniyyar tasa ce da safiyar ranar Litinin a cibiyar Biohop Kelly Centre da ke Benin City, babban jihar. Da yake yi wa dandazon masoyansa jawabi, Shaibu ya ce a matsayinsa na ɗan asalin jihar wanda kuma ya san ciwon al'ummar jihar, zai nemi shugabancin jihar ne don cigabanta da ma al'ummarta baki ɗaya.…
Read More